← Book details Asp Zarah Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 13 OF 18

Sashe 13

Asp Zarah Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Ai ɗan uwar matarka ne shine ma mij.." bata ƙarasa ba saboda tarin daya kuma sarƙafe M.J wannan karon har yana faɗowa daga kan kujerar da yake, da hanzari ta nufi kitchen ta ɗauko ruwa daidai lokacin kuma Momi ta fito, dama suna zaune ne da Baaba su hira da su Zarah kiranta da akayi a waya ne ya sata miƙewa ta shige ciki.
Da sauri ta ƙarasa inda Abdallah ke riƙe dashi tana tambayar meya faru, bai kula da yanayin ciwo da yake ciki ba da kuma suya da ƙirjinsa ke masa tamkar a tsaga a saka mishi ƙanƙara, saukowa yayi ya riƙe ƙafar Momi lokaci guda kuma ya fashe da kuka mai taɓa zuciyar duk wani me sauraronshi, sosai yake kukan yana faɗin ta yafe mishi.
Tsakanin uwa da ɗa aka ce sai Allah, tuni tausayin ɗan nata ya kamata taji kamar hawaye zasu zubo mata amma ta kauda kai sannan ta kwace ƙafarta tayi tsaki ta ce

"Sakeni dan Allah, sai yanzu kasan da cewa kamin kuskure har kake nema na yafe ma ka toh bazan yaf..."

Salatin da Baaba tayi ne yasa ta kasa ƙarasa wa sakamakon M.J da ta gani kwance a ƙasa riris ba alamun motsi a tattare da shi, salati ta doka sannan ta tsugunna tana jijjigashi cikin tashin hankali.
Baaba ce ta kalli Abdallah da tsantsar tausayin abokin nashi ya sashi zubda hawaye ta ce

"Audullahi É—auke shi mu tafi asibiti."

"Babu inda za'a kai shi yana nan a gida." Daddy da tun ɗazu yake tsaye a ƙofar shigowa yana kallonsu ne yayi wannan maganar. Ƙarasowa yayi cikin ya isa har gaban Baaba ya ce

"Ke mahaifiyace a gareni ban taba neman alfarma a gareki kin hana ba dan Allah karki dakatar dani daga abinda nayi niyya."

Faɗan da yafi ƙarfin ka aka ce maida shi wasa, don haka Baaba bata kuma tankawa ba ta nufi hanyar ɗakinta duk da tana tausayin M.J amma can ƙasar zuciyarta tana murnar sakayyar da ya fara gani, shima Daddy hanyar ɗakinsa yana faɗin
"Ban yarda ki zauna a inda Jawwad yake ba." daga haka ya shige, itama Momi miƙewa tayi tabi bayanshi fuskarta na zubar da hawaye.

Matuƙar tausayin M.J ne ya cika zuciyar Abdallah, jiki ba kwari ya miƙe ya ɗauki ruwan da Baaba ta ajiye a center table ya watsa mai a fuska, cikin sa'a ya ja wata doguwar ajiyar zuciya irin na wanda ya farfado daga suma. Miƙewa yayi zaune yana ƙara fashewa da wani sabon kukan duk da rarrashin da Abdallah ke mai amma bai dakata ba, dan haka ya barshi ya cigaba da kukan har yayi mai isarsa, a lokaci anfara kiraye kirayen sallar magriba dan haka suka mike don zuwa masallaci.
Sai da suka yi sallar isha'i sannan suka kuma nufowa gidan.
Sai da aka kai ruwa rana kafin Daddy ya sauraresu, nan Abdallah ke basu labarin abinda Hajara ta aikata, Momi kam taso a kama Hajara a kulle amma Daddy ya ce yanzu abu ya wuce ba za'a tada shi ba. Daƙyar da siɗin goshi suka yafewa M.J laifukan da ya musu sannan Daddy ya jadda mishi cewa lallai ya samu Zarah ya nemi gafararta idan ba haka ba kowa rayuwarshi tana cikin haɗari.
Abu da mai neman kuka jin Daddy ya ambaci sunan wacce yake muradin gani yasa yayi ta taɓa Abdallah kan ya tambayi Daddy inda Zarah take, gyaran murya Abdallah yayi sannan yace

"Emm Daddy ko za'a gaya mana inda ita Zarah take sai muje har can mu bata haƙuri. Bayan haka kuma muna so a sasanta inda rabo ta koma gidanshi."

"A sasanci me Abdallah?" Momi ta faɗa a firgice harda dafa ƙirji kamar wacce taga mugun abu.

Kai M.J ya sunkuyar shi kuma Abdallah ya fara sosar kai.
Murmushi Daddy yayi sannan ya ce

"Ai Zarah ba bare bace duk inda take ma ai zata dawo gida idan tazo sai ya nemi afuwarta, sannan maganar sasantawa banaso na ƙaraji dan babu aurenshi akan Zarah maganar da akeyi yanzu ma ƙarshen satin nan za'a kawo sadakinta daga masarautar Yola dan ɗan sarki ke nemanta na daɗe da bashi umarnin hira saboda sun kawo kuɗin nagani inaso. A taƙaice dai a janye wannan maganar banson kuma jinta kunsan babu kyau neman aure akan aure".

Daga haka Daddy ya sallamesu, M.J ji yayi gabaÉ—aya duniyar ta mishi zafi, Allah ba azzalumin bawanshi bane, a yanzu yana ji a ranshi lallai idan ya rasa Zarah ba zai iya cigaba da rayuwa ba.

A haka ya tattaro kayansa gabaɗaya ya dawo gidansu ya tare a tsohon sashinsa. Yawan rashin lafiya da yake fama da ita musamman ciwon ƙirji da matsanancin ciwon kai ne yasa ya yanke shawarar zuwa asibiti don duba lafiyarshi.
Gwajin farko likita ya tabbatar mai ya kamu da ciwon zuciya kuma ya kai matakin ƙarshe komai na iya faruwa da shi idan har bai kula ba, a haka likitan yayi mai gwaje-gwaje sannan ya bashi magunguna tare da shawarwari akan matakin da zai ɗauka na rashin sanya damuwa a rai. Da haka ya dawo gida.

Tsawon lokaci yana fama da jinya babu wanda ya sani sai Abdallah shima kuma ya hana ya faÉ—ama kowa, haka yake fama da matsanancin ciwo, baya yin sati É—aya cikakke batare da ciwon ya tashi ba saboda damuwa da ya sakama kanshi akan Zarah musamman yanzu da ya tabbatar tana gab da kubce masa. Yana galabaita sosai idan ciwon nashi ya motsa don aman jini yake yi sosai amma duk da haka bai sanar da kowa ba.

Watarana irin haka da ciwon nashi ya tashi lokacin yana gida a sashinsa, nan yayi ta aman jini har ya suma, a haka Abdallah yazo gidan ya same shi aikuwa bai ɓata lokaci ba ya sanarwa su Daddy nan aka ɗaukeshi zuwa asibiti hankali a tashe. Sosai Daddy ya ma Abdallah faɗa jin abinda likita ya faɗamai na cewa ya daɗe da cutar a jiki kuma suna zuwa karɓar magani.

Ko da ya nemi jin ba'asin ciwon daga gurin Abdallah kai tsaye ya shaida mishi cewa akan Zarah ne, duk da likita yace a nemowa M.J abinda yake so amma sam Daddy yace baisan wannan zance ba indai akan Zarah yake wannan ciwon sai dai ya ce Allah ya jiƙansa da Rahama dan kuwa ba samunta zai yi.
Nan likita ya bada shawarar sai anfita dashi ƙasar waje anyi mai aiki don kuwa a yanzu zuciyarsa na gab da bugawa, abu na kuɗi nan Daddy ya fara shirye-shiryen fitar da M.J zuwa ƙasar India don ayi masa aikin zuciya.
Hankalin Momi da Baaba ya tashi sosai jin abinda ya samu Jawwad din nan Daddy yayi ta tausarsu daƙyar ya samu suka ɗan kwantar da hankali.

*****************************

Duk yadda Zarah taso dawowa Nigeria hutu abun ya faskara saboda jarrabawar ƙarshe da zatayi don haka dole ta zauna ta fuskanci karatunta dan fitowa da sakamako mai kyau, watanni uku kaɗai suka rage mata ta gama wannan course ɗin mai mahimmanci dan haka tana buƙatar ta ƙara ƙaimi. A gefe guda kuma soyayyarsu da Safwan na ƙara ƙarfi sosai ta yadda har mutane na mamakin irin son da suke yiwa juna dan basa iya ɓoyewa ko a gaban wa suke.
Maganar aurensu tayi nisa dan har ankai sadaki kamar yadda Daddy ya faÉ—a sannan a tsaida ranar aurensu watanni huÉ—u masu zuwa, kenan wata É—aya bayan Zarah ta kammala karatun da take yi a yanzu.

Ammi kuwa tunda aka saka ranar auren ta ɗauko mai gyara guda tun daga Maidugurin Nigeria ta kaita har ƙasar Malasia don gyara mata ɗiyar ta ta. Ai kuwa kwalliya ta biya kuɗin sabulu dan a cikin satin kafin Ammi ta wuce Egypt ita kanta ta yaba da irin canji da ta fara gani tattare da Zarah don haka gargaɗi matar akan kada ta bari Zarah da Safwan su dinga yawan haɗuwa gudun aikin shaiɗan. Da haka ta musu sallama ta wuce Egypt.
Gyara sosai Matar mai suna Hajiya Jamila keyiwa Zarah lokaci ƙanƙani ta koma tamkar wata baturiya ko balarabiya saboda tsananin kyau da sheƙi da take fitarwa.

Duk wani shiri na fitar da M.J ƙasar waje an gama shi, inda abokinshi na kwarai Abdallah yace dashi za'ayi tafiyar dan ya dinga kula da shi. Sati na zagayowa suka ɗaga zuwa ƙasar India, sai dai kafin tafiyarsu Daddy ya kira Sadiq ya shaida mishi halin da ake ciki, sosai Sadiq ya tausaya mishi sannan yayi mai fatan samun sauƙi sai dai bai faɗawa Zarah ba, ko meye dalili oho.
Dake sun riga sun gama komai ta internet yasa har airport motar asibitin ta zo ta ɗaukesu, babu ɓata lokaci kuma aka fara baiwa M.J kulawar likitoci, irin asibitocin nan ne da ba'a buƙatar masu jinya dan haka su Daddy na gama duk cukucukun asibitin suka nemi masauki dan hutawa.
Kullum sai dai su shirya su je da safe su dubashi su dawo sannan da yamma su ƙara komawa.
Satinsu ɗaya a ƙasar jikin M.J ya fara samowa dan har yana iya bude idon sannan yana motsi da jikinsa ba kamar a Nigeria ba da tunda ya suma bai ƙara motsawa ba saboda rashin isassun kayan aiki a ƙasarmu.
Kwanansu goma aka yiwa M.J tiyatar kuma cikin sa'a akayi lafiya ba tare da ansamu wata matsala ba sai dai fatan a kiyaye gaba. Sai da ya kwana tara cur! Kafin aka basu damar sake ganinsa kuma Alhamdu Lillahi yaji sauƙi sosai sai dai rama da ya yi. A ranar har video call sukayi da su Momi wanda tunda suka bar ƙasar kullum sai sun kira fiye da goma, har Ammi ma takan kira wajen sau biyar a kowacce rana don jin yanayin jikin Jawwad ɗin.
Wata É—aya Daddy yayi a India ya tattaro ya dawo gida ya bar Abdallah don kulawa da M.J saboda shirye-shiryen bikin Zarah da za'ayi nan da watanni biyu da satikai ( Su Daddy manya kana namiji mai ya haÉ—aka da wani shirye-shiryen aure, kodayake Æ´ar so za'a aurar).
Kafin tahowarshi sai da ya zaunar da Jawwad ya mishi faɗa sosai tare da nasihohi sannan yace ya cigaba da neman zaɓin alkhairi a gurin Allah ya rabu da batun Zarah tunda dai ita Allah ya ƙaddara ba zasu sake zama da juna ba.
Chapter 13 · 0% Book details