Sashe 16
Asp Zarah Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Fadimatu bawai shawararki nake nema ba ina baki umarni ne a matsayina na uba gareki indai kin bani wannan matsayin. Kiyi hakuri da yadda ƙaddara tazo miki mun sani duka cewa kina halin da yakamata a tausaya miki amma hakan da aka miki shine gata kuma zai rage miki raɗaɗin abinda kike ji. Ki sani cewa a yanzu Safwan babu wani abu da yake bukata a gurinki face addu'a sannan bazai taɓa yin farin ciki ba matuƙar kika bijirewa iyayenki saboda kawai son da kike mishi sannan bazai ji dadi ba idan aka tada ki ranar alkiyama a matsayin wacce bata bin umarnin iyayenta, a yanzu akwai auren wani a kanki tunanin Safwan da irin soyayyar da kukayi ba shine mafita a gareki ba domin dai hausawa sunje matar mutum kabarinsa, dama can aurenku da Safwan babu shi cikin lauhul mahfuz, ta iya yiwuwa akwai tanadin da Allah ya muku a lahira shiyasa bai saka kun zama ma'aurata a duniya ba. Shi kanshi Safwan ba zaiji dadin kwanciyarsa a cikin kabarinsa ba matuƙar kin take dokar Allah saboda kawai son da kike mishi. Matukar kin bani wannan matsayi na mahaifi dan Allah Zarah ki amince da wannan auren sannan ki rikeshi hannu bibbiyu dan samun rabauta duniya da lahira, shin zaki iya yimin wannan alfarmar."
Cikin sheshsheƙar kuka ta gyada kai sannan tace
"Na aminci Baba zanyi amfani da duk abubuwan da ka fadamin sannan zanyi ƙoƙari na cigaba da ɗaukan hakan a matsayin ƙaddarata."
Kalamai masu taushi ya cigaba da gayamata har saida yaga hankalinta ya kwanta sannan ya kira sauran mutanen gidan yayi musu maganganu masu ratsa jiki musamman M.J dan kusan gabaÉ—aya fadan akanshi ne, da haka ya baiwa sauran iyayensu damar magana shikam Daddy ya kasa furta komai dan gani yake kamar a yanzu bashi da wata kima a idon Zarah dan kila zatayi tunanin saboda yana son É—anshi ne kawai ya saka aka É—aura auren.
Duk shiru sukayi kafin Momi ta bude baki ta ce
''Muhammad Jawwad a matsayina na mahaifiyarka matuƙar ka ƙuntatawa Zarah a gidan aurenka ban yafe maka ba duniya da lahira ko bayan bana raye." daga haka ta mike ta fice a falon. Kai kawai mai martaba ya kada sannan yasa aka kira mishi matan da suka zo tare ya shaida musu su shirya Zarah su fara kaita ɗakinta kafin su zo su wuce da Rahama zuwa Yola.
Haka kuwa akayi da taimakon Ammi da Jiddah suka shiryata fes ta fito amarya sai dai kallo daya zaka wa fuskarta ta baka tausayi saboda yadda ta kumbura lokaci guda tayi jazir saboda kukan da take yi.
Sam Baaba da Momi sunki yarda suyi Sallamar ƙarshe da Zarah shikuwa Sadiq hannunta kawai ya riko ya kaita har ciki sabuwar motar da Daddy ya siya musu ta fitar biki ita da Rahama ya zaunar da ita a ciki sannan ya rike hannunta gam yace
"Ki sani a kowani lokaci zan kasance tare da ke sannan bazan taba bari a cuceki ba a wannan karon matukar akayi yunkurin hakan sai inda karfina ya kare akanki, banaso ki saka damuwa a ranki ki cire komai ki saka a ranki cewa ibadah zakije yi sannan ibada dole sai da sadaukarwa. Zan kasance a tare da ke a kowani lokaci."
Hannu ya saka ya share mata hawayen fuskarta sannan ya sake hannunta ya rufe motar ya ja hannun Rahama dake fama risgar kuka suka shige cikin gidan.
Basu jima sosai a gidan Zarah ba suka yi niyyar komawa saboda tafiyar dake gabansu, hakuri sosai Ammi ta kara bata kafin su bar gidan, itama dai Jiddah bata zauna ba duk da taso hakan amma Ammi ta hana. Haka suka tafi suka barta ita É—aya tana aikin kuka.
Rahama ma haka aka tafi da ita cikin kuka da kewar rabuwa da gida musamman Ammi dan daƙyar aka rabasu saboda shaƙuwar dake tsakaninsu. A haka aka wuce da ita zuwa airport jirginsu ya daga zuwa garin Yola.
Sai fatan zaman lafiya mai É—orewa.
***************************
Zaman dai na Zarah da Jawwad ba'a magana dan kuwa zamane na doya da manja sai dai yana iya bakin ƙoƙarinshi dan kyautata mata dan da gaske yake son gyara laifukanshi na baya.
Kullum safiya shi ke gyara ko'ina na cikin gidan daga falo har sauran ɗakuna hatta ɗakin da Zarah take kwana shike tsabtacewa duk safiya idan yazo zai gayamata zai gyara ɗaki sai ta fita zuwa falo ta bashi guri idan ya gama ta kuma, bata kuma fitowa sai idan ya gama breakfast yazo ya gayamata ta fita duk da bawani abincin take ci ba kawai tsakura kawai ta tashi, idan ta gama kuma yazo ya tattare kayan da taci abincin ya wanke kafin ya shirya ya tafi office dan ma dai shine shugaba shiyasa bashi da wata matsala a fannin ƙorafin latti, da rana ma haka duk abinda yake yi zai bari ya siya abinci a resturant ya kai mata.
A haka rayuwar tasu take kasancewa sai dai babu wata alaqa tsakaninsu dan kafin Zarah ta mishi magana ma yana jimawa sosai sai dai idan abu ya kasance mai mahimmanci ne.
A haka aka shirya taron ƙarawa Zarah matsayi a wajen aikinta inda aka bata muƙamin mataimakiyar Commissioner na ƴan sanda a jahar Gombe gabaɗaya, gagarumin taro aka shirya Daddy da kanshi ya kira M.J ya shaida mishi bai ko yi musu ba ya amince inda shima yasha alwashin zuwa batare da yayi tunanin komai a ranshi ba.
Taron ya ƙayatar sosai inda Zarah ta samu manyan kyaututtuka hatta su Daddy sai da suka samu kyautar karramawa a matsayinsu na iyayenta. A haka aka watse taron aka watse.
Sosai hankalinsu Momi ya kwanta ganin babu wata alamun damuwa a tattare da Zarah ga kuma yadda M.J yake bin umarninta kamar dai itace mijin. Sai dai shi kallo É—aya zaka masa ka gane cewa hankalinshi ba'a kwance yake ba amma tunda ba furtawa yayi ba babu wanda yasan abinda ke damunsa.
Zamansu dai bai canza zani ba dan jiya iya saboda M.J ya maida kanshi tamkar bawa ya cire duk wanj girman kai yana baiwa Zarah kulawa, a yanzu da ta fara fita aiki kullum yana idar da sallar asubahi yake fara aiyukan gidan sannan ya hada musu breakfast. Idan ta gama karyawa kuwa shi da kansa yake É—aukar mata jaka ya kaita mata mota sannan ya bude mata idan ta shiga ya rufe ya mata addu'ar dawowa lafiya kafin nan ya kuma ciki ya shirya ya tafi nashi aikin.
A haka rayuwar tasu take kasancewa har zuwa tsawon wani lokaci sai dai an samu sassauci dan yanzu Zarah tana gaidashi wani lokacin kuma da kanta take dafa musu abinci musamman idan ta fahimci baya jin dadi dan a zaman su sau biyi ciwonshi yana tashi kuma yana wahala sosai.
Yau ta kasance weekend babu aiki dan haka ne tunda tayi sallar asuba ta kuma ta kwanta saboda tana bukatar hutu dan a satin tayi aiki sosai ta gaji. Baccinta take yi hankali a kwance a haka M.J y shigo dan gyara mata dakin ganin tana bacci ne yasa ya tsaya yana ƙare mata kallo tare da jinjinar girman soyayyar da yake mata, ya dade a tsaye kafin ya fita ya ja mata ƙofar a hankali ya koma kitchen da hada musu abinda zasu karya dashi.
A firgice ta mike zaune jikinta na rawa lokaci guda ta haÉ—a gumi har tana diga sosai hankalinta ya tashi akan mafarkin da tayi...âœðŸ»
*BY*
*JASMINE*🌸🌸
*ASP ZARAH*
*BOOK 2*
Take abinda ta gani cikin mafarkin ya fara dawo mata filla-filla sosai hankalinta ya tashi.
Zaune take a cikin wani haɗaɗɗen garden tana zaune tana hutawa iskar gurin na kaɗa ta, a hankali ta fara hango wani haske na nufo inda take har ya iske ta, ware ido tayi sosai ganin iyayenta cikin kyakkyawar shiga sai sheƙi suke yi. Da sauri ta mike da nufi isa inda suke sai kuma ta tsaya ganin Mami ta ɗago mata hannun alamun ta dakata batason ta iso inda suke sannan tace
"Fadimah ashe irin abinda kike aikatawa a gidan mijinki kenan saboda kinga kasa ta rufe mana ido, kenan duk tarbiyar da na baki akan yarda da ƙaddara baki ɗauka ba ko so kike Allah ya azabtar damu saboda kinki bin umarninshi, kinsan a rana sau nawa mala'iku ke tsine miki kuwa akan halin ko'in kula da kikewa mijinki. Ki gaggauta gyarawa dan sauke fushin Allah akanki, nima da kika ganni cikin jindaɗi ba komai bane sila face biyayyar da nayiwa nawa mijin shin bakyaso ki shiga jindadi ki kasance tare da mu a ƙoramar alfarma. Mahaifinki yana fushi dake sosai bayaso ma ya miki magana sai ranar da kika gyara halayenki. Na tafi kiyiwa mijinki biyayya Fadimah kiyiwa mijinki biyayya kiyiwa mijinki biyayya." A nan zancenta ya ƙare saboda hannunta da Abba yaja suka bar wajen, zama tayi a ƙasa tana kuka sosai har na tsawon lokaci kafin taji an dafa ta ɗagowar da zatayi tayi arba da Nusaiba itama cikin shigar alfarma, kafin ta iya furta komai Nusaiban ta ce
"Yaya Zarah kowa yana fushi dake harsu Kaka dake sonki duk sunyi fushi saboda abinda kike aikawata, Kaka ta ce bataso taga kullum mala'iku suna tsine miki dan haka ne ma tace babu ruwanta dake, har su Adeel duk sun daina sonki, nima kawai nazo ne na gayamiki idan baki gyara halayyarki ba bazan kuma zuwa inda kike ba."
Kafin ta ankare ta neme ta ta rasa dan haka ne ta miƙe ta fara tafiya dan barin wajen, tana cikin tafiyane ta hango wani a zaune kan wata kujera ta alfarma sai sheƙi take yi, tsayawa tayi daga nesa tana ƙare mai kallo, juyuwar da zaiyi taga ashe Safwan dinta ne da mugun gudu ta nufi inda dan isa gare shi, Dakata! Shine abinda ya faɗa da ƙarfi sannan ya cigaba da cewa
"Baki kasance cikin masu yarda da ƙaddarar da Allah ya jarabesu da shi ba dan haka karki zo inda nake." bat ta nemi shi ta rasa, kuka riris take yi tana kiran sunayen su amma babu wanda yazo.