← Book details Asp Zarah Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 2 OF 18

Sashe 2

Asp Zarah Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Bata ko tsaya amsa gaisuwar da ake mata ba lokacin data isa gurin aikinsu, kai tsaye office É—inta ta wuce saboda sarawa da kanta yake yi yana mata masifar ciwo, kanta ta kifa a teburin ta fashe da kukan da batasan dalilin yin shi ba.
Tsagaitawa tayi da kukan batare da ta share hawayen dake zubo mata ba jin alamun za'a shigo office É—inta batare da an nemi izini ba, tasan É—aya daga cikin mutum biyu ne ke shigowa ko su duka biyun wato Saleem ko Jidda.
Hannunsu sarƙe dana juna suka shigo bakinsu ɗauke da sallama, cike da mamaki suke kallon fuskarta da ta jiƙe da hawaye, tuni hankalin Jidda ya tashi ta nufeta gadan gadan tana tambayarta abinda ke damunta.
"Babu komai fa Habibaty, kawai kaina ke min ciwo."

Murmushin daya tsaya iya baki Jiddan tayi kafin da zauna shima Saleem ya zauna akan kujerun dake fuskantarta, shiru Jidda tayi ta ƙura mata ido tanason gano abinda ke damunta kafin tace.
"Kinje Office É—in commissioner da nufin taya shi murna sai akayi rashin sa'a kika tarar da Muttaka wato tsohon commissioner na jihar Bauchi a matsayin Commissioner a garin Gombe, hakan ne ya haddasa miki damuwa kike tunanin taya zaki shawo kan matsalolin dake damunki. Shin zance na haka yake ko akwai gyara.?"
Bata koyi mamakin jin batun Jiddah ba saboda sabo da tayi da hakan, shikuwa Saleem ganin Zarah ta gyaÉ—a kai alamun hakane yasa shi mamakin a ina Jiddah ta samu wannan labarin suna tare amma shi bai sani ba.

"Jeki É—auraye fuskarki kizo muyi magana." Ta kuma faÉ—a.
Wannan karon Zarah abin na Jiddah ya bata dariya domin dai ta fahimci Jiddah ta gane fitsari ya cika mata mara ne shiyasa tace taje ta ɗauraye fuska gudun kada Saleem ya fahimci zance. Babu musu ta miƙe ta shige banɗakin dake manne a office ɗin.

Saleem kuwa maida kallonshi yayi ga Jiddah cikin zaƙuwa yace.
"Sa-Jid a ina kika samu labarin abinda ya faru bayan muna tare banga wani ya kiraki ya faÉ—a miki ba."
Shiru tayi na wani lokaci kafin tace

"Nima bansan ya akeyi nake gane abinda ke ran Zarah ba, wani lokacin sai naji kamar anayi min raɗa a kunne na tuhumeta kuma na bata shawara. Abinda yake ƙara ɗauremin kai kuma shine idan mukayi amfani da shawarar sai muga ribar abin. Nima na rasa gane me hakan ke nufi."
Jinjina kai Saleem yayi cike da gamsuwa, yana ƙara tabbatar da cewa ƙaunar dake tsakanin Jiddah da Zarah daga Allah ne, babu yadda za'ayi ɗayansu ta ɓoye damuwarta batare da ƴar uwar ta fahimci haka ba.

A wannan yanayin Zarah ta fito ta samesu, zama tayi suka cigaba da tattauna abinda da ya shafi binciken da Saleem yake gabatarwa akan mutuwar É—an Jaridar.

"Ni fa inaga lokaci yayi daya kamata mu tunkari inda azzalumin nan yake tunda yaranshi biyu na hannu, mu tursasa sai sun faÉ—a mana inda yake." Inji Saleem

"A'a dear lokaci baiyi ba amma saura ƙiris domin muna gab da sanin inda yake." Cewar Jiddah.

"Hakane Barrister akwai sauran lokaci, baya ga haka har yanzu Raliya taƙi mana bayani akan komai daya shafe shi duk kuwa da irin azabar da ake gana mata."- Zarah

"Shikenan amma ya kamata muje ki ƙara yiwa mutumin nan barazana domin shima bashi da alamar yin bayani."

"Inada niyyar hakan dama tunda kunzo sai muje gaba É—aya daganan na sake yiwa Raliya tambayoyi".

"Ok muje É—in"
Daga haka suka miƙe tare da barin offishin.

Babu wani da zaiyi tunanin mutane na rayuwa a inda su Zarah suka je, domin wani tsohon kwango ne da ya ji jiki ginin gaba ɗaya ya fara rugujewa. A haka suka shiga tare da kutsa kai a wani babban ɗaki, Saleem ne ya isa daidai inda wasu shukoki suke ya kauda ƙasar dake gurin gefe sai ga wani murfi kamar na rijiya ya bayyana a gurin. Key Zarah ta miƙo mishi ya saka ya buɗe babban kwaɗon dake wajen tare ɗage murfin sai ga matattakala ta bayyana. Juyowa yayi ya kallesu yace
"Muje ko."
Kamar ko yaushe sune ke fara shiga sai ya biyo bayansu, yauma hakan ce ta faru saida suka shige kafin shima ya bisu bayan ya dudduba baiga kowa ba.
Tana ɗaure a jikin kujera sai wata mata dake gefe a zaune tana daddana waya, ganin shigowarsu Zarah ne yasata miƙewa tana musu barka da zuwa tare da gaishesu, amsawa sukayi cike da fara'a kafin Zarah tace
"Babu wata matsala ko Jummai.?"

"Babu ranki ya daɗe, sai dai jiya tayi ƙoƙarin guduwa bayan na kwance ta zatayi amfani da toilet, amma ta rasa hanya ina kitchen naji ta shine nazo na ɗaure ta."

"A tunaninta zata iya guduwa daga nan.?" -Jiddah

"Haka take gani." wacce aka kira da Jummai ta bada amsa.

Gabanta Zarah ta isa ta É—ago fuskarta da ta nuna alamun galabaita tace.
"Kinga wannan Raliya acid ne a yau idan baki mana bayanin inda Alpha yake ba zamu kona fuskarki ta yadda ko kin kuɓuta babu yadda za'ayi ya aure ki kamar yadda kike da buri."

A razane Raliya ta ɗago ta kalli Zarah tana mamakin yanda akayi tasan wannan zancen domin bayan ƙawayenta dake gidan da Alpha yake ajiyesu babu wanda yasan wannan zance, yanzu ta sadaƙar cewa ko bata gaya musu ba zasuyi amfani da asiri su karanci abinda ke ranta. Hawaye ne ya wanke mata fuska cike da takaicin yau zata faɗi wani sirri na masoyinta tace.
"Zan faÉ—a miki."

"Muna jinki." Saleem ya faÉ—a.

🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂

Malam Surajo Mai Idon Naira shine sunan da mutane kw kiranshi saboda tsantsar son kuɗi da yake da shi daga shi har Matar sa mai suna Lauratu. Malam Surajo da Lauratu ma'auratane da aka sansu da masifar son kuɗi da roƙo tare da bibiyar masu kuɗi suna musu fadanci, ƴaƴansu biyu kacal a duniya. Hajara itace ta farko wacce a yanzu take da shekaru 22 sai ƙanwarta Na'ima dake shekaru na 17. Duk wani buri sun ɗaurashi akan ƴaƴansu domin suna mishi kallon kadara wacce zasu dinga zamun kuɗi dasu.
Saidai a cikinsu Hajara ce kaɗai tayi gadon iyayen nata domin tana da buri sosai, a cewarta ma bazata yi aure ba idan ba mai hannu da shuni ta samu ba, saidai a ɓangaren Na'ima abin ba domin yarinya ce mai nutsuwa da sanin ya kamata sam bata yi halin iyayen nata ba shiyasa basa shiri sam dasu.

A daren ranar lahadi ne wanj abin farin ciki ya samesu a cewarsu, domin wani baƙo ne ya zo musu da wata kwangila mai tsoka. So yake su yi sanadin da ƴarsu Hajara zata auri ɗan shahararren mai kuɗin nan wato Eng. Muhammad Jawwad Sulaiman, batare da tunanin komai ba suka amince saboda zunzurutun kuɗin da za'a basu bayan haka kuma zasu samu kuɗi sosai idan ƴarsu tayi nasarar auren shi. Ya tsara musu komai da yadda Hajara zata haɗu da M.J tare da kalan aikin da yake so tayi mishi idan taje gidanshi, a haka suka rabu bayan ya ajiye musu makuɗan kuɗi domin yin hidima tare da faɗa musu cewa ta kasance cikin shiri domin a kowani lokaci zai iya kiranta domin su haɗu da M.J ɗin.
Wannan abu ya matuƙar faranta musu rai, domin a ganinsu fa kakarsu ta yanke saƙa.

Washegari kuwa kamar yadda yace, ya kirasu tare da yin magana da Hajara bayan ya gama gaya mata abinda zatayi idan ta fita.

A ɓangaren M.J kuwa bayan ya sha magani ya ɗan samu sauƙin abinda ke damunshi, shiryawa yayi ya fita zuwa gurin aiki domin bazai iya zama a gidan ba. Yana tafe zuciyarsa cike da tunani kala-kala, bai ankara ba hannu motar ta kwace mishi cikin rashin sa'a kuwa ya bige budurwar dake ƙoƙarin tsalleke titin tana sanye ta dogon hijabi har ƙasa milk colour, da hanzari ya taka birki ya kashe motar cikin tashi hankali ya fito ya sameta a zaune tana ƙoƙarin miƙewa alamun motar bata taɓata sosai ba.

"Sannu kinji baiwar Allah, kiyi haƙuri, daure ki mike na kaiki asibiti a duba ki."

Cikin sanyin murya tace

"A'a banji ciwo ba ka barshi kawai." tana mikewa da kyar tamkar saniyar dake naƙuda.

"Kar muyi haka dake dan Allah muje na kaiki ko da Pharmacy ne a duba ki."

Babu musu ta bishi tana takawa dakyar har ta ƙarasa inda yake tsaye ya buɗe mata ƙofar motar yana jera mata sannu babu adadi. Bayan shigarta ne shima ya shiga motar ya tada ta suka bar gurin zuwa asibiti.....✍️

_Kai na na mini ciwo_.🥺

*BY*
*JASMINE*🌸🌸

*ASP ZARAH*👩‍✈️

*BOOK 2*

*Page 3*

Da kwatance take nuna masa hanya ya Isa har ƙofar gidansu bayan ya kaita Pharmacy an duba lafiyarta duk da ba wani rauni sosai ta ji ba, ita ta fara shiga cikin gidan jim kaɗan kuma Na'ima ta fito ta gaidashi tare da faɗin ance ya shiga daga ciki, babu musu kuwa ya bita har cikin gidan inda aka shimfiɗa masa tabarma a tsakar gurin Inda su Malam ke zaune tare tare da Hajara.
Bayan gaishe gaishe ne M.J ya kuma basu hakuri akan abinda ya faru, nan suka nuna babu wata matsala, miƙewa sukayi duka inda aka barshi da Hajara bayan ta kawo mishi sihirtaccen zoɓon da Ummansu ta haɗa mishi, duk da yake mutum ne mai ƙyanƙyami amma haka bai hanashi shan zoɓon ba ganin kamar yanayin mutanen baiyi kama da ƙazamai ba.
Sun daɗe suna hira kamar da ma can sun saba duk da shi ba mutum bane mai yawan magana amma ya sake sosai yana hira da ita, ya jima kafin ya musu sallama ya tafi bayan yayi musu ɓarin naira tare da alƙawarin zai dawo ya duba jikin Hajara, haka sukayi sallama zuciyar wannan ahali cike taf da farin cikin samun wannan arziki da sukayi.
Chapter 2 · 0% Book details