Sashe 3
Asp Zarah Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Yana tafe amma zuciyarshi fal tunanin mutanen da yau ne ya fara haɗuwa dasu musamma ƴar su da ta riƙe mishi zuciya lokaci ɗaya yaji kamar sonta na barazanar kamashi, lokaci guda kuma zuciyarshi ta aminta cewa ya samu kalar matar da yake nema a fannin tarbiyya duk da yanason mace wacce tayi karatun boko, fata yake a cikin ranshi Allah yasa babu wanda ya riga shi domin kam bazai yarda yayi rashin wannan kamilar mace ba. Da wannan tunanin ya isa office amma ya kasa taɓuka komai tunanin yadda zai ɓullowa su Daddy da zancen ƙara aure ne ya dameshi musamman da bayaso auran ya wuce nan da wata ɗaya ko biyu.
⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡
Cike da ƙosawa Jiddah ta kalli Raliya dake faman zubda hawaye tace
"Kina daɗa ɓata mana lokaci fa idan ba zakiyi magana bane ki faɗa tun wuri mu samawa kanmu masalaha."
"Bansan ta yaya bane zaku isa ga inda Alpha yake domin nima bansan hanyar inda yake ba bare nayi muku jagora." ta faɗa gami da sunkuyar da kanta ƙasa.
Cikin ɓacin rai Jummai ta kawo mata duka saidai bata kai ga isarta ba Zarah ta tare ta tana faɗin.
"Sassauta Jummai abinda ta faɗa gaskiya ne amma tsaya muji ƙarashan zancen" komawa baya Jummai tayi tana huci kamar wani firgitaccen zaki.
"Ke muke saurare Raliya bamu da lokacin da zamu cigaba da zama anan."
Shiru tayi na wani lokaci kafin tace
"An haifeni ne a garin Jos, ni kaɗai ce ƴar da iyayena suka haifa kuma mahaifina hamshakin mai kuɗi ne na ban mamaki yana da dukiyar da shi kanshi bai san adadinta ba, watarana sai harƙalla ta haɗasu da Alpha batare da yasan ko shi waye ba. A zahiri Alpha dukiyar mahaifina kaɗai yaso karɓa amma ganin mahaifin nawa yasan wasu daga cikin sirrikanshi yasa watarana da daddare yazo har gida ya same mu ni da iyaye ya basu zaɓin ko ya barsu a raye ya kasheni ko kuma ya barni a raye ya kashe su. Haka ina ji ina gani ya bani bindiga na kashe iyaye na da kaina, daga nan ban kuma sanin inda kaina yake ba sai lokacin da na farfaɗo na tsinci kaina a Alpha Villa." wani gauron numfashi taja mai bayyana abinda take faɗa yana mata zafi a rai kafin ta cigaba da cewa
"Bahagowar Rayuwa muke yi acikin wannan gida ni da wasu daga cikin matan da yanayin rayuwa yakai su wannan wajen, na daɗe kafin nasan wasu daga cikin abubuwan dangane da Alpha a lokacin ne nagane cewa ba shi ne yaje ya samu mahaifina ba wani yaronsa ne domin a yadda ake bani labari babu wanda ya taɓa ganin wani ɓangare na jikinsa wanda za'a iya shaida shi dashi, tun daga lokacin na ɗau alwashin sanin wani abu dangane dashi. A haka na cigaba da neman kusanci da shi har zuwa lokacin da nayi nasarar ganin faratanshi waɗanda zan iya ganewa a ko'ina idan naga mai kalansu ko shi ɗin, bayan ya gano ni ne kuma ya saka aka shigar dani ɗakin duhu inda anan yake horar da yaran dake mishi akai. Ta haka ne nasan Alpha sosai har na kamu da sonshi matuƙa duk da har yanzu bai taɓa bayyana kanshi gareni. Na rantse da sarkin dake busamin numfashi wannan ne iya abinda nasani game da shi ko da kuwa zaku bani qur'ani na dafa iyaka gaskiya ta kenan." daga haka ta cigaba da rera kuka a hankali ta barsu kowanne da abinda yake saƙawa a ranshi.
Zarah ce ta fara katse shirun ta hanyar tambayarta tace
"A wani mataki kika tsaya da karatu kafin afkuwar wannan lamarin."
"Ina shekarar farko a jami'ar Jos na fara karantar Mass com."
Shiru suka kuma yi duka na wani lokaci babu mai tankawa kafin Jiddah tace
"Akwai wani ɓoyayyen al'amari da kika sani dangane da rayuwarsa ko wani nasa?"
Kusan mintuna uku kafin ta É—ago tace
"Ehh na taɓa karanta wani kundin sirri a ɗakinsa, akwai wata da naga hotonta da sunanta Phalmata."
A tare suka kusan haÉ—a baki wajen faÉ—in
"Phalmata.??" fuskar Zarah da Jiddah cike da mamaki.
"Meye alaqarsu da ita."
"A yadda na karanta na fahimci cewa ita kishiyar mahaifiyarsa ce kuma tare suka fara duk wannan harkallar, a yadda na gani ma ita kaÉ—aice yanzu a duniya tasan sirrikanshi na da dana yanzu. Inajin idan kuka nemeta zata iya sanar daku komai akansa musamman a yanzu da suke halin gaba zaku fi samun ingantattun bayanai."
"Kinsan wani abu dangane da inda zamu sameta ne."
"Eh toh ita É—in fasihiyar na'ura ce bayan haka kuma tana Æ´an tsibbace tsibbace, ina ganin ta hanyar tsibbu ne kaÉ—ai zaku iya isa gareta."
"A ina take.?" Saleem ya tambaya cike da ƙosawa domin shi burinshi kawai yaji inda zasu samu wannan matar
"Tana garin Dutse a Jigawa."
"Zaki iya tuna adireshinta da kika gani a kundin."
"Eh zan tuna harda fuskarta ma domin yanzu ba ita kaÉ—ai take aiki ba kamar dai Alpha, idan ba sanin wani abu nata akayi ba zata iya haÉ—a mutum da wata daga cikin masu yi mata aiki a matsayin itace."
Miƙewa Zarah tayi tana gyara tattarewar da kayanta yayi saboda tsugunno da tayi, kana ta kalli abokan tafiyar tata tace
"Muje koh? Jummai ke kuma zuwa gobe ki wuce da ita gidanki ta cigaba da zama acan amma ki tabbatar da tsaro."
"Toh ranki ya daÉ—e Allah ya tsare."
Da haka suka fice zuwa inda motarsu take, kai tsaye office É—in Zarah suka wuce domin tattaunawa.
"Zamu É—aukarwa Raliya malamin dazai dinga koya mata zane-zane domin lallai da taimakonta ne zamu samu zanen hoton Phalmata da yatsun Alpha." cewar Zarah bayan sun zauna zaman tattaunawa akan matsalar.
"Nima nayi tunanin haka, amma bakya ganin koyamata zai ja lokaci? Ina ganin a neme mai zanen kawai ta dinga fasalta mishi ya zana koh."
"A'a Saleem yarinyar tana da kwakwalwa sosai zata koya cikin ƙanƙanin lokaci musamman idan muka mata barazana, da kanta zata fi iya zana komai da ta sani ba kamar idan faɗa take yi ba."
"Wannan haka yake, amma tsawon wani lokaci kenan.?"
"Sa-Jid yau muna ɗaya ga wata, a cikin sati ɗaya Raliya zat gama koyan zane tare da yi mana zanen da muke buƙata, a sati biyun da zasu biyu baya na binciko inda Phalmata take ne, a satin ƙarshe na wannan watan kuma zanje Abuja na neme takardar shaidar kama Alpha kunga kenan a wata ɗaya zamu gama wannan task ɗin muje na gaba wato binciko inda Alpha yake tare da kamashi."
Tafi suka mata cikin jinjina da barkwanci, Saleem ne yace
"Wani lissafin Æ´an sanda ne kaÉ—ai zasu iya shi."
Murmushi kawai tayi sannan tace
"Zanyi magana da Daddy idan yaso shi sai yayiwa M.J maganar tafiyarmu Zamfara"
"Shikenan wato har yanzu kunƙi sasanta kanku" cewar. Saleem
Bata ce komai ba ta fara haÉ—a abubuwanta domin tafiya gida, tare suka fito ta shige motarta bayan sunyi sallama sannan suma suka tada motarsu suka wuce.
A kwanakin da suka biyo baya sam Zarah bata zauna a gida ba saboda ta tsaya kai da fata wajen ganin Raliya ta koyi abinda suke buƙata, a ɗaya ɓangaren kuma suna shirye-shiryen tafiya Zamfara ita da ɗan'uwanta Sadiq da kuma Jiddah da Saleem domin tafiyar da zasuyi ba ƙarama bace saboda adireshin da Raliya ta basu yana da nisa da garin dutse sosai dan haka suna buƙatar su shirya sosai.
Wannan dalilin ne yasa kwata-kwata basu haÉ—u da M.J ba.
💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕
A ɓangaren M.J da Hajara kuwa soyayya da shaƙuwa mai ƙarfi ne ya shiga tsakaninsu, basa iya ɗaukar dogon lokaci batare da sunji muryoyin juna ba. Da fari Hajara tanason auran M.J ne saboda kuɗinshi saidai daga baya ta gane shine irin mijin da take so kuma gashi ta samu dan haka ne ma tayi alwashin cewa idan akayi aurensu ta gama aikin da zata yiwa Alpha zata cigaba da zama da mijinta domin ta samu kalarta. Shima a nashi ɓangaren yana mamakin yadda cikin ƙanƙanin lokaci ya kamu da matsananciyar soyayyarta.
Takurawar da Malam Surajo ke mishi akan idan yanason Æ´arsa ya turo magabata ne yasa yau yasha alwashin bayan ya tashi a aiki zai biya ta gidan ya sanar musu komai zai faru ya faru.
Ƙarfe shida ya tashi a office kai tsaye kuma gidansu ya nufa, saida ya tsaya yayi sallar magriba a masallacin dake unguwar kafin ya ƙarasa zuwa cikin gidan nasu.
A harabar gidan ya ga motar Zarah hakan ya tabbatar masa cewa tana cikin gidan, ba ƙaramin daɗi yaji ba kuwa domin yana son duk abun da za'ayi ayi a gabanta. A babban falo ya tarar da su duka suna ƙoƙarin yin dinner Daddy, Momi, Sadiq da kuma Zarah, dan haka shima kai tsaye teburin ya nufa da suci abincin tare. Gaishe da iyayensa yayi kana ya baiwa Sadiq hannu suka gaisa fuska babu yabo ba fallasa ko da Zarah ta gaidashi sharewa yayi batare da ya amsa ba wanda duk su Daddy sun lura da hakan amma babu wanda ya tanka haka suka fara cin abincin cikin nutsuwa kowa da abinda ke ransa.
Bayan gama cin abincin kuwa cikin falon suka koma suna hira har kaÉ—an kaÉ—an, cikin dakiya da dauriya tare da fargaba M.J ya buÉ—i baki yace
"Ehhmm Daddy dama nazo muyi magana ne."
Tun farkon shigowar shi Momi ta fahimci akwai abinda ke tafe dashi amma sai ta basar batayi magana har yanzu da ya furta da kanshu, murmushin manya Daddy yayi kana yace
"Ina jin ka."
Shiru ya kuma yi har sai da Daddy yace
"Ko maganar na buƙatar sirri ne."
Cikin hanzari yace.
"A'a ba wata magana ba ce, dama ehmm dama iyayen yarinyar da nake nema ne suka ce na turo magabata na ayi magana, a taÆ™aice dai aure nakeson Æ™arawa."...âœðŸ»
_BY_
_JASMINE_.🌸🌸
*ASP ZARAH*👩â€âœˆï¸
*BOOK 2*
*Page 4*