← Book details Asp Zarah Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 5 OF 18

Sashe 5

Asp Zarah Part 2 Complete Hausa Novel · about 7 min read

"Kinsan abinda ya kawo mu dan haka ki bamu salin alin saboda yau zamu yi ta mukare tsakanin mu da ke." Mutumin ya kuma faɗa batare da ya kula da halin da take ciki ba, kauda kai tayi gefe tana addu'ar Allah ya bata nasarar kunce kanta duk da suna da yawa tasan zata iya musu mugun lahani ba tare da makami ba ma. Saura ƙiris ta fasa ƙara saboda wani gigitaccen zafi daya ziyarce ta a gefen cinyarta, kallonta ta maida gurin taga ashe ɗaya daga cikin matan nan ne ta yi mata muguwar yanka a cinyarta take kuwa jini ya ce dama hanya nake nema nan ya fara zuba tamkar kwararo shi ake yi, raɗaɗi take ji sosai amma hakan bai sa ta amsa tambayar da ya kuma mata ba, ya ce
"Ba zakiyi magana ba ke wace iriyar yarinyace mai taurin kai ne, mtsssw ku shiga ku bincika min ko ina a cikin gidan nan."
Dukkansu suka nufi hanyar da suka ga Zarah ta fito mutum uku kaɗai suka bari biyu na tsare da M.J da Hajara sun saka musu bindiga akai sai babban dake gefen inda Zarah ke ɗaure yana wasa da wuƙar hannunshi yayinda ɗaya hannu ke rike da bindiga. Kusan mintuna arba'in suna dube-dube a cikin gidan amma basu ko ga wata alamar da zata nuna musu cewa Diamonds ɗin suna cikin gidan ba, cike da rashin kwarin gwiwa suka dawo suka sanar da shi, bai ce komai ba ya zaro waya ya daddanna sannan ya kara a kunnenshi jim kaɗan ya fara magana yace
"Yallaɓai jiya i yau fa, taurin kan yarinyar yayi yawa ta tushe kowace hanya bata bamu damar sanin komai ba."
Huci ya furzar mai zafi kana yace
"Wannan karon inaso ku taɓa Zarah, ina so taji a lafiyarta cewa ba'a gardama dani, ina so taji lallai cewa bazata iya cigaba da ajiyar Diamonds ɗin nan ba, lallai ku yi mata mummunan lahani kamar yadda zuwa yanzu na tabbatar idan Raliya tana raye to tana cikin mawuyacin hali."

"Angama ranka ya daÉ—e." daga haka ya katse wayar ya kalli matan dake tsaye ya ce
"Ku cika aiki" tamkar suna jira haka suka ruftu su biyar akan Zarah kowa da irin dukan da yake kai mata amma duk da haka ko tari bata yi ba bare ayi tunanin zatayi kuka.
Karo na farko Hajara taji mugun tausayi da dana sani sun baibayeta, ciwon Æ´a mace na Æ´a mace ne, sosai taji da na sanin haÉ—a kai da ita da akayi tun farko har zuwa yau da suka shigo cikin gidan nasu. Shikuwa M.J ba yadda za'ayi ka gane yanayin da yake ciki domin fuskarsa tana nan yadda take.
Cikin mintuna ƙalilan farin tiles ɗin dake falon ya fara rinewa yana yin ja saboda jinin dake gangarowa daka jikin Zarah sakamakon bugu da yanka da suke jikinta, ganin kamar ta daina numfashi ne yasa ya dakatar da su sannan suka fice a gidan.
Da hanzari Hajara ta rarrafa ta isa kanta hawaye na biyowa a idanunta ta juya ta kalli M.J ta ce
"Hubby É—auki key da sauri mu kaita asibiti."

"Ni? Asibiti? Babu inda zan fita da daren nan, ita ta jawo wa kanta."

"Ka dubi halin da take ciki mana dan Allah ka taimaka."

"Yaya Jawwad dan Allah ka kiramin Daddy ko da bazaka kai ni asibitin ba." Zarah ta faÉ—a a galabaice, numfashinta na fita É—aiÉ—ai.
Bai kula ta ba ya zo yaja hannun Hajara suka nufi ƙofar part ɗin shi, tsayawa yayi cak! Sannan ya dawo ya tsugunna a gabanta yana ƙare mata kallo shi kansa yasan tana buƙatar taimako na gaggawa amma yana jin zafinta sosai a ƙasan zuciyarsa, gyaran murya yayi sannan yace
"Kinsan yanzu babu igiyar aure tsakanina dake, dan haka zan taimaka miki ne kaÉ—ai a matsayin karuwar da nakeso ta tuba ga Allah kafin ta mutu, wannan ne kaÉ—ai gatan da zan miki, kin amince na taimaka miki.?"

"Zan fi ƙaunar na mutu a haka matukar da wannan ƙudurin zaka taimake ni, na tsane ka, baka da tausayi ko kaɗan, kai mara imani ne."

KafaÉ—a ya kaÉ—a ya mike sannan yace
"Duk yadda kika gani sai ki kira wanda kike jin shi zai iya taimakonki ko a cikin abokan watsewarki ne." daga haka yaja matarsa suka shige suka barta a nan kwance.
Cikin dakiya da juriya ta miƙe zaune tana jan jiki harta isa ƙofar da zata sada ta da farfajiyar gidan cikin tsananin azaba da ciwo.

A firgice ta miƙe daga baccin da take yi, juyawa tayi ta kalli agogo 2:05am kallonta ta maida kan Saleem dake sharar baccinsa hankali kwance, a hankali ta fara bubbuga bayansa har ya farka ya buɗe idanunsa ganinta a zaune ne yasa shima ya zauna yana miƙa ya kalleta yace
"Lafiya kuwa me ya same ki.?"

"Sa-Jid nayi mafarki Zarah na ta kirana tana faÉ—in na taimaka mata, zuciyata da jikina sun amsa bana jin daÉ—i sam ina da tabbacin cewa akwai abinda ke faruwa da ita."

"Me zai faru da ita da wannan daren haba dan Allah mafarki fa ba gaskiya bane."

"Na sani amma dai wannan yayi kama da gaskiya, miƙomin wayar can na kirata."

Hannu yasa ya ɗauko wayar dake kan bedside drawer ya bata, cikin hanzari ta fara danna lambar Zarah tana kira amma kusan kira 30 babu amsa. Zuwa lokacin ta gama ruɗewa, kuka ta sakawa Saleem akan lallai sai ya kaita gidan Zarah a daren duk yadda yaso ta haƙura amma taƙi, sanin da yayi cewa idan damuwa zata iya jawowa ƙaramin cikin dake jikinta matsala ne yasa dole ya miƙe ya zura jallabiya ya ɗauki key ɗin motar suka fice a gidan, har zuwa lokacin kuma bata daina kuka da sambatu ba...✍🏻

*BY*
*JASMINE*🌸🌸

*ASP ZARAH*

*BOOK 2*

*Page 5*

... Su uku ne zaune a cikin wani ƙayataccen falo da yaji kayan alatu tamkar na shugaban ƙasa Sadiq, Rahma da kuma Zarah, kallo ɗaya zaka musu ka gane suna cikin tsantsar farin ciki da suka daɗe basu samu ba duba da yanayin yadda fuskokinsu suka kasa ɓoye farin cikin da suke ciki. Rahma ce ta ajiye cup ɗin dake hannunta a center table ɗin dake gabanta sannan ta juyo ta dubi Sadiq dake nunawa Zarah abu a waya suna ƙyalƙyala dariya ta ce
"Bazan iya tuna ranar ƙarshe da naga dariyarku haka ba musamman Zarah."

"Ba mu da wata sauran damuwa ne shiyasa ki ka ganmu haka, ke ba abin farin ciki bane a gareki ace yau wanda yayi sanadin da iyayenmu suka bar duniya shima ya mutu ta dalilinmu, baya ga haka Æ´ar'uwar mu wacce muke tunanin ta zauce yau ta samu lafiya ingantacciya, kinga kuwa dole mu yi farin ciki." Sadiq ne yayi wannan sharhin bayan ya maida hankalinsa kanta.

GyaÉ—a kai tayi ciki da gamsuwa tace
"Haka ne amma naku ne kawai ke fitowa fili, nawa na barshi a zuci."
Zarah waccw tun da aka fara maganar bata tanka ba ta É—ago tace
"Meye zai hana ki fito dashi fili mu haÉ—u mu yi murnar tare."
Cike da zolaya Rahma tace
"Yau kam naci girma na bar muku."
Ɗaya daga cikin ƙananun pillows ɗin dake kan kujerar Sadiq ya ɗauka ya jefeta da shi cikin harara yace

"Ke banson raini fa"

Itama cikin zolaya tace
"Kwanaki ƙalilan a ne tsakaninmu fa."

"Duk da haka dai ya riga ki shaƙar iskar duniya." Cewar Zarah.

"Haka ne toh na baka girman ka, yanzu daga nan ina zaku wuce."
Shiru sukayi na wani lokaci kafin Sadiq yace
"Daga nan Malasia zamu wuce, Little zata fara karatun masters É—inta acan, ni kuma na cigaba da aikina."
Fuska ta sauya kamar zatayi hawaye tace
"Za mu ƙara yin nisa da juna.?"

"Ki shirya mu tafi tare." fadin Zarah.

Hararar wasa ta mata sannan ta kuma cewa
"Na gaji da kawaici fa, tun É—azu inaso ku É—auko min hirar abubuwan da suka faru amma kun share."
Dariya suka yi duka sannan Sadiq yace
"Tun É—azu na lura dake kawai na yi miki shiru ki furta da bakinki."

"Na tambaya yanzu a gayamin meya faru."

"Labari ne mai tsawo fa ki nemo biro da takarda" Inji Zarah.

"A'a bani wannan baiwar sai dai na kira Sis Jasmine ta mana aikin rubutun."

"Tom shikenan haka za'ayi."

"Ke nake sauraro."

🩸🩸🩸🩸🩸🩸🩸🩸🩸
Chapter 5 · 0% Book details