← Book details Asp Zarah Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 4 OF 18

Sashe 4

Asp Zarah Part 2 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Wata irin zabura Momi da ke kan kujera tayi har saida ta sauko ƙasa ta dira a gaban M.J tana ƙura mishi ido, shikuwa Sadiq wayarsa ƙirar IphoneRx dake hannunshi ne ta saɓule ta faɗi ƙasa ji kake tasss ta fashe akan tiles, murmushin da akewa laƙabi da na ciwo shi Daddy yayi sannan ya kalle Momi da Sadiq yace
"Mene ne haka kamar kun riski saƙon mutuwar wani na jikinku.?"
Jan jiki Momi tayi ta jingina da kujerar da Zarah ke zaune,wacce tun faɗar maganar M.J zuciyarta taki nutsuwa a ƙirjinta sai barazanar fitowa take yi. Daddy ne ya kuma magana yace
"Muhammad Jawwad kace aure zaka ƙara koh.?"
Cikin fargaba da tsoro jin Daddy ya kira asalin sunanshi abinda bai taɓa ji daga bakin uban nasa ba tun yarinta,ya gyaɗa kai yace
"Ehh Daddy."

"Ƙarya kake yi wallahi ba isa ka jamin zagi a gari ba Jawwad, bazai taɓa yiwuwa ba wani kallo kakeso a dinga min idan na shiga cikin mutane." Momi ce ta faɗi haka cikin hargowa tana mai fashewa da kuka.
KaÉ—a kai kawai Daddy yayi cikin takaici ya kuma maida hankalin shi ga M.J yace
"Shin zan iya sanin dalilin ƙarin auren ko akwai wani abu da Zarah take maka ne wanda bakajin daɗinsa."

"Babu komai Daddy dama muna soyayya da yarinyar ne yanzu kuma mahaifinta ya ce yana bukatar aurar da ita." ya fada kai a sunkuye.

"Kaji ka amince cewa kanason yarinyar kuma zaka aureta ." Daddy ya kuma tambaya.

"Ehh Daddy." ya amsa a taƙaice.

"Shikenan tunda dai kai kazo da zancen bazan hanaka raya sunnah ba , na yarje maka kaje kayi aurenka amma bawai dan hakan zai min daÉ—i a raina ba, kaje ka fara shiri sannan ka turomin adireshin gidansu yarinyar nan da sati biyu masu zuwa in sha Allah za'a É—aura maka aure da ita kamar yadda kake so. Sai dai inaso ka shaida wallahi duk wani abu da ya biyo baya karka tunkareni da shi. Tashi kayi tafiyarka."

"Nagode Daddy." ya faÉ—i haka da hanzari ya mike ya fice daga falon gudun kar Momi ta kuma yin magana

Baki sake kamar mutum-mutumi Momi ke kallon Daddy kamar wacce taga wani abin al'ajabi mai girma, shikuwa Sadiq sarkin zuciya har ya mike ya finciki hannu Zarah da nufin su fice a falon Daddy ya dakatar dashi, cak! Ya tsaya ita kuwa Zarah tuni ta fara sana'ar tata na kuka.

"Indai ka É—auke ni a matsayin uba ka dawo ka zauna."
Babu musu suka juyo suka zauna zuciya sam babu daÉ—i, mintuna suka shuÉ—e babu wanda ya tanka kafin daga bisani Daddy ya ce
"Ku yi haƙuri da kalan hukuncin da na yanke, akwai wani abu da na hanga ne da sannu zaku ga abinda zai biyo baya domin jikina baya bani akwai alkhairi a ciki. Kiyi haƙuri Zarah faruwar komai jarrabawa ce daga Allah watarana sai labari., labarin ma watarana va za'a samu masu bada shi ba. Kiyi hakuri kinji, Allah ya jiɓanci lamuranki, kai Sadiq tashi ka rakata gida."
Babu musu ya miƙe ita kuma ta yi musu sallama suka wuce, a hanya babu mai magana a cikinsu har lokacin da suka isa har cikin harabar gidan M.J kafin Sadiq ya riƙo hannunta ya ce
"Ki dinga yawan tunawa da nasihar da Abba yake mana a ko yaushe, hakuri shine ribar zaman duniya, nima inaso na dinga kwatanta hakan sai dai zuciyata bata iya jure ganin ɗayan ku cikin ƙunci. Da sannu ni da kai na zanzo har cikin gidan nan na ɗauke ki na kaiki inda zaki samu farin ciki na har abada."
Murmushi kawai tayi mishi kana ta fita a motar ta shige gida, shi kuma ya juya kan motar ya fice a harabar gidan.

Kamar yadda suka tsara cikin sati Raliya ta zana musu fiskar matar kamar yadda ta dage wajen koyan abinda ake koyar da ita. Sai dai batun tafiyar ta su a katse sakamakon tasuwar bikin mijin Zarah.
A wannan lokacin kuwa tuni batun auran M.J ya kankama domin an bada sadaki sannan ankai kayan aure ranar kawai ake jira tazo a É—aura auran, sai dai mutane da dama basuyi farin ciki da wannan auran ba amma babu yadda aka iya da hukuncin Allah.

Rana dai aka ce bata ƙarya sai dai uwar ɗiya ta ji kunya, kamar yadda ya kasance ranar juma'a bayan zagayowar sati aka ɗaura auran Muhammad Jawwad Sulaiman da Hajara Suraj, bikin daya kasance tamkar na bazawara saboda rashin jama'a.
Haka amarya dai ta tare a gidan mijinta cike da buri a ranta na abubuwan da ta shigo cikin gidan da niyyar aikatawa.

Hausawa kan ce _Rawar da aka fara ta da tsalle ƙarshenta baya kyau_, kamar haka ce ta faru a gidan M.J wanda tun farkon kawo amaryarsa ya nuna mata cewa Zarah bata da wani matsayi a gurinshi face na ƴar uwa domin baya mata kallon matarsa, wannan dalilin ne ya saka sam Hajara bata ganin girmanta bare ayi tunanin zasuyi zaman amana, a wasu lokutan a gaban Hajara M.J ke yiwa Zarah cin kashi tare da cigaba da yi mata ƙazafin zina batare da lura da illar hakan da zai haifar masa anan gaba ba.
Yau ma kamar kullum Zarah ta dawo daga aiki a gajiye liƙis, ta shigo babban falon ɗauke da sallama a bakinta, kamar ko da yaushe suna kwance a dogowar kujera manne da juna suna soyayya tamkar zasu haɗiye juna, yau kwanansu goma kenan da aure amma kullum a haka suke wuni tare batare da M.J yayi tunanin bada haƙƙin addini akan wanda yayi sabon aure ba ko da yake bata zaton hakan daga gareshi domin ko da take ita kaɗai ma baya bata haƙƙinta daya rataya a wuyansa. Tunaninda takeyi ne ya katse sakamakon muryar Hajara da ta daki cikin dodon kunnenta tana faɗin
"Hubby haka kenan gidanka zai cigaba da kasancewa mafakar fasiƙai alhalin da ranka da lafiyarka.?" mikewa yayi daga kwancen ya zauna sannan ya dubi Zarah dake ƙoƙarin shigewa part ɗinta ya ce
"Ina fatan kin wanke janabar da kika É—ebo tun a waje baki shigomin dashi cikin tsabtaceccen gidana ba.?"
KaÉ—a kai kawai tayi sannan ta shige É—akinta cike da takaici domin ya ci ace ta saba da irin cin kashin da mijinta da kishiyarta ke mata a duk kwanan duniya.

*1:45am*

A daidai wannan lokacin ko wani halitta na ɗan adam yana tsaka da bacci in ka ɗauke ɗaiɗaiku da wani uzurin ya hana su bacci, cikin waɗanda basu yi bacci ba a wannan lokacin harda Zarah dake zaune gaban na'urarta tana gabatar da wani aiki gefenta kuwa wani ƙaramin kofi ne da shayi a ciki sai tururi yake yi, tana sanye da riga da wando na bacci mai santsi kalar sararin samaniya ta ɗaura wata hula mai gashi a kanta, gabaɗaya hankalinta ta maida akan aikin da take gabatarwa.
A hankali ta miƙe ta nufi window ɗin ɗakin saboda jin alamun kamar hayaniya na tasowa daga farfajiyar gidan, labulen ta ja kaɗan tare da leƙa tsakar gidan ga mamakinta sai taga kamar gilmawar mutum, ganin dare ne yasa bata wanj damu ba ta koma inda take zaune da ta cigaba da aikinta.
Zamanta ke da wuya ta ji an hayaniya da kururuwar Hajara a babban falon tare da sallallami da M.J ke yi, take ta gane cewa wasu sun shigo cikin gidan, da sauri ta miƙe ta ɗauki jacket ɗinta ta saka sannan ta zari ƙaramar bindigarta ta nufi falon. Ai kuwa kamar yadda ta zata mutane ne a falon su tara kowanne da shiga mai kyau fuska a rufe, uku daga cikinsu ne kawai maza amma duk sauran mata ne, ganin fitowarta ne yasa wasu mata su huɗu suka nufeta da nufin rikota, wani wawan naushi ta kaiwa waɗanda ke da nufin riƙe mata hannu da duka hannuwanta biyu sannan ta sunkuya ta kaiwa wacce take gabanta naushi a ciki take ta durƙushe saboda zafin da taji. Sai dai kafin ta kuma wani yunƙuri wasu suka tura ta ta faɗi ta gaba kafin ta ɗago suka yi nasarar ɗaure mata hannaye. Ɗaya daga cikinsu ne yayi maganar su ƙyale Zarah haka sannan ya juya ya kalli M.J ya ce
"Ran matan ka ko kuma dukiya.?"
Cikin kauda kai M.J dake riƙe a hannun ƙarti biyu da mace ɗaya yace
"Malam ni matata É—aya ce kuma gata nan" ya nuna Hajara sannan ya cigaba da cewa" Ku kama wacce ta muku laifi ku rabu da mu."

Dariya yayi sannan yace
"Ya za'ayi mu yarda da hakan bayan a mun shaida É—aurin auren ku."

Shiru yayi na wasu mintuna sannan yace
"Idan kuna so ma zaku iya shaida warwarewarsa."
Cike da dariya mugunta ya kuma cewa
"Mai zai hana kuwa."

Cike da takaici Zarah tace
"Yaya Jawwad kada kayi abinda zaka zo kana da na sani, ina da rauni sosai sannan ni marainiyace. Kada ka lalatamin rayuwa ta hanyar maida ni ƙaramar bazawara."
Bai kula da maganganunta ba ya ce
"Na sake ki saki É—aya Zarah."
Tabbas mutuwar aure babu daÉ—i ko da babu soyayya wannan dalilin ne yasa Zarah taji zuciyarta tayi mata zafi sosai lokacin da É—an'uwanta ya furta kalmar saki a gareta.
Chapter 4 · 0% Book details