← Book details Asp Zarah Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 17 OF 18

Sashe 17

Asp Zarah Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Wasu hawaye masu zafi ne suka sauko daga idanunta, duk da ance mafarki ba gaskiya bane itakam wannan gaskiya ta É—auke shi dan a fahimtarta iyayenta dake kwance cikin kabari basa jindadin abinda take aikatawa. Amma ya zatayi takasa cire Safwan din a ranta, bawai bata yafewa M.J abinda ya aikata mata bane amma tana jin ciwo ace ta rayu da shi a maimakon Safwan din da take buri.
Sai dai wannan mafarkin lokaci guda ya sauya tunaninta ta saka a ranta cewa zata yi ƙoƙarin ganin ta sauke haƙƙin aurenshi da Allah ya ɗaura mata. Istigfari ta fara tana neman yafiyar Allah dan tasan ba ƙaramin zunubi ta kwasa ba a zamanta da M.J din, shi Allah babu ruwansa da tanaso ko bataso haƙƙin da ya rataya a wuyanta kawai zata sauke idan kuma takasa zunubi ne a kanta, tabbas tasan hukuncin macen da bata yiwa mijinta biyayyah ba a gurin Allah kaɗai hatta mala'iku da sauran halittu kullum cikin tsine mata suke yi.

Kuka ta ƙara fashewa da shi har da sheshsheƙa zuciyarta na mata zafi sosai, M.J dake tsaye gaban Dinning yana jera abinci ya jiyo sautinta ai da gudu ya nufo ɗakin. Tana nan a zaune tana kuka, da hanzari ya nufi inda take yana tambayarta meya faru sai dai bata bashi amsa ba. Zama ya yi yana rarrashinta tare da bata haƙuri dan a zatonshi shine ya mata laifin.
Sun dade a haka kafin ta sassauta kukan tana sauke ajiyar zuciya, toilet ya shiga ya hada mata ruwan dumi sannan yace taje tayi wanka, mikewar da zatayi jiri ya ɗebeta luuu! Ta kuma zata fadi ya tare ta. A hankali ya ɗauke ta ya shigar da ita bayin, da kanshi ya mata wankan ganin lokaci guda zazzaɓi me zafi ya rufeta sai rawar ɗari take yi. Riga kawai ya zura mata bayan ya fito da ita sannan yaje ya hado mata tea me kauri ya haɗo da Paracetamol, dakyar tasha Tea din kaɗan ya bata maganin sannan ta kuma ta kwanta.
Ganin har rana jikin nata yaki sauki ne yasa ya kira Abdallah ya mata allura sannan ya ɗaura mata drip, falo suka koma suna tattauna matsalar M.J din Abdallah na ƙara bashi shawarwari akan wannan ce kaɗai damar da zaiyi amfani da ita wajen sasanta tsakaninsu da Zarah, sun dade kafin ya maj sallama ya tafi.

A takaice dai sai da Zarah tayi sati tana jinya har su Momi sai da suka zo dubata, ranar da Sadiq yazo gaisheta da jiki saida yayi mamakin abinda yaga M.J na yi mata, M.J ɗan kwalisa da shan ƙamshi amma shine ya ƙasƙantar da kanshi akan mace, dan a kitchen ma ya taddashi yana soya wainar fulawa wai Zarah take son ci, tun abin na bashi mamaki har ya koma tausayin M.J din ganin gabadaya bashi da wani lokaci da zai yi abin kansa sai wanda tace dashi, hakan yasa ya musu sallama ya tafi a yanzu hankalinshi ya kwanta da auren nasu.

Shikuwa M.J duk wannan abin da yake yi sam baya damunshi musamman da a yanzu ya samu sake har kwana yake yi a ɗakin Zarah kuma bata hanashi wani lokacin ma har hira suke yi sosai musamman idan suna kallon labarai aka taɓo harkar tsaro nan zasu zauna suna tattaunawa akan halin da ƙasar mu ke ciki ta fannin tsaro.

Da haka zaman nasu ya fara daÉ—i ko bayan da ta warke, kullum tare suke bacci watarana a É—akin M.J din ko a É—akinta, tare suke tashi su kimtsa gidan kowacce safiya dan Zarah ta tubure batason me aiki duk da M.J yaso ya É—auki me taimakamata dole ya hakura tunda ta nuna bataso. Tare suke fita ya sauke ta a wajen aiki kafin ya wuce nashi wajen aikin idan an tashi ma haka zai zo ya É—auketa su wuce gida wani lokacin kuma gidan Momi suke wucewa.
Da haka dai har M.J ya hillaceta haƙarsa ta cimma ruwa, aikuwa ranar ya sha kuka da nadamar abubuwan da ya aikata mata har sai da ciwon shi ya tashi, hakuri kuwa har sai da ta nuna zatayi fushi sannan ya daina bata.

Zaman da ya biyu baya babu laifi zamane na aminci da kyautatawa juna duk da har a lokacin Zarah ba sonshi take yi ba kuma bata manta da Safwan cikin ranta ba dan kullum idan tayi sallah sai ta mai addu'a shi da iyayenta da sauran musulmai magabata.

Babu irin gatan da M.J baya mata wani lokaci har tausayi yake bata idan taga irin kulawar da yake bata, komai nashi ita ne duk abinda ya samu ita.

A cikin watannin da suka biyi baya ne watarana M.J ya tashi da wani irin zazzabi me zafin gaske, sosai hankalin Zarah ya tashi dan har sumewa yake yi da ya farfaÉ—o kuwa zai kuma ba shiri ta kira gida ta sanar sannan ta kira Abdallah suka É—auke shi sai asibiti.
Kwananshi biyu amma duk allurai da magungunan da ake bashi kamar ba'ayi har anfara tunanin ko ciwon bana asibiti bane.

Ranar da Baaba tazo asibitin ne ta gane ainihin musabbabin ciwon, suna zaune harda su Momi da Jiddah dan lokacin dare ne anyi sallar isha'i ma, kallon Zarah tayi sannan ta kalli M.J ta tuntseri da dariya sosai har tana saukowa daga kan kujerar da take, kallonta suke yi cike da mamaki, Sadiq ne ya rike baki ya ce

"Momi bari na kira likita inajin matar nan ba kalau take ba."

Jin abinda ya faÉ—a ne yasata tsagaitawa ta kalleshi ta ce

"Zan saba maka fa Habu ni kake dangantawa da taɓin hankali."

"Alama kika nuna ai" ya fada yana kauda kai.

Tsaki tayi sannan ta maida kallonta ga M.J dake kwance cikin ciwo tace

"Wato dai kai Muhammadu da gaske kake so ka zama mijin tace koh? Ita ke da cikin amma kaine kake mata laulayin."

"Laulayi kuma Baaba.?" Momi ta tambaya.

"Yoo ai sai kuyi kuma sau nawa akayk muka gani Zara'u ce fa ke da ciki shi kuma yake mata laulayin cikin dama ana samun haka wasu lokutan idan mata ta samh shigar ciki ta hanyar mijinta kaÉ—ai ake ganewa dan wasu ciwo suke kamar ba zasu rayu ba."

Wani irin farin ciki ne ya sauka a zuƙatansu babu shiri Momi taja hannun Zarah suka fice kai tsaye sashin da ake bincikar masu ciki ta kaita dan ayi mata awo saboda itakam ta yarda da batun Baaba dan a zamanin baya ma kafin wani daga cikinsu ita da marigayiya yasan yana da shigar ciki Baaba ce take fara ganewa ta fada musu kuma idan anje asibiti a tabbatar.
Kasancewar an sansu a asibitin ne yasa babu ɓata lokaci aka shigar da Zarah ɗakin scanning din aka kwantae da ita sannan aka jona mata na'urorin, mintun biyu tsakani kuwa sai ga hoton cikinta ya bayyanah da ɗa kwance, farin ciki ne ya rufe Momi ba shiri ta fadi acan gefe tayi sujjadar godiya ga Allah.

Wani zuben zinari me matuƙar tsada dake hannunta ta cire ta baiwa matashiyar likitar tukwici.

Basu dawo ɗakin ba sai da aka gama buɗewa Zarah file na masu ciki sannan ta riƙo hannunta suka dawo nan take shaida musu fa akwai cikin a jikin Zarah har na wata hudu ma, hamdala suka fara yi tare da gode ma Allah hatta M.J dake kwance sai da ya mike ya zauna sannan ya riko hannun Zarah dake gefenshi yana zuba mata godiya.
A daren yace bazai kuma kwana a asibitin ba tunda angano silar ciwonshi dole haka likita ya sallameshi suka koma gida inda aka bar Baaba dan kulawa da Zarah.
Sanda Rahama taji labari kuwa tayi murna sosai duk da itama a lokacin tana da ciki har ya shiga watan haihuwa.

Tunda cikin Zarah ya bayyana kuma sai ciwon da M.J yake yi ya ragu nan ya cigaba da baiwa matarshi kulawa baya ko kunyar Baaba dake gidan hakan yasa ta tattara kayanta tabar gidan dan tace ba zata iya zama ayi abin kunya a gabanta ba.

Sati biyu da faruwa haka Rahama ta haifi Æ´arta mace. Gabadaya suka tattara suka nufi Yola da sha tara na arziki.
Anyi shagalin suna sosai irin na gidan sarauta,yarinya taci sunan mahaifiyar su Mahmud Zulaihat ana kiranta da Afrah, satinsu guda suka juyo suka bar me jigo cikin kulawar dangin mijinta dan su gidan sarauta basu yarda da al'adar wankan gida ba.

Watan Afrah huÉ—u da kwanaki Zarah ta sauka lafiya ta haihu Æ´an biyunta macw da namiji kyawawa masu kama da ubansu. Farin ciki kuwa ba'a magana a gurin dangi. Nan aka fara cika gidan Æ´an uwa da abokan arziki kowa na zuwa ganin Æ´an biyu.

Ranar suna kuwa ansha mamaki kwarai sunan da M.J ya sakawa yaran, macen Fadimatul Zarah namijin kuma Safwan inda za'a kirasu da Amrah da Amran. Mutane da dama sun jinjina wannan abu da ya yi, ita kuwa Zarah tayi farin ciki matuƙa har ta kasa ɓoye hakan.

Mai Martaba da kanshi sai da yazo ya yi godiyar wannan kara, inda yawa yara kyautan manyan filaye guda biyu bayan kuma kaya da aka kawo musu.
Yara sunzo da goshi dan sun samu kyaututtuka da dama na ban mamaki.

Kulawa sosai suke samu daga wajan iyayensu da sauran dangi. Musamman mahaifinsu ma daya É—aura son duniya akansu.

Haihuwar Zarah ba da dadewa ba aka yi auren Sadiq wanda ya tara manyan mutane sosai sannan an kashe kuÉ—i sosai.

A haka rayuwa ke tafiya awanni na shudewa su bada kwana daga nan satika har watanni.

Watarana su Zarah sun fita shopping, a hanyar dawowarsu ne suka kusa kaɗe wata almajira, ko da suka fita suka duba ba kowa ba ce face Hajara, ƙafarta ɗaya an guntule sai sanda take amfani dashi. Ko da ta ganesu nan ta durƙusa tana basu hakuri sosai tana basu labarin abubuwan da suka faru da ita dan har prison sai da aka kaita sanadin wannan Alhajin daya mata ciki, gashi iyayenta ma duk basu da lafiya suna kwance ƴar uwarta ce kawai ke taimaka musu itama mijinta ya ɗauke ta sun bar ƙasar.
Sun tausaya mata sosai nan M.J ya mata kyautar maƙudan kuɗaɗe bayan sun yafe mata.
Chapter 17 · 0% Book details