Sashe 15
Asp Zarah Part 2 Complete Hausa Novel · about 7 min read
A wannan dare kusan kwana tayi idonta biyu da tunanin M.J a ranta.
Washegari kuwa da manyan baƙi suka tashi don Ammi ce da Rahama suka diro ƙasar tun safiya, murna kuwa a gurin Zarah kamar ta shiɗe. A ranar haka suka wuni cikin walwala da yamma kuma suka wuce gidan Jiddah dan acan zasu kwana saboda aikace-aikacen suna da za'ayi washegari.
Mutanen sunyi mamakin karar da Jiddah tawa Zarah kodayake ba mamaki idan aka duba irin shaƙuwar dake tsakaninsu. Yarinya dai taci suna Fatimah Zarah za'a dinga kiranta da Amrish.
Suna ya ƙayatar sosai uwa da ƴa sun samu kyaututtuka na ban mamaki, a haka aka watse taron kowa ya tafi da souvenirs da aka yi.
Saleem bai yarda a tafi da Jidda wankan gida ba dan haka ne aka nemi wata daga cikin danginsu ta zauna da ita.
Kwanaki biyu tsakani Safwan ya shirya tafiya Yola sai dai zai jira Yayanshi da yazo Gombe aiki ya gama su tafi tare. Tun ranar da yazo basu haɗu da Safwan ba sai ranar tafiyarsu gida ya taho gidansu Zarah dan gaisawa da surukan ƙaninshi.
Rabon kwaɗo ko a ruwa zafi yake baya wucewa, Tunda yayi arba da Rahama zuciyarshi a karo na farko ta gamsu da ita yaji yana sha'awar ƙulla taraiya ta har abada da ita.
Bai bayyana hakan ba sai a hanyarsu yake shaidawa Safwan aikuwa yayi murna sosai inda yace zai sanar da mai martaba a haÉ—a aurensu tare.
Sanda iyayensu suka ji wannan batu sunyi murna matuka musamman da kullum burinsu bai wuce suka Mahmud yayi auren ba, babu wani jan lokaci dan sun yanke shawarar a haÉ—a auren biyu indai ya tabbata, ko da Mai martaba ya kira Daddy ya tambayeshi ko anyiwa Rahama mijin cewa yayi a'a amma zai tambayeta ko akwai wanda take so, Alhamdulillah bai sha wuya da Rahama ba ta gayamai babu wanda ta tsayar dan haka ya kira Mai martaba ya shaida masa.
Kwanaki uku tsakani aka hado lefe da sadakin Rahama aka kawo inda aka tsaida biki rana É—aya da nasu Zarah wata É—aya da sati biyu masu zuwa.
Murna kuwa ba'a magana, nan Ammj ta ƙara zagewa ta fara gyara ƴaƴan nata na musamman.
Shidai M.J ya daina jinya a fili sai a zuciya, yana matuƙar galabaita sosai dan ya rame yayi haske kamar wanda ke gargarar mutuwa.
*********************************
Kwanci tashi asarar mai rai, yau gashi har an shiga satin da za'a fara shagalin bikinsu Zarah, duk wasu shirye-shirye da suka kamata anyi. KuÉ—i kuwa tamkar ba nemansu ake yi da zafi ba yadda ake fiddasu kamar ba'asu.
Daga masarautar su Safwan kaÉ—ai miliyon goma aka turo na gyaran amare banda manyan akwatuna da aka ciko da kayan fitar biki masu tsadar gaske.
Æangaren su Daddy ma shirye-shirye ake yi sosai dan Daddy kwarai yake son nuna su Zarah na da gata duk da ubansu baya raye, shikanshi sai da ya musu akwati bibbiyu ya shake da kaya na fitar biki bayan kayan É—aki da suka shirya da Momi da Ammi suka je har Italy dan siyowa, hatta cokali abin banza a Æ™asar waje aka siyo musu komai nasu daga can ne.
Baaba kuwa tayi faɗan harta gaji amma sunƙi dainawa.
Babban Yaya kuma wani danƙareren Boutique ya gina musu wanda aka cikashi da kayan siyarwa na manyan mutane da ko a ƙasar waje sai haka, inda aka shirya taron buɗeshi ranar da za'ayi bridal shower ɗin amaren, bayan haka sai da ya saka musu makudan kudi a cikin account dinsu.
Tun ranar Monday aka fara gudanar da shagulgula inda akayi Welcoming dinner ranar monday a farfajiyar gidan Daddy an kashe kuÉ—i sosai amare kuwa sun sha kyau tamkar a sace su a gudu, washegari ranar talata kuma akayi Fulani day mai ban sha'awa dan harta mutanen Yola sai da suka zo a jirgi bayan angama ya kwashe su ya kuma, Ranar laraba kuma akayi shagalin buÉ—e Boutique É—insu Mai suna *RAHAZAR BOUTIQUE* wanda ya samo asali daga farkon sunan kowaccensu.
Washegari Alhamis ne za'a gabatar da Reception kuma a ranar Safwan da abokansu zasu taho Gombe dama shi Mahmud tun ranar Monday yake nan saboda wani taro da suka gabatar shiyasa bayan an kammala yayi zamansa kawai tare da wasu daga cikin abokanansu.
Fitowar Zarah daga wanka kenan saboda bata tashi da wuri ba dan gajiya dama kuma tana fashin Sallah, turo Æ™ofar akayi a hankali kanta ta maida kan me shigowar Sadiq ne da Daddy suka shigo kallo É—aya zaka musu ka gane tsantsar damuwa a tattare da su. Hijab ta É—auka ta zura sannan ta gaida Daddy bai amsa mata ba illa zaunar da ita da yayi a gefen gado ya fara magana kamar....âœðŸ»
*BY*
*JASMINE🌸🌸*
*ASP ZARAH*
*BOOK 2*
Nasiha sosai Daddy ya fara mata me ratsa jiki, ƙirjinta ne ya fara dukan uku saboda yadda taji yana ambatar karɓar ƙaddara, ko wacce ƙaddarar ce ta kuma samun rayuwarta, tunaninta ya katse sanda taji Daddy na faɗin
"Zarah haƙuri da juriyar da na sanki dashi a wannan karon ma shi nakeso kiyi sannan ki rungumi ƙaddarar da Allah ya ɗora miki da hannu biyu. Kiyi haƙuri Zarah yau da asuba Allah yayiwa Safwan mijin da zaki aura rasuwa sakamakon ciwon ciki da ya kulleshi a jiya da dare."
Tamkar saukar aradu haka taji maganar Daddy a kunnuwanta bata kyma gaskatawa ba sai da taji É—an uwanta na maimaita batun Daddy É—in.
Bata kuma sanin inda kanta yake ba sai buɗe ido tayi ta ganta kwance a gadon asibiti da ƙarin ruwa a hannunta, a hankali ta fara juya idanunta tana ƙarema inda take kallo da mutanen dake wajen, mutum uku ta gane a cikinsu Baaba, Jiddah sai Rahama da suka yi wujiga-wujiga alamun tashin hankali ya bayyana a garesu, ƙoƙarin mikewa ta farayi da sauri duk suka ƙaraso inda take suna mata sannu bata kula ba ta fara magana tana cewa
"Dan Allah kuce mafarki nayi na zahiri bane dam Allah kada kucemin Safwan ya rasu bazan iya rayuwa batare dashi ba, wayyo Allah shin wani zunubi na aikata a rayuwata da nake ganin irin waÉ—annan kaddarori." Kuka mi cin rai ta fashe da shi me cin rai.
Gabaɗaya tausayinta ne ya kamasu su kansu rasuwar Safwan ta jijjigasu matuƙa bare ita kuma da kowa ya zauna da su a ɗan ƙanƙalin lokacin nan zai fahimci irin ƙaunar da suke wa juna. Kwananta biyar kenan a kwance batasan wanda yake kanta ba tun ranar da aka faɗa mata batun rasuwar Safwan ɗin. Bayan su Daddy sun kawota asibiti ne suka bi jirgi zuwa garin Yola dan jana'izarsa, kwanansu biyu suka dawo kuma kafin su dawo sai da aka ɗaura auren Rahama da Mahmud sannan Zarah da Jawwad dan Mai martaba ya ce baza'a ɗaga auren ba sannan shi da kanshi ya baiwa Daddy shawarar a ɗaura aurenta da Jawwad ɗin sannan yace shi da kanshi zai zo ya taushi Zarah idan anyi sadakar bakwai sai dai an dakatar da shagulgulan da aka shirya.
Kuka takeyi sosai harda shiɗewa suna bata baki ganin taƙi yin shirune yasa Jiddah ta kira likita yana zuwa kuwa ya mata allurar bacci nan bacci ya ɗauke ta sannan ya cigaba da dubata.
Sai da Zarah ta yi wata guda a asibiti kafin ta fara dawowa daidai tare da sakawa ranta cewa lallai Safwan ya tafi ya barta saidai ya barta da rauni a zuciyarta da bazata taɓa warkewa ba, ta kuma shiru shiru sam bata son hayaniya kullum cikin jan carbi da karatun alqur'ani take yi, a haka likita ya bata sallama bayan nasihohi da aka mata.
A ranar da Safwan ya rasu harda M.J da Abdallah suka shirya zuwa jana'izarsa. Kuma a gabansa aka É—aura aurensa da Zarah, a ranar ji ya yi tamkar mafarkan da ya saba yi ne yake yi, babu kalar addu'ar alkhairi da bai yima mai martaba ba godiya kuwa har saida ya dakatar da shi, kwana yayi yana sallar godiya ga Allah da kyautar da yayi masa a lokacin da ya cire tsammanin samu.
A haka suka gama kwanaki uku suka baro Yola zuciyar M.J cike da farin ciki sai dai a ɓangare guda yana taraddin yadda zai fuskanci Zarah ko da wani idon zata kalleshi idan taji labarin ya zama mijinta a karo na biyu.
Kullum sai yaje asibitin dan dubata sai dai yafi zuwa lokacin da yasan tana bacci, tana bashi tausayi sosai saidai a ɓangare guda yana kishi idan ya tuna saboda wani take yin wannan jinyar.
Kwanaki biyu da sallamo Zarah Mai martaba da tawagarsa suka zo, da kanshi ya nemi ganawar sirri da Zarah, shima dai nasihar ya mata sosai kafin daga baya ya shaida mata batun aurenta da Jawwad, aikuwa nan hankalinta ya ƙara tashi ta fashe da kuka, roƙonta mai martaba ya shiga yi dakyar ya samu ta sassauta bayan ya shaida mata yau yake so dukkansu a wuce dasu ɗakin mazajensu dan dama Rahama tare da masu ɗaukarta suka zo. Nisawa yayi ganin yadda take risgar kuka yace