← Book details Ƙanwar Maza Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 18 OF 47

Sashe 18

Ƙanwar Maza Complete Hausa Novel · about 8 min read

Mama ta ce"Ai ba ƙarya ta yi ba, ku yi ta kwasar mini kwanuka kuna kaiwa ɗakin ku, sai na bi na tsinto abina, ƙazaman banza kawai"

Mama na tsaka da mitar sai ga Aliyu ya shigo, ya ce "Ina ruma"

Ta ce "Gani"

"Yo sauri, abokaina ne na filin ball suke tambayata kina ina, shi ne suka biyo ku gaisa, saura kiyi wani haukan da zaki zubar mini da mutunci ".

Murmushi ta yi ta ce"A'a ba zan zubar maka da mutunci ba, bari na sako gyalena"

Yana maganar ya fice, Huzaifa ya ce "Mama ke ba a zo gaishe ki ba, sai wannan yarinyar lallai ruma".

Ta fito daga É—akin mama da sauri, ta kalli Huzaifa ta ce "Ka yi mini Addu6, Allah ya sa su bani kuÉ—i" tana gaya masa ta kwasa da gudu ta fita waje.

Da fari gaishe su tayi kamar nutsatsiya, suka amsa mata cikin mutuntawa.

"Ya makaranta ya rikici2?"

Ta ce "Makaranta lafiya ƙalau, amma ni bana rikici" suka din ga jan ruma da hira ita kuma tana zuba, Aliyu sai hararta yake amma ta cigaba da zuba.

Dariya suka dinga yi mata, suka babbata barka da salla, ko ɗan cewa ba zata karɓa ɗin nan ba tayi ba, zuruf ta miƙa hannu ta karɓe tana godiya.
Wani mugun kallo yake wa ruma, amma ko saurararsa ba tayi ba.

Ta duba a cikin kuɗin da aka bata, akwai ɗari biyu da ta tsufa sosai, ta kalli wanda ya bata ya ce "Ɗan uwanmu ɗan canza mini wannan, ba zata karɓu ba" buɗe baki Aliyu ya yi yana bin ruma da kallo.

Aikuwa ya karɓa ya canza mata wata, ta ce ta gode ta shige gida.

"Mama kin ga abokan yaya Aliyu sun bani, kuma sun ce suna gaishe ki"

Mama ta ce "To madalla"

"Mama gashi ki ajiye mini, ki ɗora da lissafi, idan kin manta ni ina sane da lissafin, dan Allah mama kar na zo karɓar kuɗina ki fara ce mini, abubuwan da ki ke mini ba da kuɗina ki ke yi mini ba, wallahi mama da za ayi lissafi ban san iya adadin kuɗin da nake bin ki ba"

Cikin gatse mama ta ce "To Anty ruma, ki zauna ki lissafa duk kuÉ—in da ki ke bina, na biyaki"

"Dan Allah mama da gaske ki ke?"

"Eh mana" murna ta dinga yi tana cewa 'Ai mama kuÉ—in da nake binki, sai ma zauna musamman na yi lissafi, tsaf sai na zama attajira da kuÉ—in nan, unguwar da muke zuwa a bani kuÉ—i ai da yawa"

Yasir ya ce "Ba zaki taɓa hankali ba".

Aliyu ne ya shigo rai a ɓace yana hararar ruma.
Kawar da kanta tayi gefe taƙi kallonsa.

"Dole ki kawar da kai mana, yarinyar nan ana bata kuɗi ta karɓe, wai har da cewa wai wata ba zata karɓu ba, da yake ke ki ka basu ajiya"

"Yaya ba kyau mayar da hannun kyauta baya fa"

"Zaki mini shiru, ko sai na mareki, mara kai kawai"

A ranta ta ce "Ohoo dai, tun da Allah ya sa na karɓa".

Bayan sallar isha'i yaya Umar ya dawo, duk sun daddawo suna gida, ana ta hira.
Ruma tayi gyaran murya, ta kalli Yaya Usman ta ce "Mama kin san me?"

Mama ta ce "A'a".

Usman ya zubo mata ido, kowa ya yi shiru yana sauraron wani shirmen zata faÉ—a.

Ayshercool
08081012243

(INCLUDE ME IN YOUR PRAYERS PLEASE 🙏)
[05/07, 5:40 pm] JAKADIYAR AREWA:                     ƘANWAR MAZA
                

Na Aisha Adam (Ayshercool)

MIKIYA WRITER'S ASSOCIATES

https://www.youtube.com/@CoolhausaNovels

Ku yi subscribing  YouTube channel ɗin
@Cool Hausa Novels, domin samun daÉ—aÉ—an litattafan hausa na sauraro.

P9

Wani irin kallo Usman yake mata, amma ta basar ta ce "Mama kin san me yaya Usman ya yi?"

Mama ta ce "A a sai kin faÉ—a"

Usman ya ce"Haka muka yi da ke ruma?"

"Oho ni dai bana munafurci da rashin gaskiya, duk abin da aka yi mama bata nan sai na gaya mata, ba zan ga ana ba dai-dai ba mama bata sani ba na yi shiru".

Kamar ya yi kuka ya ce"Amma haka muka yi da ke?"

Mama ta ce "Gaya mini ina jin ki"

Ruma ta kalli Usman ta ce "Sai dai ka yi haƙuri fa, amma wallahi sai na faɗa a gaban kowa da kowa, ba zan zuba ido ana abin da ba dai-dai ba"

Ba dan ya san idan ya yinƙura zai yi mata wani abu mama zata hana ba, da sai ya kife Ruma da mari, ya san idan ta ɗaga maganar nan akwai damuwa, zai sha faɗa da mita.
Uwa uba ga Yaya Umar a zaune a wurin, kuma ba shi da tabbacin iya abin da ruma ta gaya masa ta ji, shi kaÉ—ai É—in ta ji, dan kawai É—aga kai ya yi ya ganta a tsaye lokacin da yake wayar.

Ta gyara zamanta sannan ta ce "Ɗazu, da ki ka aikeni kai tuwo gidan mai ƙuli, na ganshi a ƙofar gidan su wannan abokin nasa Yahaya, shi da abokansa sun dawo daga idi, ko gida ba su zo ba, ya zauna an fito da abinci sun haɗu suna ci, kuma kin hana hakan"

Ajiyar zuciya ya yi, yana hamdala da ba wancan zancen ta yi ba.

Mama ta ce "To wannan abun ne ki ke ta zuzutawa, ai shima ya zo ya É—au abinci ya fita da shi sun ci tare"

"To mama sai aka ce ya je ya zauna a ƙofar gida yana cin abinci ai rashin kamun kai ne, kuma ke ki ka ce rashin kamun kai ne fa".

Mama ta ce "To shikenan, za a yi masa faÉ—a".

"To mama kiyi masa faÉ—an mana yanzu"

A fusace ya ce "Ke wai ni sa'an ki ne?"

Umar ya ce "Maganinku kenan da ku ke wasa da ita"

Can ta sake gyara zama ta kalli mama ta ce "Mama, kin san wani abu?"

"Ke na gaji da wannan shirmen naki fa" mama ta faɗa cikin ƙosawa.

"Mama ba shirme zan ba, É—azu na ga Habiba a masallacin idi, da tsofaffin kaya na ganta".

"To ina ruwanki? Kin ga ina rabaki da sabgar munafurci amma ba zaki dai na ba ko?"

Jiki a sanyaye ruma ta girgiza kai ta ce "Mama so nake a bata kaya É—aya a cikin kayana" gaba É—aya juyowa suka yi suna kallon ta jin abin da ta ce.

Huzaifa ya ce "Kina da hankali kuwa?"

"Amma dai ka san tun da nake ni ba mahaukaciya ba ce ko? Mama dan Allah a bata ita ma ta saka sabon kaya"

"Rufewa mutane baki, mara zuciya nan babarta ta zo ta ciwa mutane mutunci, amma ki ka cigaba da shishshige mata, ba za a bayar ba É—in" Aliyu ya faÉ—a yana zaro ido.

Mama ta girgiza masa kai, ta dubi ruma ta ce "Allah ya kaimu gobe, sai ki zaɓi wanda zaki batan"

Murmushi ruma ta yi ta ce "Na gode mama, Allah ya saka da alkhairi, to zaki É—an zuba mini naman kazar ita ma na kai mata ta ci, na san su basu yanka kaza ba".

Yasir ya ce "Dama ta yaya zasu yanka, wannan babar ta su tana kiwon kaji kamar su kasheta, amma ba zata yanka su ci ba, bayan talauci har da son zuciya"

"Ka daina zagar mini babar ƙawa dan Allah"

Mama ta ce "Kin ga, tashi ki wuce ki je ki kwanta"
Ta miƙe ta shige ɗaki, mama ta mayar da idonta kan Aliyu ta ce "Aliyu, kar ku hora yarinyar nan a kan halin rowa, duk rashin jin ta tana da tausayi da son taimako, idan har abin da za ta yi bai saɓawa shari'a ba ku ƙyaleta"

Aliyu ya jinjina kai. Ruma kuwa ji take kamar ta janyo washegari, ta kai wa habiba wannan kayan, ita ma ta saka ta ji daÉ—i.

Washegari da wuri ruma ta yi wanka, ta yi kwalliyar salla da É—aya daga cikin kayanta, ta zauna ta É—aukarwa Habiba set É—aya na atamfa har da ribbon da abin hannu.
Mama bata hanata ba, ta ƙulle mata nama ta bata ta kai wa Habiban.
Har zata É—auka ta fita, ta tsaya ta ce "Mama, dan Allah idan ta yi kwalliyar zamu je gidan 'yan ajinmu mu yi wasa".

Mama ta ɗan ɓata fuska ta ce "Amma dai kin san babna son wannan abun ko, ba na son yawace-yawace"

Ta É—an marairaice ta ce "Dan Allah mama, kin san bana yawo, daga aike sai makaranta, yanzu fa salla ce".

"Shikenan, na ji, saura kuma ki je ki zauna sai an nemo ki, ina da ina zaku je?"

Ruma ta lissafa mata, mama ta yi ajiyar zuciya ta ce"Yanzu ƙarfe goma da rabi, kar ki wuce sha biyu, idan ki ka wuce abin da zai zo biyo baya ba zai yi miki daɗi ba".

Cikin murna ta ce "Mama da wuri zan dawo in sha Allah " ta yi waje ta na murmushi.

Kai tsaye gidansu Habiba ta nufa, ko da ta je ta yi ta sallama, shiru ba a amsa ba.
Tsayawa ta yi a tsakar gidan ta cigaba da sallama.
Sani ne ya leƙo yana amsawa, yana ganin ruma yayi saroro ya ce "Ke uban me ki ka zo yi mana a gida?"

Hararsa ta yi ta ce "To ina ruwanka ai ba wurinka na zo ba, ba yayana yayi maka tsakani da ni ba, babu ni babu ba, ko kuma na kira shi, ya zo ya ƙara kumbura maka fuska"

Tana tsaka da maganar, sai ga babar Habiba ta fito daga banÉ—aki, tana ganin ruma ta tsuke fuska ta ce"Ke me ki ka zo yi mini a gida?"

"Gurin Habiba na zo"

"Da izinin wa ki ka zo wurin Habiban?"

Habiba ce ta fito daga ɗaki, hannunta riƙe da kwanon tuwo da miyar kuka, tana ganin ruma ta ce "Laaa ruma, kin dai na zuwa makarantar allo "

Ruma ta ce "Ba na ganki a masallacin idi ba ki ka ƙi kulani"

Habiba ta ce "Wallahi ruma ban ganki bane ba? Ya salla?"

"Lafiya lau, wurin ki na zo, zo ki ji?"
Chapter 18 · 0% Book details