Sashe 11
Asp Zarah Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Yana zaune saman durowar kitchen ita kuma tana gaban fanfo tana wanke-wanke, hirarsu su ke yi cikin nishaÉ—i kamar waÉ—anda suka É—auki tsawon shekaru su na soyayya. Tufa É—in da ke hannunshi ya gutsira sannan ya ce
"Mrs. Safwan kinsan me ya sa ban takura anyi auren nan da wuri ba.?"
Ba ta re da ta juyo ba ta ce
"Sai ka fada"
"Saboda inaso ki gama ƙarasa wannan karatun don idan na aure ki nasan ba zaki nutsu ki yi karatun nan ba saboda yadda zan ruɗa ki da salon soyayyata sai kin daina fahimatar kowani zance idan ba nawa bane."
Dariya ta yi sannan ta juyo ta naɗe hannayenta a ƙirji tana kallon shi ta ce
"Saboda ina da ƙaramar kwakwalwa koh.?"
"A'a saboda soyayyar da zan nuna miki ta musamman ce kina buƙatar cikakkiyar nutsuwa don fahimtarta."
"Toh Allah ya kaimu lokacin yasa kada ka canza abinda ka fada."
"Bazan canja ba saboda ina miki ƙaunar da bana yiwa kowa irinta a duniyar nan."
"Uhmm" ta ce cikin murmushi sannan ta juya ta cigaba da wanke-wanke suna hira har ta gama ta gyara gurin.
Sai a lokacin ya sauko daga inda ya ke zaune ganin ta fara hada-hadar ɗaura abincin rana, kamar ko da yaushe idan yana nan yakan taya ta da ƙananun aiyuka kamar su yanka albasa, fera dankali, bare maggi da sauransu a haka har su gama girkin.
A haka Sadiq ya zo ya tarar da su a kitchen É—in ya kalli Safwan ya ce
"Mijin Hajiya zo ka min wani aiki a falo."
"Haba babban Yaya baka ga ina taya ta aiki bane." cewar Safwan.
"Little ba shi umarni kinji abu zai min mai mahimmanci."
Dariya Zarah ta yi ta ce
"Ba ni na riƙe shi ba fa, jeka ta ya shi aikin mana"
Hannunshi Sadiq É—in ya kama su ka fice ta re suna dariya.
Haka kullum suke kasancewa cikin farin ciki yayinda soyayyarsu ke da ɗa ƙaruwa.
Kwanci tashi asarar mai rai a haka kwanaki ke shuÉ—ewa har suka zama watanni.
NIGERIA
A watannin da suka biyo baya duk wanda ya kalli M.J zai gane hankalinshi ba'a kwance ya ke ba gabaɗaya ya rame ya yi baƙi, abubuwan da Hajara ta ke masa ya ƙaro musamman yanzu da take ɗauke da juna biyu babu kalar fitsarar da bata yi mishi idan ya nemi ya tanka sai ta yi iƙirarin zata zubda ciki, gashi Allah ya ɗora mishi son cikin sosai musamman da su Daddy su ka sassauta mishi tunda suka ji labarin Hajaran na ɗauke da juna biyu, a gefe guda kuma tunanin Zarah da ke addabar zuciyarsa duk yadda ya so dainawa amma ya kasa nan ya fahimci cewa sonta ne ya mishi mugun kamu sai dai yana ƙoƙarin ɓoye hakan don har a wannan lokacin bai daina zargin cewa tana bin maza ba musamman idan yayi la'akari da yadda ya ganta a hotel ta re da wanda ba muharraminta ba.
Yana zaune a office ɗinshi cikin tunanin da ya saba ya ji ana kwankwasa kofar shigowa, umarni ya bada aka shigo sakatariyarsa ce riƙe da takarda a hannunta ta ce
"Yallaɓai wannan saƙo ne aka kawo ance a baka."
"Daga wanene saƙon?"
"Bai fada ba yallaɓai ya ce dai a baka ne yana sauri zaku yi waya."
Kan tebur ɗin ya nuna mata ta ajiye daga haka ta fice, hannun ya zura ya janyo takardar ya buɗe, wata irin zabura ya yi tare da miƙewa tsaye daga zaunen da ya ke.
Zufa ce ta karyo masa lokaci guda wasu hawaye masu ɗumi suka sauko daga idonshi, sambatu ya fara yana kiran sunan Hajara. A haka Abdallah ya turo ƙofar ofishin ya shigo ya same shi cikin wannan yanayi, a kiɗime ya ke tambayarsa abinda ya faru. Bai iya magana ba illa takardar da ya miƙa mishi cikin zubda hawaye.
"Innalillahi wa inna ilahi raji'un." shi ne abinda Abdallah ke maimaitawa bayan ya karanta abinda ke cikin takardar...âœðŸ»
*BY*
*JASMINE🌸🌸*
*ASP ZARAH*👩â€âœˆï¸
*BOOK 2*
*Page 10*
Fuska ba walwala ya É—aga ido yana kallon M.J dake dube-dube a kan tebur ya ce
"Me kake nema ne haka.?"
"Abdallah gidan zanje naji ba'asi wallahi yau kome za'ayi sai na ci mutuncin Hajara a garin nan."
Duk da suna cikin wani hali amma hakan bai hana Abdallah dariya ba ganin yadda gabaÉ—aya M.J ya birkice yana neman key É—in mota bayan ga key din nan a gefen tebur amma tashin hankali bai barshi ya gani ba, kai ya kaÉ—a sannan ya ce
"Muje na sauke ka a yadda kake din nan bai kamata kayi tuƙi ba."
"Muje muje Abdallah."
Fita suka yi M.J a gaba tamkar zai tashi sama, a haka suka shiga motar Abdallah ya tada suka É—auki hanyar zuwa gidan M.J din, Abdallah ne ya kalleshi ya ce
"M.J ya akayi haka ta faru har yake ƙoƙarin maka ka a kotu.?"
"Bansani ba Abdallah, innalillahi wa inna ilaihi raji'un, a gidana ace har matata na É—auke da cikin wani amma bansani ba. Wallahi sai yanzu na tuna sam bai kamata ace cikina bane don yanzu ne cikin ya shiga wata uku kuma rabona da ita na jima sai lokacin da aka ce tana da cikin nan sam zumuÉ—i bai barni nayi lissafi ba." M.J ya fada idonshi na zubar da kwalla.
"Ishara ce Allah ya nuna maka Jawwad shiyasa ake so mutum ya dinga kyautata zato akan É—an uwansa."
"Me kake nufi ne.?"
"Abubuwan da kake zargin Zarah da su ne Allah ya tabbatar maka akan matarka."
"Ba zarginta nake ba tabbatarwa nayi."
Murmushi Abdallah ya yi wanda iyakarsa baki sannan ya ce
"Rana na tafe, sai dai kamar yadda nayi alƙawari duk randa ka gane gaskiya kada ka neme ni don taimaka maka. Yanzu ya za'ayi da batun Hajara.?"
"Abdallah zanje na tuhumeta sai ta faɗa gaskiya matuƙar da aurena ta ke bin wasu mazan wallahi sai na rabu da ita bayan na wulaƙanta ta, har ni za'a turowa takardar sammaci zuwa kotu akan bana kula da cikin da wani ƙato yayi har ana ikirarin idan wani abu ya same shi sai anyi shari'a da ni."
"Uhmm" kawai Abdallah ya ce daidai lokacin da yayi horn a gaban gidan M.J mai gadi ya buÉ—e masa ya shiga da motar, ko parking bai gama tsaidawa ba M.J ya fita a sukwane yana faÉ—in
"Jirani ina zuwa."
Rai ɓace ya shiga falon ganin bata nan ne yasa ya nufi hanyar ɗakinta, a fusace ya banka ƙofar ɗakin.
"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un" ya shiga maimaitawa, tashin hankali da ba'a saka masa rana, Hajara ce da wata babbar mata a kwance kan gado haihuwar uwarsu suna aikata masha'a. Sulalewa yayi a ƙasa ya rasa ma abinda zaiyi, sai lokacin suka farga dashi da hanzari suka miƙe matar ta rarumi kayanta zata gudu aikowa ya miƙe ya rufe ƙofar ɗakin sannan ya koma ya zauna, sun ɗau mintuna a haka lokacin duk sun maida suturunsu miƙewa yayi ya kwance belt ɗin da ke jikinshi ya shiga dukansu ba ji ba gani tun suna ihu da neman taimako har muryarsu ta daina fita, sai da ya tabbatar sun galabaita sannan ya tsagaita cikin fushi ya ce
''Kinci amanata Hajara wallahi yau bazan barki ba sai kin gayamin abinda na miki har kika nemi ƙuntata min haka, dama badan Allah kika aureni ba. Bayan zina har ƴan uwanki mata kike bi, ke kuma ki tashi ki ficemin daga gida tun kafin na halaka ki."
Da mugun sauri ta miƙe ta bude ƙofar ta fita, karo suka yi da Abdallah wanda tun sanda suka fara ihu ya jiyo su shine ya shigo dan ganin abinda ke faruwa, sai yanzu da M.J ya yi magana ya fahimci dalilin dukan na su. Kaɗa kai ya yi cike da takaici ya shiga ɗakin don fito da M.J kar ya yiwa Hajara wani illah.
Da ke Hajara matsoraciya ce gashi kuma ta ji jiki a hannun M.J tuni ta fara sakin zancen da batasan tana furtawa ba, tiryan-tiryan ta labarta mishi dalilin da ya sa ta aureshi har zuwa ranar da aka zo har gida aka duki Zarah, ashe da ita aka haɗa baki ta buɗe musu ƙofar falon dan ta kasance automatic ne ba da key ake buɗewa ba. Cikin kuka ta cigaba da cewa
"Ni bansan me ta yi musu ba, kawai sun same mu ne suka faɗa mana cewa ta yaudari wani da ke musu aiki har tayi sanadin da aka kamashi a garin bauchi shiyasa suke son ɗaukar fansa. Sai daga baya na fahimce cewa Diamond suke son karɓa a wajenta shiyaaa aka haɗa baki da ni don idan ta bayar nima a bani wani kaso a ciki."
Rigiji gabji! A yau Jawwad ji yayi ya fi buƙatar mutuwarsa saboda yadda yake jin zuciyarsa na suya tana barazanar fitowa a ƙirjinsa, tabbas bai cacanci yayi farin ciki ba a rayuwarsa a yadda ya ɗau tsawon lokaci yana ƙuntatawa marainiya.
Sai yanzu abubuwa suka fara dawo mishi dalla-dalla, a lokacin daya dawo daga ƙasar waje gabaɗaya sanda zai fara aiki a _M.J JEWELS_. ya tambayi Daddy diamond ɗin da ya siya a hannun turawa sai dai bai bashi cikakkiyar amsa ba sai cewa da yayi
"Son waɗannan Diamonds ɗin suna hannun wacce duk rintsi duk wuya nasan bazata taɓa bari su salwanta ba saboda tsananin ƙaunata da take yi da kuma riƙon amana da gaskiya da ta ginu akai."
A lokacin da Daddy ya faÉ—a mai haka yayi tunanin Momi aka baiwa ajiya ashe Zarah ce, sam a lokacin bai kawo ta cikin tunaninsa ba sai yanzu da Hajara ke mai bayanin nan. Wani abu da ya kuma zuwa tunaninsa shine batun Hajara da ta ce Zarah ta yaudari wani an kamashi a hotel a jihar Bauchi, kardai abinda ya fara tunani ya zama gaskiya.
Cikin zare ido ya kalle Hajara dake É—ar-É—ar ya ce
"Kince ta kama wani a Bauchi wane ne wannan."
"Bansan shi ba nidai kawai sunce min wai ta yaudareshi akan zata bishi hotel su kwana tare ashe shi baisan cewa Æ´ar sanda bace bayan sunje ne ta ga hodar iblis dama suna zarginshi shine ta kira jami'an da suke tare aka tafi dashi."