← Book details Ƙanwar Maza Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 33 OF 47

Sashe 33

Ƙanwar Maza Complete Hausa Novel · about 8 min read

DPO ya ce "Yanzu Madam, so ki ke a kai ku kotu ke da wannan yarinyar jikarki ko kuwa?"

Aliyu ya ce"Yallaɓai, ta ƙirga abin data kashe, in sha Allah ba zai gagara ba sai a biyata"

Sai da ta ji haka hankalinta ya É—an kwanta, ta lissafa kuÉ—i dubu talatin da biyar ta ce a biyata.

Aliyu ya ce"Yallaɓai a nema mana sassauci, wallahi yarinyar nan marainiya ce, kuma na gaya maka, tana da matsalar ƙwaƙwalwa, ana kai ta shan magani, ana ta abin da za a ci ga karatun ta, ga rashin lafiya abun da yawa"

"Wallahi lafiyata ƙalau, ni bana rashin lafiya sai zazzaɓi, ko gudawa, amma dai wataran idan raina ya ɓaci sai na ji aljanuna sun tashi, ƙarfina ya ƙaru, idan na kama mutum na dunƙule hannu na dinga dukansa ko hmmm ba a magana, da na ce na daina dambe saboda mama ta daina fushi, ita Asiyar ce ta janyo muka yi faɗa".

Aliyu ya ce "Dalla rufewa mutane baki, Yallaɓai ba ta da cikakkiyar lafiya"

Headmaster ya ce "Amma ai mu da ku ka kawota makarantar baku gaya mana ba"

Babar Asiya ta dage, ba zata rage ko sisi ba, DPO ya ce zai biya dubu ashirin a aljihunsa, su ruma su biya dubu goma ".

Aliyu 'yan kuɗin registration ɗin sa ne da yake tarawa, haka ya biya, suka din ga bada haƙuri shi da ruma.

Duk da wannan abu, babar Asiya ba ta huce ba, dan ta so a zane ruma, sai dai bisa ga mamakinta yarinyar sa'ace da ita, babu wanda ya daketa, sai ma nasiha da DPO ya yi mata, yana cewa Aliyu "Ka ga irin wannan yaran, idan aka yi haƙuri, suna da ɓoyayyiyar baiwa da Allah ya yi musu, da al'umma za iya amafana, ku yi haƙuri ku cigaba da kai ta Asibiti tana ganin likita, da sauƙi tun da har tana iya zuwa makaranta, sannan ku kiyaye abin da zata din ga kallo".

"Kaii wallahi ni babu wani likita da nake gani, nifa lafiyata ƙalau, wato Yaya Aliyu kana nufin ni mahaukaciya ce?" Harar ya watsa mata yana yi mata daƙuwa suka cigaba da magana da DPO.

bayan sun fita daga ofishin, Headmaster ya ce ruma ta zauna a gida, sai wani satin sa duba su gani idan zasu iya bari ta cigaba da zuwa makarantar.
Tsalle ta yi tana faÉ—in Alhamdilillah.

Aliyu ya girgiza kai ya ce "Mara hankali kawai"

******
"Takawarka lafiya magajin galadima, Allah ya baka yawan rai, ya ja kwanan hajiya" ɗaya daga cikin hadiman Mummy kenan, da ta ware maƙogwaro, take ta zabga wa Adam kirari kamar za ta dungura, maƙogwaronta ko zafi ba ya yi mata.
Hannu ya É—aga mata, ya cigaba da tafiya zuwa cikin falon.

Sanyi A.C ya cika ɗakin, ga ƙamshin turare da ya haɗu ya gauraye falon.

Risunawa ma'aikatan da ke cikin falon suke yi a gareshi, tamkar sun ga sarki.

Jinjina musu kai ya yi, ya nemi wuri ya zauna a ɗaya daga cikin kujerun falon. Ya shafe a ƙalla mintuna takwas, sannan ta fito cikin wata haɗaɗiyar shadda sai ɗaukar ido take yi.

Ta na ganin Adam, ta yalwata murmushin fuskarta ta ce "Hutawarka lafiya takawa, fatan ana lafiya? Kuma ina fatan ba a gaji da jirana ba, ina shiryawa ne"

Girgiza mata kai yayi ya ce "Barka da wannan lokacin"

"Yauwwa barka dai, an dawo lafiya ya ibada?"

"Alhamdilillah"

Ta sake yin murmushi sannan ta ce 'Ai har na fara shirin zuwa da kaina na kwashi gaisuwa, na ji labarin ka dawo, amma ba ka zo mun gaisa ba, kuma har aka yi bikin gidan Turaki aka gama ban ganka ba, ko jikin ne?"

Ya É—aga idanuwansa ya kalleta, amma bai bata amsa ba.

"Well, kun haÉ—u da Mahmud kuwa?, yazo gari shima ya kusa komawa ma, ya dawo lokacin kana saudiyya"

"Dama zuwa na yi na gaishe ki, and a gayawa su Fauziyya ba na son yawan fitar nan" yana kaiwa nan a maganarsa ya miƙe, ya fara takawa sannu a hankali.

Murmushi ta yi ta bi bayansa da kallo. "A zahiri mutum har mutum, amma baÉ—ini ba wanda ya san cikakken waye, kamar bil adama kamar kuma wani abu daban, da ni ki ke zancen Binta, sai na rabaki da komai sai na tabattar da na huce a kam abin da kk ka yi mini" ta yi maganar a hankali tana bin bayan takawa da kallo.

Ya kai tsakiyar falon, Mahmud ya buɗe ƙofar ya shigo, ganin junansu ya sanya suka yi turus, suna musayar kallo, kamar abokan gaban da suka yi shekara da shekaru ba su haɗu ba sai yau.

LITATTAFAN DA NA RUBUTA SUN HAÆŠA DA.

ABDULJALAL (FREE BOOK)
AƘIDATA (BOOK1 FREE 2 PAID)
WATA KISSAR SAI MATA (FREE)
WUTA A MASAƘA (FREE)
RUƊIN ƘURUCIYA (BOOK1 FREE 2 PAID)
GABA DA GABANTA (1FREE 2 PAID)
ƘANWAR MAZA (1FREE 2 PAID)

Mai buƙata ni zai tuntuɓa ta lambata Please, a din ga biya kan a karanta, in kin sai littafi baki faɗi ba, atleast kin taimaki marubuciyar da bata ƙwarin gwiwa 😒

https://www.youtube.com/@CoolhausaNovels
*Wai ina da ku fans, ace haryanzu ban haɗa 1k subscribers a channel ɗi na ba, anya akwai amana kuwa😒*

Taku har kullum
Ayshercool
08081012143
[24/07, 7:43 pm] JAKADIYAR AREWA:                     *ƘANWAR MAZA*

Na Aisha Adam (Ayshercool)

MIKIYA WRITER'S ASSOCIATES

*MAMAN MEENAT COLLECTION, MAMAN MEENAT SUPPLEMENT/SKIN CARE*

*SHI YAR UWA KINADA LABARIN* *SHAHARARRIYAR MAI SAYAR  DA SUPPLEMENT DIN NAN KUWA? TO IDAN BA KI SANI BA KIYI MAZA KI GARZAYA DOMIN KEMA KI SAMU RABONKI DOMIN ZATA GYARAKI TSAF KI FITO KAMAR SABUWAR AMARYA, KEMA KI SHAGA CIKIN MATAN DA SUKE HASKAKAWA KAMAR TAURARO. SHIN ƘURAJE NE SUKE DAMUNKI, KO KUMA MATSALOLIN FATA NE? KO KUWA SO KI KE FATARKI TA DIN GA SHEƘI TA NA HASKAWA? MAZA KI GARZAYO WURIN MEENA DOMIN SAMUN MAFITA*

*Royal jelly big 22000*
*Royal jelly 30 pieces 2200*
*Royal jelly small one 60 pieces inside the pack 3000*
*Vitamin C-100, 2700*
*Vitamin E big 3000*
*Pesona 2300*
*Dara 2300*
*Cantik ayu 2300*
*GLUTA white 2700*
*Khusus ibu 3800*
*Sugar wanita 3500*
*Majakani 3 in 1 3200*
*Eve Care 3700*
*Juliet eve 11,500*
*Phyton buster 18,000*
*Phyton collegen 18,000*
*Glute sparkling 18,000*
*7 days ginger oil for hair 1,200*
*Papaya oil for breast 1,200*
*Garlic oil for hips 1200*
*Vitamin C serum 1,500*
*Vitamin E serum 1,500*
*Busty blend 2800*
*Gluta prime 2800*
*Collegen+C 3800*
*Yan uwa abun fa da yawa bazan iya kawosu gaba daya ba amma muna da duk wani supplement da kuke bukata masu kyau da inganci tested and trusted, sayen na gari mai da kudi gida, gaskiya da Amana shine takenmu sannan Maman Meenat collection ba anan kadai ta tsaya ba muna saida turaruka kowanne irin na wuta dana jiki, da Airfreshners, sayen daya ko sari ke dai kawai neme ni a wannan number call or chat 08039437158*

https://www.youtube.com/@CoolhausaNovels
*Wai ina da ku fans, ace haryanzu ban haɗa 1k subscribers a channel ɗina ba, anya akwai amana kuwa😒*

Ku yi subscribing  YouTube channel ɗin
@Cool Hausa Novels, domin samun daÉ—aÉ—an litattafan hausa na sauraro

Page 16

Kallon-kallo suka shiga yi wa juna, aka rasa wanda zai bawa wani hanya, Mahmud ne ya fara janye nasa idon ya wuce yana wani irin taku cike da rainin hankali, ya bawa Adam hanya.
Cikin hanzari Adam ya bar falon, yana jin wani abu yana tsikarar zuciyarsa.

Adam na fita, Mummy ta taso ta na faÉ—in "Mahmud ya haka, meyasa ba zaka tsaya ku gaisa ba, kamar ba É—an uwanka ba?"

Mahmud ya ce "Mummy, ni baki ga abin da ya yi mini ba? Lokacin da ya sauke girman kai ya duƙa mini, wataƙila na fara saurarasa"

"Haba Mahmud, shi ne fa gaba da kai, ya zaka ce haka? ni fa bana son ace ina ziga ka, kuma ko ba komai ya ci sunan mai martaba, ya cancanci ka girmama shi, kuma idan Allah ya sanya sarautarmu ta dawo gidan nan, ka san shi ne magajin babanku, shi zai zama galadima tun da shi ne babba"

Ya dubi Mummy ya ce "Ni wata sarauta ko wani abu makamancin haka bai dameni ba, a naɗashi sarki ma gaba ɗaya, wannan shi ta shafa, look Mummy, a bar wannan zancen ni bani da lokacinsa, bari na je na karya"  yana gama maganar ya wuceta, ya na bada baya, Mummy ta yi murmushi ta ce "Haryanzu ina wasana yadda nake so, Mahmud dole na ɗarsa maka zaƙin mulki da ƙaunar sarauta, sannan kuma azo a rasa sarautar gaba ɗaya mu je zuwa".

****
Aliyu suna tafe a hanya, yana ta yiwa ruma faÉ—a.

"Dan ubanki kuɗin makaranta na, na registration na fara tarawa, yanzu kin saka na kwashe na bayar a banza, ban ci ba ban sha ba, dan ma Allah ya sanya DPO ya biya mafi yawa daga kuɗin. Saboda ba ki da mutunci ina kareki ki na ƙaryata ni, ni dama na ƙyaleta ta yi miki shegen duka".

Ta waro ido ta ce "Kaii, idan ta sumar da ni fa?"

"Ai gara ta sumar da ke É—in, tun da ke dai har abada ba kya hankali, wai ki ka karya 'yar mutane saboda tsabar kanki ba daÉ—i"

"To ba kai ne ka ce mini mahaukaciya ba, wai ana kai ni asibiti"

"To meye marabarki da mara hankalin? Zaki gane kurenki ne, bari mu je gidan sai na daki kuÉ—ina" har suka isa gida, ruma ba ta sake cewa komai ba.

Mama na ganin Aliyu tare da ruma sun dawo, ta fito daga É—aki ta na tambayar ko lafiya?

Ruma ta É—an sosa kai tana kallon Aliyu.
"Zaki dai na kallona ko sai na tsokane idon? Sai ki yi mata bayanin abin da ki ka yi ai".

Ruma ta kalli mama, kamar zata yi kuka ta ce "Wallahi mama tsautsayi ne"

"Tsautsayin me? Me ki ka aikata kuma?" Ruma ta yi tsilla-tsilla da ido.

"Ba zaki gaya mata ba"

"Mama, da wasa fa na gwada irin na wrestling É—in nan, shi ne wata ta karye"

A É—an hasale mama ta ce "Kai ka gaya mini abin da ta yi mana, ka tsaya ka na mini wasa da hankali".
Chapter 33 · 0% Book details