← Book details Asp Zarah Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 8 OF 18

Sashe 8

Asp Zarah Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"A wani garin marasa hankalin aka taɓa aikata haka Sulaimanu? Kana nufin kenan Muhammadun ya fi ƙarfin ka eyeee. Kai ba za ka iya masa hukunci ba kenan har sai ka dangana da wasu a waje, kai ne uban ko shine? Ban yarda ba, ban amince ba, matuƙar na isa da kai toh ban yarje maka ka kai ƙarar Muhammadu kotu ba." Baaba ce ta yi wannan zance.
"Baaba laifin da Jawwad yayi mai girma ne, ko da Gwamnati ne ta ji labarin abinda ya aikata ba zata barsa ba, ki bari kawai a hukunta shi." Cewar Momi

"A'a ban yarda ba a nemi wata hanyar hukunta shi amma ba ta hanyar kotu ba."

"Ko da yaushe wannan tsohuwar sai kin kaucar da mutane akan hanya." Sadiq ya faÉ—a.

"Ka kiyayeni fa Habu, ba na wasa da kai."

"Shikenan Baaba za'ayi yadda kike so, amma wannan karon Jawwad ya ɓata mana rai matuƙa dan haka zan yanke masa hukunci mai tsauri." Inji Daddy.

"Yauwa ɗan albarka ai idan rai ya ɓaci hankalj baya gushewa."

Daddy ne ya maida kallonsa inda M.J da Hajara ya ce
"Ka tashi ka tafi banaso na ƙara ganin fuskarka."

"Dad-dy!" M.J ya faÉ—a cike da rauni.

"Ehh ka tafi Jawwad ba ma so ƙara ganin fuskarka a cikin mu." Momi ta faɗa cikin hawaye.

Gwiwarsa ya zube a ƙasa da nufin ba ta haƙuri sai dai ta riga shi da faɗin

"Ka bani kunya Jawwad, wallahi da nasan akwai ranar da zata zo da zaka yi sanadin shigata baƙin ciki kamar yadda nake ji a yanzu, da tun kafin Allah ya bani cikin ka zan roƙe shi ya hanani cikin ka, Allah ya jiƙan Rahama ko da ɗaure fuska nayi cikin wasa sai hankalinta ya tashi, kai da nake tunanin zaka maye min gurbinta sai gashi kaine mai son kashe ni da baƙin cikin ka, Allah ya w...."

"Kul! Kada ki yarda ki ƙarasa, kin san munin da tsananin da fushin iyaye ke jawo wa ƴaƴan su kuwa? Banason ƙara jin kunyi mugun furuci akan yaron nan." Baaba ta katse Momi da ke magana cikin tsananin fusata.

GabaÉ—aya ya firgice da kalaman iyayensa, ya san fushin su akan sa babban musiba ne a gareshi, hawaye ne suka fara sintiri a kuncinsa.

"Matuƙar na buɗe ido na same ka a ɗakin nan ban...✍🏻✍🏻

*BY*
*JASMINE*🌸🌸

*ASP ZARAH*👩‍✈️

*BOOK 2*

*Page 7*

..."Matuƙar na buɗe ido na same ka a ɗakin nan ban yafe maka ba." Momi ta yi wannan furucin cikin zafin rai.
Da hanzari ya miƙe ya fice Hajara ma ta miƙe ta bi bayan shi ba ta re da ta ce komai ba. Nan Baaba ta rufe Momi da Daddy da faɗa, ta inda ta shiga ba ta nan take fita ba, su dai sai haƙuri kawai suke bata, daƙyar suka samu ta daina faɗan.
A wannan ranar ma tare muka wuni da su cikin kulawa, wajen ƙarfe tara na dare ne muna zaune sai sallamar Ammi muka ji, cikin mamaki nake kallonta Momi kuwa sai dariya ta ke min tana faɗin dama taki sanar da ni ne saboda zumuɗi irin nawa. Cikin murna muka gaisa tana tambayata yanayin jikina, ko da lokacin tafiya yayi sai Ammi ta ce nan zata kwana, daƙyar aka samu Jiddah ta bi Saleem suka tafi gida. Tare muka kwana da Ammi tana bani kulawa kamar zata maida ni ciki.

Kwana na goma a asibiti kuma naji sauƙi sosai sakamakon kulawar da likitoci suke bani a gefe guda kuma ga kulawar da su Momi ke ba ni. Tun waccan ranar kuwa ban ƙara saka M.J a idanuna ba, saboda su Momi sun ɗau zafi sosai, Ammi ce ma wani lokacin nake jin su suna magana a waya wanda yawanci roƙonta ya ke akan ta baiwa su Daddy hakuri akan fushin da suke yi dashi. A yadda na fahimta, ko kaɗan abinda ya same ni bai damu M.J ba fushin da iyayensa ke yi da shi ne kaɗai abinda yake damunsa. Kayana da ke gidansa kuwa tun waahegarin da Ammi ta zo suka je da Jiddah aka kwashemin aka maida min gidan Daddy, part guda aka waremin tamkar wata matar gida.

Gabaɗaya mun gama shirin tafiya Enugu sallamar likita kawai muke jira, dama na riga da na jima da karɓar takardar shaidar kama Alpha dan damƙa shi a hannun hukuma a ko wani hali, dan haka abinda kaɗai nake jira shine na ƙarasa warwarewa don mu tafi Keruba. Tafiyar ta mutane bakwai ce Ni, Sa-Jid, Yaya Sadiq, sai wasu jami'aina na sirri guda uku da zamu yi tafiyar tare.

A daren da na cika sati biyu ne a asibiti likita ya sallameni inda a washegarin ranar kuma zamu wuce Enugu, tafiyar da bamu da tabbacin ko zamu yi nasara, haka dai muke ta shiri zuciyoyi sam babu dadi.
Kasancewar tafiyar mota zamu yi yasa washegari da asuba bayan munyi sallar asuba muka yi sallama da su Daddy muka É—auki hanyar tafiya cikin motoci biyu.

Sallah kawai ke tsayar damu a hanya amma duk da haka ba mu isa cikin garin Enugu ba sai wajen sha biyu na dare, hotel ɗin da muka kama ta internet muka nufa kai tsaye ba mu sha wahalar ganewa ba saboda munyi amfani da google map, cikin lokaci ƙanƙani muka isa wajen.
Bayan karɓi makullan ɗakin ne muka wuce don kowa ya huce gajiyar da ke tattare da shi.

Kwananmu biyu muna huce gajiyar hanya kafin ranar asabar da yammaci muka shirya tafiya garin Keruba kamar yadda aka kwatanta mana zuciyoyin mu cike da zullumi duk kuwa da kasancewar a daren wannan ranar kwana muka yi sallah muna neman zaɓin Allah a cikin lamarin. Sai Yamma lis kafin muka isa cikin garin wanda yake da kyawun tsari, duk da mun baro arewacin Najeriya a bushe amma wannan yankin ko ina da damshi alamun dai basa dadewa ba ta re da ruwan sama ba. Wani ƙaramin masauki muka kama don mu kwana a ciki kafin washegari mu ƙaddamar da abinda ya kawo mu. Wannan dare kwana nayi a gaban maliccina ina kai mai kukana ya taimaki ne akan abinda na sa gaba. Wallahi ban taɓa sanin cewa addu'a na da wannan ƙarfin ba sai a washegarin wannan dare, ban taba tunanin abubuwa zasu zo mana da sauƙi ba sai a lokacin na tabbatar cewa babu kamar hawayen wanda aka zalunta a wajen Allah.

Washe gari kamar yadda aka faɗa mana cewa Alpha na fita zagayawa a gari cikin ɓadda kama haka muma muka shirya ɓadda kama tamkar wani shirin film. Duk da cewa cikin Jiddah bai wani girma ba amma a haka muka yi amfani da ita. Kasancewarsa mutum mai kaifin basira yasa ba mu yi tunanin yin ƙaryar yin dressing da bandage ba gudun karya gane ƙarya muke yi. Dole ta sa aka yi wa Jiddah rauni a jikinta, duk yadda ta so daurewa sai da ta kasa na gane cewa tana matuƙar jin zafi a jikinta.

Kayan masu aikin Momi da muka karɓo muka saka sannan wata daga cikin jami'an nan ta shafa mana wani abu a fuska da jiki wanda idan ba mutum ya sammu sosai ba bazai gane mu ba. Tunda wuri muka yi wa hanyar da Alpha zai bi tsinkaye, cikin tsananin shiri da taka tsantsan.
A tsakiyar hanya muka zauna Jidda ta kishingiɗa ta yi matashi da cinyata, kasancewar a yanki kudu kowa harkar gabanshi yake yi ya sa babu wanda ya kula da lamarin mu kowa ya zo wuce wa yake yi batare da ya tambayi dalilin da yasa muke zaune a gurin cikin wani yanayin da babu kyan gani ba. Mu na zaune a wajen har kusan mintuna talatin ni da Jiddah, yayin da su Saleem ke can nesa a ƙasan wata bishiya suna zaune.

Tun daga nesa na hango tahowarsa, kallo ɗaya zaka masa ka fahimci cewa yana taƙama da izza saboda yanayin yadda yake tafiya tamkar mai tausayin ƙasa, duk da shiri ne amma ni da Jiddah mun gaji sosai kallo ɗaya zaka mana kasan mun galabaita. Magana nayi a hankali na sanar da Jidda tahowarsa, ai kuwa tuni ta fara juyi kamar wacce ke naƙuda alhali cikin nata wata 3 ne kacal, ƙamshin turarensa kaɗai ya isa sanar da cewa mai kuɗi ne na gaske, domin indai hancina ya jiyo min ƙamshin nan daidai Abbana yana amfani da kalan turaren nan sanda yake da rai, saboda akwai watarana da na dage sai ya bani kyautarsa shine Mami ke gayamin kuɗin turare yakai dubu ɗari uku.
Cikin takun ƙasaita yazo ya wuce ta gefen mu ba ta re da ya kalli ko gefen da muke ba, take naji hawayen rashin nasara sun sauko daga idanuna, har ya ɗan yi nisa naga ya tsaya sannan ya juyo ya nufo inda muke, farin ciki ne ya kamani dakyar na saisaita kaina gudun matsala.

"Sannunku bayin Allah" Sautin muryarsa naji ta daki kunnena, zan iya rantsewa tun da nake a duniya ban taɓa jin wata murya mai zaƙi irin tasa ba, mintsilin da Jiddah ta yi min a gefen cinya ne ya dawo da ni da ga duniyar tunanin da na tafi. Cikin sanyi na amsa mai da
"Yauwa sannu" na kauda kaina gefe ina matsar kwalla.

"Me ya sa kuke zaune anan gurin da babu tsabta haka."

"Ƴar uwa ta ce ba lafiya cikinta yana ciwo, kuma akwai ƙaramin ciki a jikinta shiyasa na zauna anan mu ɗan huta ta ce ba zata iya tafiya ba." Na faɗa cikin rauni.

"Subhanallah! Taimako ya kamata ke nema a kaita asibiti ai, ciwon cikin masu juna biyu ai ba daÉ—i." Ya fada da alamun ruÉ—ewa a tare dashi. Bance komai ba illa kwallar da na cigaba da matsa kamar wacce ke cikin wani babban tashin hankali, wata tsadaddiyar waya ya ciro a aljihunshi ya fara dannawa ya ce
"Bari na kira Æ´ar uwata ta taimaka sai mu kaita asibiti."
Chapter 8 · 0% Book details