← Book details Asp Zarah Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 7 OF 18

Sashe 7

Asp Zarah Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Innalillahi wa inna ilaihir raji'un, Allah yasa kunnuwana ba daidai suka jimin ba." Abinda Momi ta faɗa kenan wacce suka shigo a tare da Daddy suka tarar ina wannan zancen, gabaɗaya muka juya gareta muna kallonta har ta ƙaraso inda nake ta zauna tana fuskantata tace
"Zarah dan Allah me naji kina faɗa yanzu? Kice min ba abinda naji kika faɗa ba dan Allah.?" ta ƙarashe maganar tana riƙo hannuna ɗaya da babu ciwo, tausayinta naji ya kamani zuciyata tayi nauyi, tabbas nasan banason auren nan nayi biyayya amma mutuwar aure sam babu daɗi musamman ga mace mai irin aikina lokaci guda mutane zasu juya maganar zuwa wata daban, ciwon ƴa mace na ƴa mace ne, nasan tabbas Momi tana jin wani irin yanayi a cikin ranta kwatankwacin yadda nakeji, ban taɓa son M.J ba har gobe amma ban taɓa fatan ace aurenmu dashi ya rabu ba. Cikin murya mai rauni na ce
"Ehh Momi hakane aurenmu da Yaya Jawwad ya rabu a daren jiya." wasu hawaye masu É—umi naji suna zubomin saboda hoton abinda ya faru a wannan daren daya bayyana cikin kwakwalwata. Salati suka saka gabaÉ—aya illa Jiddah gwanar kuka da tuni ta fara zubda hawaye, shikuwa Sadiq yana tsaye a gefena har wannan lokacin sai dai babu wanda zai iya tantance yanayin da yake ciki.
Daddy ne yayi ƙarfin halin tambayata yace
"Daughter me ya faru ne kin saka mu a cikin ruÉ—ani."
Cikin nauyinsu da nakeji na labarta musu abinda zan iya tunawa, ai kuwa tamkar waɗanda ke jiran ƙiris nan suka soma fashewa da kuka hatta Daddy sai da yayi hawaye illa Sadiq da kallo ɗaya zaka mishi ka firgice da yanayinsa na tsantsar ɓacin rai da yake ciki.
Nan suka fara jajanta abin kowa da abinda yake faɗi akai musamman Momi da saida Baaba ta tsawatar mata saboda ɗiban albarka da take yiwa M.J ba ƙaƙƙautawa.
Tare muka wuni a asibitin har Daddy kowa da kalar kulawan da yake bani, cikin wuni ɗaya kuwa tamkar wacce ta daɗe tana jinya naji na samu ƙarfin jiki sosai, duk waɗannan abubuwa dake faruwa zuciyata a ƙage take dare ya ratsa na samu na karanta littafin da Saleem ya kawomin wanda dashi nakeson amsa musu tambayoyin da suke ta yimin akan littafin musamman Jiddah.
Sai wajen ƙarfe goma na dare su Momi da Saleem suka yi mana sallama aka barni da Baaba da Jiddah domin kwana da ni, duk yadda akaso Jiddah ta je gida ta turje hakan yasa aka barta mu kwana tare.
Kaɗan-kaɗan muke hira har bacci ya rinjayi Baaba ta kwanta ta barmu ni da Jiddah muna hirar, ganin baccinta yayi nisa ne yasa na fito da littafin daga ƙarƙashin filon da nake kwance na yafito Jiddah tazo gefena ta zauna muka buɗe littafin a hankali mu ka fara karantashi cikin zumuɗi.

*ASALIN LABARIN WANZOWAR ALPHA*...✍🏻

_🙏🙏🙏 Nima na shaida nasan kuna haƙuri da ni sosai musamman ƴan VIP da yanzu bana iya muku update kullum. Dan Allah kuyi haƙuri abubuwa suna yimin yawa ne amma zan dinga ƙoƙari in sha Allah.🥰🥰 Kamar yadda nasan kuna yi inaso ku cigaba da sani a addu'o'inku akan abinda na sa a gaba.🙏🙏🙏 Ina son ku irin totally💃💃💃

*BY*
*JASMINE*🌸🌸

*ASP ZARAH*👩‍✈️

*BOOK 2*

*Page 6*

_Mafarin Lamarin_.

Asalin sunansa Al'amin, ya kasance ɗa na biyar ga Malam Mudi da matarsa Inna Habi, sauran ƴan'uwansa uku mata da namiji ɗa inda ya kasance auta, bayan haihuwar Al'amin ne Malam Mudi ya ƙaro aure inda ya auri wata bazawara da ake kira da Phalmata, tun daga lokacin kuma rainon Al'amin ya dawo hannunta.

Saboda kulawar da take bashi yasa Inna Habi ta bayan ta yayeshi ta tattara kayansa ta maidawa Phalmata riƙonshi gaba ɗaya.

Shekararsa takwas kacal a duniya Allah yayiwa Inna Habi rasuwa, a wannan lokacin duk sauran yayyinsa sunyi aure illa ɗan'uwansa guda da shima yake shirin yi. Tun ƙuruciya Phalmata ke koyawa Al'amin dabarun sace kuɗin mutane da zarar sunyi sake sai dai duk da haka bata gaza wajen ganin cewa ya samo ingantaccen ilimi saboda wani buri da ke ranta, baya ga haka itama tayi karatu kuma ta ɗanɗani daɗinsa.

Tun girmansa sai ya kasance ya kara haɗuwa da abokai masu irin tarbiyarsa, tun daga wannan lokacin lamarin satarsu da fashi ya shahara, sai dai suna yin komai ne cikin basira basa taɓa bari su bar shaidar da za'a gane su.

Bayan kammala karatunsa na Jami'a ne Allah yayiwa mahaifinsa rasuwa, a wannan lokacin ne Phalmata ta baiyana masa shirinta na zamewarsu shahararrun ƴan ta'adda da zasu addabi ƙasa da duniya baki ɗaya. Suna kashe duk wanda suka nemi dukiyarsa ya hana, sannan muddin suka kwallafa rai akan abu sai sun samu. Haɗewar sunan Phalmata da Al'amin ne ya samar da sunan ALPHA wanda mutane da dama suke tunanin sunan na mutum ɗaya ne.

Shararsu ne tasa gwamnati ta shiga neman hanyar da zata kamasu gadan-gadan, sai dai sun siye baki mutane da dama daga sama wannan dalilin ne yasa duk sanda zasu tura yaransu yin fashi suke hada baki da manyan jami'ai domin a dakatar da tsaro a inda zasuje É—in.

Sun yi nesa da inda mutane suke sannan sun alkinta kansu ta yadda babu wanda zaiyi tunanin saninsu ko yasan wani abu dangane da su.

A yanzu haka suna rayuwa ne a garin Enugu a cikin wani ƙauye da ake kira Keruba, wani abun mamaki shine duk da a cikin mutane suke amma hakan baisa mutane sun shaida su, dalili kuwa shine, wani madaidaicin gida kamar ko wanne gida da kuka saba ganin mutane na rayuwa a ciki, amma a ƙasan wannan gida rantsatstsiyar fada ce tamkar ta sarakai wacce aka yiwa laƙabi da _ALPHA VILLA_.
Babu wanda yasan a inda ƙofar dake sada mutane da Alpha Villa take a cikin wannan ƙaramin gida, a duk lokacin da mutum zai shiga ko fita sai an shaƙa masa hodar dake saka bacci na wasu mintuna.

Ta hanya ɗaya ne kacal zaku iya nasarar kama Alpha a sauƙaƙe.
A kowacce ranar Lahadi yana ɓadda kama ya fito daga wannan gidan don ya zaga gari, yakan kwashe awa guda da rabi yana zagawa kafin daga baya ya koma mazauninsa. Babban lagon Alpha guɗa ɗaya ne, wato mace mai ciki. Yana matuƙar tausayin mace mai ciki ko da wucewa tayi ta gabansa sai yaji hawaye na neman fitowa daga idonsa. Saboda haka idan kunason kama Alpha dole ku nemi wata mace da ke da ciki don samun lagonsa.

Mun daÉ—e mu na karatun wannan littafin har dare ya ratsa sannan mu ka gama, ajiyar zuciya mu ka sauke a tare ni da Jidda bayan na rufe littafin na maida shi inda yake, kallon juna mu ka yi cike da rauni kafin Jiddah ta ce
"Na samo mana mafita."

"Mafita? Wace iri?" na tambaya.

"Mai ciki ake nema kuma gani sai ki zame min Æ´ar jagora."

"Ke baki da hankali ne Jidda kinsan me kike faÉ—a kuwa."

"Wallahi idan kika kuma mu sa min akan abinda na faɗa ban yafe hakkin ƙaunar da nake miki." Jiddah ta fada tana mikewa ta koma kusa da inda Baaba ke kwance itama ta kwanta, ta barni sororo ina jimami.
Na jima a zaune kafin daga baya na tura littafin ƙasan filo,sannan na sulale na kwanta zuciyata cike da tunanin mafita.

Washe gari tunda farar safiya
Sadiq ya iso asibitin, kallo É—aya za'a masa mutun ya gane cewa bai runtsa ba, Baaba ya fara gaidawa sannan nida Jidda muka gaishe shi ya amsa yana tambaya ta ya jiki. Zama yayi a gefena yace lafiyarki"
Cikin mamaki muke kallonsa ni da Jiddah kowa da abinda yake saƙawa a ranshi.

"Amma Yaya me yasa ba zaka barni anan ba."

"Ina so ki yi nesa da M.J banaso ya kuma ganinki bare wani abu ya shiga tsakaninku ko da kuwa kalmace ta fatar baki."

Baaba da ke zaune can gefe ne ta ce
"Haka ba shine mafita ba Sadiq a barta anan É—in kawai, ai an riga da anyi kuskure ba za'a kuma bari kalan haka ta faru ba."

Ganin Baaba na son jan maganar ne yasa ya ja bakinsa ya yi shiru bai kuma magana ba. Mu na zaune a haka su Daddy suka shigo shi da Momj da Saleem, hannun Sa-Jid ɗin ɗauke da kwandon abinci, gaishe-gaishe aka yi suna ƙara tambayata ƙarfin jikin. Momi ce ke faɗamin cewa Ammi ta kira waya tana gaishe ni, sannan ta ce zasu taho a satinnan, cikin jindaɗi na amsa ina ƙara jaddada ƙaunata a zuƙatan waɗannan mutanen. Jidda ce ta zuba mana abincin, dafa dukan cous-cous da farfesun kayan ciki, sosai naji daɗi abincin kuma na ci sosai irin wanda na jima ban ci ba saboda a lokuta da dama ba na samun damar yin girki saboda aiki, dama kuma M.J ba abincina ya ke ci ba bare nayi tunanin dafa mishi.

Ƙamshin turarensa ne ya fara sanar da ni zuwansa, mu na zaune su ka turo ƙofar ɗakin shi da Hajara cikin kyakkyawar shiga irin na masu morar amarci, da alama hankalinsu kwance yake kamar tsumma a randa.

Da sallama a bakin Hajara, Baaba ce kaɗai ta iya amsa sallamar hatta Daddy kai ya kauda gefe. Ganin haka ne yasa suka gaida Baaba kaɗai sannan suka nemi guri su ka zauna. Jim ɗakin ya yi babu wanda ya tanka, Daddy ne ya ciro wata farar takarda daga aljihunsa sannan ya baiwa Sadiq ya miƙawa M.J da kansa ke a sunkuye, cikin son ƙarin bayani ya kalli Daddy sai dai ya kauda kansa gefe, hakan yasa shi buɗe takardar don ganin abinda ta ƙunsa. Cikin razana ya ɗago ya ce

"Kotu! Daddy me na yi?"

"An haÉ—a baki da kai wajen cutar min da Æ´ata."

Da matuƙar mamaki mu ka ɗago a tare muna kallon Daddy, Baaba ce tayi ƙarfin halin cewa
"Sulaimanu wanj zance nake ji haka, wa za'a kai kotu."

"Ba wani abin tashin hankali bane fa Baaba, komai zai zo da sauƙi." Daddy ya faɗa.
Chapter 7 · 0% Book details