Sashe 7
Ƙanwar Maza Complete Hausa Novel · about 8 min read
Murguɗa baki tayi tana fari da ido ta ce "Tubarkallah zuƙul-zuƙul maye ya ci kansa da kansa, wallahi ni bana kama da Akushi, son kowa ƙin wanda ya rasa"
"Ke dalla ware, meye son kowa ƙin wanda ya rasa, aba Kamar gurguwar akuya" Yasir yayi maganar yana dariya.
Haushi ne ya kamata ta buÉ—e baki za tayi rashin mutunci, ta sanya idonta a cikin na Umar, ta haÉ—a maganar da zata yi, da lomar abincin ta haÉ—iye.
Suka gama cin abincin, Yasir ya kwashe kwanuka, ya fara ƙoƙarin wankewa, Huzaifa ya shigo da tsintsiya zai share ɗakin, Umar ya ce ya ajiye tsintsiyar ya bawa Rumaisa ta share.
Haushi ne Yakamata ta lura tun da aka kawo ƙararta ya tsaneta, dama can ba wani shiga shirginta yake yi ba.
Bayan ta kammala sharar ta nemi wuri za ta kwanta Mama ta kalli kan Rumaisa, da ta fara tsifa, tayi rabi ta bar rabi ta ce "Fita ki bar mini É—aki, karki sake shigowa sai kin gama wannan tsifar.
Fitowa ta yi ta na tura baki, tana nema ta yi kuka.
"Autar Mama, meya ɓata miki rai ne?" Cewar Yaya Abubakar da yake ƙoƙarin shiga ɗaki.
Dama ƙiris ta ke jira, dan haka ta fara kuka "Ba mama ce ta koreni daga ɗakinta ba, wai sai na gama tsefe kaina ba, ni mama ta tsaneni".
Girgiza kai ya yi ya ce "Yi haƙuri ki daina kukan, bari na zo na tayaki tsifar"
Haka suka zauna ya samu kibiya ya tsefe mata kan tsaf, suka wanke gashin, ya ce da safe zai bata kuÉ—in kitso.
Mama ta na kallonsu ba ta kula su ba, ta cigaba da sabgoginta.
Abdallah yana ta dube-dube a kitchen, ya ci karo da allon Rumaisa, duk gefensa ya karye, ga rubutun jiki yayi baƙi ƙirin, ba ta sake wani ba.
Ya fito da allon a hannunsa ya ce "Ruma, wannan allon naki yaushe zaki yi wani rubutun?" Ta haÉ—e rai ta ce "To ban iya ba, sai na iya zan wanke".
"Haka dai, ba kya ja a ko ina, daga arabin har bokon, Allah ya sa su zaneki idan ki ka je sati mai zuwa, baki wanke allon kin yi wani rubutun ba, gandamemiya da ke amma haryanzu a izifi biyu ki ke"
Sai da yayi wannan maganar ta tuna yadda malam Babba ya dinga ƙwala mata kira amma ta gudo gida, yanzu sati mai zuwa ta yaya zata je makarantar allon? Kuma muddin abin da ta yiwa malam ya zo gidan nan, ta san ta kaɗe".
"Astagfrillah, ni 'ya su meyasa haka ne, garin in gujewa wani hukuncin sai na faÉ—a wani tarkon, ya zan yi da raina?.
Ayshercool
08081012143
Kar a manta ayi subscribing YouTube channel É—ina na Cool hausa tv
[18/06, 2:35 pm] JAKADIYAR AREWA: ƘANWAR MAZA
   BY AISHA ADAM (AYSHERCOOL)
Ku yi subscribing YouTube channel É—in mu, domin samun daÉ—aÉ—an litattafan hausa na sauraro.
https://www.youtube.com/@CoolhausaNovels
Arewabooks @ ayshercool7724
Watpad@ ayshercool7724
MIKIYA WRITER'S ASSOCIATION
    p 4
Ko da sati ya zagayo, Mama tana sa ran ta ga Ruma ta shirya ta tafi makarantar allo, amma ta ga bata da niyyar yin hakan.
Sai ma aiki take a tsakar gida, wanda ba ta saba ba, tana naÉ—e yayyenta je komai.
Aliyu ne ya fito daga banɗaki, hannunsa riƙe da buta ya kalli Ruma ya ce "Ke ina makarantar allon?"
Ta ɗan ɓata fuska ta ce "Ni na cire kaina na daina zuwa".
"Saboda ke ki ka saka kanki, shine sama ta ka ki ka cire kan ki ko? Da alama baki da gaskiya"
Mama ta fito tsakar gida ta ce "Ali ajiye butar nan ka je mini makarantar allon ka ji me ta aikata, dan ban yadda da ita ba"Â dan jikinta ya bata Ruma wani laifin tayi.
"Wallahi Mama ba abin da na yi, ba sai ya je makarantar ba, idan ya je ma sharri za su yi mini, ba sa sona malaman"
Mama ta ce "Au malaman ne suke miki ƙarya Rumaisa, ai ko me za ace mini kin aikata ba zan musa ba"
Huzaifa daga cikin ɗaki ya ce "Dama saboda ƙawayenta ya sa ta ce ita ma a sakata a makarantar, ba dan Allah take zuwa makarantar ba ".
Aliyu ya saka jallabiyarsa ya tafi makarantar allon.
Bayan fitarsa rantse-rantse take ta yiwa Mama, akan ita fa ba abin da ta aikata a makarantar nan, amma Mama ta shareta.
"Ruma!"
"Na'am Yaya Sadik "
"Zo ki sayo mana ƙwai ki soya mana mu karya"
Kasancewar Ruma akwai kwaɗayi, ya sanya ta daina fargabar zuwan Aliyu makarantar su, ta karɓi kuɗi ta tafi aiken da Abubakar ya yi mata.
**********
A kashingiɗe take a kan kujera, ta ɗora ƙafa ɗaya kan ɗaya, ta tattara dukkan wata nutsuwarta a kan ƙatuwar wayar hannunta, da alama ko me take kallo mai muhimmanci ne.
"Samha me ki ke wa wannan kallon ƙurillar ne?"
Wadda aka kira da Samhan ba ta motsa ba, balle ta daina abin da take yi.
Hannu É—ayar ta saka, ta zare wayar daga hannun Samhan, tana dubawa.
Har a wannan karon, Samha ba ta yi motsi ba, balle ta karɓi wayarta ta ba.
"Samha kina da hankali kuwa? Wai dan Allah da gaske ki ke dama?"
Samha ta ja ajiyar zuciya ta ce "Nusaiba, ke da kin É—auka da wasa nake yi dama?"
Nusaiba ta jinjina kai ta ce "Eh, ni ban san abin da ki ke faÉ—a har zuciyarki ba"
Samha ta gyara zamanta ta kalli Nusaiba, cike da son tabattar mata abin da take faÉ—a ta ce "Nusaiba, ban fara dan na daina ba, ko zan tafi tsirara zan mallaki abin da zuciyata take muradi"
Nusaiba ta ɗan jinjina kai ta ce "Amma ya batun alaƙa fa, ko kin manta?".
"Alaƙa bata gabana, na san a yadda zan yi wasana. Kar ki manta anjima akwai walima a gidan Shamaki"
"Hmmm Allah ya kaimu, Allah ya sa ba wani banzan abun zaki yi ba".
Wani É—an guntun murmushi Samha tayi, ta ce "Koma dai menene, we should see"
********
Ko da Runaisa ta dawo gida daga aiken Yaya Sadik, tana daga tsakar 6 tarar da Yaya Aliyu a falo yana wassafawa Mama abin da aka gaya masa a makarantar allonsu, ga Yaya Umar a zaune.
"Wallahi mama ba ki ji yadda ake complain a kan yarinyar nan ba, malaminsu ya ce dama ko ta dawo korarta za su yi, ba karatun take yi ba, sai tsokana da fitsara, da damben da yaran mutane, wai sam ba ta da nutsuwa da É—a'a, malam Babba ya tara su zai hukunta su sun yi laifi ta É—au allonta ta gudu, yana kiranta amma tayi masa banza".
Cike da fushi Umar ya ce "Ba kune kuke goya mata baya take wani rashin mutuncin ba, tun da ta san ko me ta ɗauko zaku tare mata ba, ku bari ta tsokano waɗanda zasu nakasata yadda gobe ba zata ƙara ba. Babu wanda yake faɗar alkhairi a kan ta sai sharri" ya ƙarasa maganar yana fitowa tsakar gida cike da fushi.suna yin ido huɗu da Rumaisa ta saki ƙwan hannunta a ƙasa ta na ja da baya, saboda tsoro da fargaba.
Taku biyu ya yi ya danƙota, ya sanya hannunsa ya riƙe kunnenta ɗaya da ƙarfi.
Wani irin ihu ta kurma tana riƙe hannunsa, saboda ji tayi kamar zata ɗaga kai ta ga kunnen a hannunsa, saboda azabar zafi.
"Dan ubanki idan har ba zaki canza hali ba, makarantar kwana zan kai ki, tunda ba ki in da yake miki ciwo ba, ko mu mayar da ke can ƙauye, su miki aure"
Usman ya ce 'Ai Rumaisa sai ka ce wadda ta sha nonon aljana, hatsabibancin ta yayi yawa, ba ta jin magana sam"
Abubakar ne ya fito daga ɗakinsu a fusace, ya ƙaraso ya riƙe hannun Rumaisa, ya kalli Yaya Umar ya ce "Sakar mata kunne" Umar ya ɗan yi turus yana kallon Sadik.
"Baka ji bane?"
Sadik ya maimaita masa. Yaya Faruk ya saki kunnen Rumaisa, da idanunta tuni suka yi ja saboda kuka.
Ya janyota ya zaunar da ita a kan tabarma, ya dinga share mata hawayen fuskarta.
Cikin ɓacin rai ya ce "Yakamata ku dinga yiwa kan ku adalci a kan yarinyar nan, ita kaɗai ta tashi a cikinmu mace, tayaya zaku ce sai kun tanƙwarata yadda ku ke so? Tayi laifi kowa yayo kanta, ba mai yi mata nasiha, daga mai ce mata munafuka sai me ce mata aljana haka ake rayuwa?"
Yasir ya ce "Wallahi Yaya Sadik, duk ranar da yarinyar nan ta kwaikwaya maka rashin mutuncin da take aikatawa zaka gane ba tsanarta aka yi ba"
"Koma dai yane, a dinga barin yarinya ta huta a daina takura mata haka "
Guntun tsaki Umar ya ja, ya fice daga gidan gaba daya, suna zaman zamansu Mama ta haifo wannan 'yar kalen hanjin da ta gallabi rayuwarsu.
Yau cikin dare, Mama ta tashi tana ibada, kamar yadda ta saba domin a cewarta wanda duk ya tara zuriya yake neman kuma dacewa, bai ga ta bacci ba.
Fitilar É—akinta ta kunna, haske ya gauraye ko ina, Rumaisa tayi rashe-rashe a kan katifa, zaninta daban ita daban daga ita sai wando, kanta ko É—an kwali babu.
Mama ta girgiza kai, ta janyo zanin ta ɗaura mata, ta saka mata hula ta lulluɓeta, sannan ta fice ta ɗauro alwala ta zo ta tayar da salla. Sai dai sam Ruma ba ta san an yi bama, tana ta fama da bacci.
Can Mama ta kuma juyawa, amma ta ga Rumisa ta kuma yada zanin, ƙafafuwanta duk suna ƙasan katifar, ta kuma tumɓur tana bacci.
Haushi ne ya kama Mama, ta ƙarasa in da take, ta ɗala mata duka a cinya. Amma maimakon ta tashi, sai ta sake dunƙulewa tana bacci.
"Ke Ruma, ba zaki tashi ba sai na saka miki bulala?" Da ƙyar ta tashi tana murza ido tana kalle-kalle.
'tashi ki É—auki rigarki ki saka, ki É—aure kanki ki je ki yo alwala ki salla".
"Wai har asubar ta yi ne?"