Sashe 10
Asp Zarah Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Sai dai kafin ta kai ga miƙewa Sadiq ya ruƙo hannunta ya zaunar da ita ba ta re da ya ce komai ba abincinsa kawai ya cigaba da ci, tuni ta gane abinda ya ke nufi don haka ta zauna cikin takura ta fara cin abincin, duk da bata kallonshi amma ta tabbatar kallonta ya ke yi don haka ta ji sam zaman gurin bai yi mata ba.
Sun rigata gamawa don haka ne ma suka koma cikin falo suna hira. Duk da haka idon mayen nata na kanta.
_Safwan Muhammad Habib shine sunansa matashin saurayi ɗan kimanin shekaru ashirin da bakwai ɗan kwalisa, asalinsa ɗan Nigeria ne karatu ne ya kawo shi waje daga haka kuma suka riƙeshi, babban likitane a ɓangaren da ya shafi mata da ƙananan yara._
_Ya fito ne daga gidan sarauta inda a yanzu haka mahaifinsa shin Sarkin Adamawa, cikin ƴaƴan Mai martaba shida da matarsa Hajiya Zulaihat guda biyu ne maza, ɗansu na fari Mahmud sai auta Safwan shiyasa Mai martaba ya ɗauki gatan duniya ya ɗora shi akansu ba kamar Safwan ba ma da ba ya iya ɓoye son da ya ke masa ko a gaban waye, tun da ya isa shiga makaranta Mai Martaba ya ɗauke shi zuwa saudiyya inda wata ƙanwarsa ta ke aure, anan ya yi karatunsa daga na boko har zuwa addini hutu ne kawai ke maida shi Nigeria, sanda ya isa shiga jami'a ne ya koma London ya haɗa degree ɗinsa na farko daga nan ya koma Malasia yayi Masters ganin ƙoƙarinsa da sanin kan aiki ne yasa bayan ya gama karatun ƙasar ta riƙeshi zai yi mata aiki na tsawo shekaru biyu, ɗan uwansa Mahmud kuwa tunda ya gama karatu mai martaba ya sashi ya kuma Najeriya inda ya buɗe mishi wani babban company tun da dama karatunshi akan kasuwanci yayi, saboda kasancewarsa magaji shiyasa mai martaba bai yarda ya zauna a waje don yin aiki ba, a yanzu haka yana da shekaru 35 kuma har zuwa wannan lokacin bai yi aure ba duk takurar da iyayensa ke masa an haɗashi da ƴaƴan manya sosai sai dai duk cikinsu ya kasa zaɓar ko guda ɗaya._
_Farkon ganinta da Safwan washe garin ranar da suka zo Malasia ne, gidansu da nashi na fuskantar juna ƙaramin titi ne kawai ya rabasu, a ranar Sadiq ke gayamata cewa ya shaida Safwan ɗin don sun taba haɗuwa sau biyu a saudiyya sanda ya je Umrah, anan ne ma ta ke jin tarihinsa da inda ya fito shiyasa wani lokacin bata ganin laifinsa idan yana girman kai bata ganin laifinsa don ya fito ne daga gidan sarauta_
Ta na iya jiyo hirar da suke yi daga inda ta ke, tana mamakin yadda ya ke hira haka harda dariya amma idan ka ganshi a wani wajen kamar mala'ikan mutuwa.
"Zuwa wani sati zanje Egypt." Cewar Sadiq
"Haba dai yaushe ka dawo daga Egypt din da har zaka koma, me Ammi ta ke baka hakane ko kuma akwai wacce ka ajiye acan ne shiyasa kake zuwa ganinta." Safwan ya faÉ—a cike da zolaya.
"A'a ka bari dai ai yanzu Yola zanje na zaɓo santaleliyar mata jinin Fulani, zanje na taho da Rahama ne kasan har yanzu ba wata isasshiyar lafiya gareta ba."
Hararar wasa ya aika masa sannan ya ce
"Kana shagwaɓa yaran nan dayawa fa, yanzu duk wayar da kuke yi da video calls bai ishe ku ba har sai ka aje aiki kaje ka ɗauko ta."
"No bawai haka bane wallahi, next week little zata ƙara shekara shiyasa nake so tazo mu yi murnar tare."
"La'ilah party zaka koya musu."
Dariya yayi mai isarsa sannan ya ce
"Ba wai party bane, Abbah ya rigada ya saba mana ne duk ranar zagayowar haihuwar wani daga cikin mu sai an haɗu an taya shi murna hatta ni da bana ƙasar ma, har inda nake ake zuwa a same ni ayi komai tare dani. Kuma kaga ita little bata taɓa ƙarin shekara cikin nutsuwa ba aikin nan nata baya barinta ta yi abubuwa cikin lumana ko bata gari anyi ta kiranta a waya kenan har sai ta gaji ta koma."
Dariya ce ta so kwacewa Zarah jin irin sharhin da É—an uwan nata ya yi, shidai Sadiq akwai surutu idan ba haka ba yanzu me ya haÉ—a Safwan da wannan dogon zance na family, ko da ya ke Sadiq É—in ba shi da wasu abokai sai turawa shi yasa idan ya haÉ—u da bahaushe ya ke zuba kamar ruwan sama.
GyaÉ—a kai Safwan ya yi cikin gamsuwa ya ce
"Hakane gaskiya bai kamata ace don Abban baya raye ba kuma a daina musu hakan zasuji kewa ta damesu. Allah ya jiƙansu Abbah ya gafartamusu."
"Ameen" Sadiq ya faÉ—a sannan ya kalli inda Zarah ke zaune, ganin hankalint baya kansu ne yasa shi cewa
"Ka faÉ—a a hankali karka tada min rigima dan idan little ta birkice ta fi tsohuwar mota."
Dariya suka yi duka harda tafawa.
Miƙewa ta yi bayan gama cin abincin ta fara tattara kwanukan tana kaiwa kitchen, harta gama ta shige ciki ta barsu suna hira batasan lokacin da Safwan din ya tafi ba don a Malasia dare baya yiwa mutane sai dai idan mutum ne ya gaji da zirga-zirga ya je ya kwanta.
Kwanaki uku tsakani Sadiq ya wuce Egypt, kwananshi É—aya acan suka dawo tare da Rahama. Ranar kusan kwana suka yi suna hira irin ta Æ´an uwa.
Washe gari da safe dukkansu ukun suka shiga kitchen dan haɗa breakfast, sosai Sadiq ke zaƙewa wajen baiwa ƙannen nashi kulawa.
Bayan sun gama breakfast ne kuma suka hau aikin gyaran cikin gida har zuwa farfajeyar gidan, gabaÉ—aya Zarah da Rahama sun yi kaca-kaca da ruwa sun jika ko ina wai suna baiwa fulawoyi ruwa har abun ya koma suna watsawa juna.
Yana daga ɗakinshi ya ke hangosu ta window, sosai ƙaunar da suke wa juna take matuƙar burgeshi musamman yadda yaga dukkansu suna baiwa alawar zuciyarsa kulawa, murmushi yayi mai sauti saboda wani abu da ya tuna. Safwan kenan.
Wuni suka yi ranar cikin nishaɗi da kulawa da juna, yadda suke nuna ƙaunar juna kowa ya gansu sai sun bashi sha'awa.
Kamar wacce aka yiwa baki tunda Zarah ta kwanta bacci bata tashi ba, kasancewar tana fashin sallah shiyasa Rahama bata tasheta ba lokacin sallar asuba.
Sai wajen ƙarfe goma na safiya ta farka, da wasu haɗaɗɗun greeting cards ta fara yin tozali, da hanzari ta miƙe saboda tunawa da ta yi yau ranar zagayowar haihuwarta, cards ɗin ta janyo guda uku ta fara karantawa cikin jindaɗi sai dai guda ɗaya ya matukar tafiya da ita kuma ga alama ya fi duka kyau da tsada, duba suna ta yi taga an rubuta SMH bata gane ko na wanene ba tunda na Sadiq da Rahama duk sun saka sunansu bata wani damu ba ta miƙe ta nufin zuwa toilet, idonta ya sauka akan dressing mirro wani kwali ta gani dan haka ta yi saurin isa ta buɗe shi, wata haɗaɗɗiyar arabian gown ne a ciki kalar pink mai matuƙar kyau dai wani takalmi golden.
Da hanzari ta shiga bayan gida ta watsa ruwa ta fito dan tasan Æ´an uwanta na jiranta.
Simple makeup ta yi a fuskarta sannan ta saka doguwar rigar wacce ta mata kyau matuƙa, veil ɗin rigar ta naɗa akanta sannan ta nufi falo.
Da alamun mamaki a fuskarta ganin falon gabadaya duhu mamaye shi, bata gama mamakin ba kuma haske ya gauraye falo ta re da suwar happy birthday to you, ido ta waro tana kallon mutanen falon cikin mamaki harda maƙotansu da matayensu, tuni ta ƙara rudewa ganin Jiddah da Saleem a gefe ɗaya, hawayen da ake kira na farin ciki ne ya sauko a fuskarta. Da sauri Rahama ta zo ta ja ta zuwa gaban tebur din da aka aje ƙaton cake kalar pink da fari, hannun ta kai da nufin yankawa Rahama ta yi saurin riƙe hannun, kallonta ta yi da alamun tambaya bata amsa mata ba sai ma zura hannayenta da tayi ta rufe mata idanu, kusan sakan goma sannan ta buɗe mata, sai da ta razana saboda abinda ta ga ni ta kuma ji, Safwan ne a durƙushe gabanta riƙe da ɗan ƙaramin akwati na zobe yana faɗin
"Will you marry me (Shin zaki iya aurena)"
Sam ta rasa a wata duniyar ta ke ciki, tana fata idan mafarkine ta yi gaggawar farkawa, kallon gefe da Jiddah ke tsaye ta yi, gira ta ɗaga mata tare da kashe ido ɗaya sannan ta rungumo Saleem a jikinta. Abin yaso baiwa Zarah dariya matuƙa yadda Jiddan ke yi kamar za'a kwace Saleem din.
Bata san ya akayi ta gyaÉ—a kai ba sai ji tayi kawai an zura mata zobe a hannu.
Tafi suka yi gabaÉ—aya sannan ne ta yanka cake É—in.
Ƙaramin shagali suka yi sannan kowa ya watse sai su Jiddah da zasu wuce Dubai da daddare ita da Saleem zasu je siyayyar haihuwa.
Cikin ƙanƙani lokaci soyayya mai ƙarfi ta ƙullu tsakanin Safwan da Zarah, har wani lokacin suna mamakin junansu ta yadda basa iya ɗaukan awanni ba ta re da sun ji muryar juna ba, idan suka zauna hira kuwa da ƙyar Sadiq ke lallaɓa Safwan ya tafi gida ya kwanta idan dare ya yi, da ya shiga gida kuma zai kirata su ɗaura daga inda suka tsaya.
Harta su Daddy sai da suka san da batun soyayyar nan domin Safwan dai ya yi wa Abbansa maganar Zarah inda shi kuma ya aika Waziri da wasu wakilansa har garin Gombe su ka tambayowa Safwan auren Zarah tare da bada kuÉ—in nagani inaso da goron tambaya kamar yadda ya ke a al'ada ya tanadar.
Yau ma kamar kowani lokaci a ƙarshen mako sukan wuni tare ne harta ayyukan gidan tare suke yi, su na yi wani lokacin Sadiq na tsokanar Safwan mijin Hajiya, don shi Sadiq ba shi da wani girman kai irin na Yayu akan ƙannansu musamman idan su na soyayya da abokansu, ya na zama su yi hira sosai wani lokacin idan su ka yi faɗan masoya ma shi ya ke sasanta tsakaninsu idan bayanan kuma sai a kira Rahama ta video ta shirya tsakaninsu.