← Book details Ƙanwar Maza Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 21 OF 47

Sashe 21

Ƙanwar Maza Complete Hausa Novel · about 8 min read

Cikin gajiya da halin ruma mama ta ce "Ki tashi ki cire uniform ki yi wanka"
Ruma ta tashi ta cire kayanta, ta É—ebi ruwa ta shiga wanka. Ta na tsaka da wankan, ta jiyo muryar Usman ya shigo, daga banÉ—akin ta buÉ—e murya ta ce "Yaya Usyy Albishirin ka"

"Ruma ban hanaki surutu a banÉ—aki ba?"

Ta ce 'yi haƙuri mama"

Ba dan ta gama wankan ba, cikin zumuÉ—i ta fito daga wankan 'Yaya usman, bari na nuna maka wani abun mamaki"

Ba ta san a ya ta fito daga banÉ—akin ba, sai da mama ta daka mata tsawa, daga ita sai pant ta fito. Ta koma ta É—auko zani, sannan ta kwaso kyaututtukanta ta nunawa Usman.

Ya kalli ruma sannan ya kalli kayan ya ce "Ruma ban yarda da ke ba"

Ta ce "Saboda me?"

"Ina ki ka ga kwanyar da zaki yi wani abun arziki ke?" Tsuke fuska ta yi tana kallonsa ta ce "To me ka ke nufi?"

"Ɗauko takardar da aka baki, na yi miki tambayoyi" ta miƙe ta je ta ɗauko masa takardar ta miƙa masa.

Ga mamakinsa duk abin da ya tambayi ruma, sai ta bashi amsa daidai ko gyaranta ba ya ci.
Ya ajiye takardar, ya kalli ruma ya ce "Ni fa haryanzu mamaki nake, matar da take zuwa ta kusa da ta ƙarshen aji, ita ta yi wannan ƙoƙarin"

Ruma ta yi murmushi sannan ta ce "Ikon Allah kenan, baku san haushin da nake ji idan aka ce mini daƙiƙiya ba, shi ya sa na dage na je na iya"

"Congratulations, ina ma zaki cigaba da dagewa da kin ga cigaba a rayuwarki"

Ta taɓe baki ta ce "A'a da wahala gaskiya, ka san baƙar wahalar da na sha kan na iya wannan abun, dan a dai na ce mini daƙiƙiya daga wannan ba zan kuma ɗaukar dala ba gammo ba"

Usman ya yi murmushi ya dafa kafaɗarta ya ce "Haba ƘANWAR MAZA, rayuwa ce fa, kuma idan da rai da lafiya yanzu aka fara, kar ki sake ɗarsawa ranki cewa akwai wani abu da zai gagareki komai wahalar sa, rayuwa sai da gwagwarmaya da faɗi tashi, musamman ga ɗan talaka. Kar wani abu ya ƙara razana ki, ko ki yadda ke daƙiƙiya ce zaki iya komai kema"
Ta yi ajiyar zuciya sannan ta ce "Dan Allah da gaske Yaya Ussy?"

Ya jinjina mata kai ya ce "Sosai makuwa, ki dubi rayuwarmu a cikin gidan nan, tun baki da wayo, har zuwa yanzu a cikin gwagwarmaya muke, farincikinmu kawai ki ke gani, amma kowa akwai kalar ƙalubalen da yake fuskanta, ki kalli mama ba ta yi karatu mai zurfi ba, amma ta cancanci a kirata jarumar uwa, ba lallai ki fuskanci me nake nufi ba a yanzu, amma ki saka maganganun nan a ranki akwai ranar da za su yi miki amfani. Amma ki tsaya a kan ƙafafuwanki, ki fuskanci abin da yake baki tsoro, ke fa jaruma ce, bai kamata sunan daƙiƙiya ya biki ba"

Ruma ta É—an yi shiru sannan ta kalli Usman ta ce "Yaya Usy, in sha Allah zan dinga mayar da hankali na yi karatu sosai na daina wasa"

"Yauwwa ko ke fa, ai hakan ya fi deluwa"

"Kuma zan cigaba da ƙoƙari, in zama mai ƙarfi sosai, duk wanda ya tsokane ni, in yi masa dukan tsiya in farfasa masa baki da hanci, in kakkarya mutum"

Mama da take jin su ta ce "Ke kuma ba kya fatan ki girma ki yi hankali, sai rashin hankali ke ba kya fatan Allah ya shiryeki ki daina faÉ—ace-faÉ—acen banzan man a matsayinki na mace, faÉ—a ba na 'ya mace bane"

Ruma ta ce "A'a mama, gara ki bar ni na koyi ƙarfi sosai"

"Sai kuma ki yi ai".

Usman ya kuma murmusawa ya ce "Ba irin wannan ƙarfin ake magana ba, ƙarfin zuciya da kaifin basira wurin sarrafa duk wata Matsala da za ta tinkaro ki, kar ki bari matsalolin ki su razana ki, ko sau ɗaya kar ki bada wannan damar, ki turje ki dake ƙalubale duk girmansa, ki yi gaba da gaba da shi"

Ruma ta ce "Mhmm, gashi dai hausa ka ke yi, amma bana gane me ka ke faÉ—a, sai na ji kamar ma wani yaren ka ke daban, ban wani gane me ka ke nufi ba"

"Ni ma na san ba zaki gane a yanzu ba shekarunki da hankalinki babu lallai ya kai, saboda ke a yanzu ba ki sa wata damuwa ko matsala. Tashi ki zubo mana Abinci mu ci" Ruma ta miƙe ta tafi kitchen.

Mama ta ce "Kai ma banda abinka, wannan zaka zaunar ka na wani gayawa wannan bayanan, me zata gane a ciki? Ita ban da wautarta da tambayoyin ta na rashin kan gado me ta sani?"

Usman ya ɗan yi shiru sannan ya ce "Haka kurum mama ina jin tausayin yarinyar nan, jikina na bani za ta yi gwagwarmaya a rayuwa, gwagwarmaya a bugiren da ba zamu iya tsaya mata ba, ko yi mata wani taimako ba, gwagwarmayar da take buƙatar ta tsaya da ƙafarta ta cimma nasara"
Mama ta ce "Tooo ikon Allah, to koma dai menene, ni dai addu'a kullum cikin yi muku ita nake, ba ku kaÉ—ai ba, dukkan 'ya'yan muslmai baki daya, Ubangiji Allah ya shiga lamarinku, ya tsare gabanku da bayanku, ya kula da rayuwar ku"

"Amin mama, Allah ya ƙara miki lafiya da nisan kwana uwa ma bada mama"

"Amin ya rabb"

A ranar duk wanda ya shigo, sai ruma ta nuna masa kyaututtukan da aka bata, har a waya sai da aka kira mata yaya Abubakar ta gaya masa, tun ana tayata murna da Allah ya sanya albarka har ta fara ƙular da mutanen gidan. Dan hatta maƙwabta sai da ta shiga ta gaya musu ai tayi ƙoƙari a makaranta an bata kyauta.
Da ta je Islamiyya kuwa, har ofishin shugaban makaranta ta je, shi ma ta gaya masa, ya tayata murna tare da sanya mata albarka, ta ƙarasa staff room bayan sun gaisa da malaman suma ta gaya musu ai a makarantar boko tayi ƙoƙari an bata kyaututtuka. Nan suka yi ta mata fatan alkhairi, ji take a duniya yau ta ƙure daɗi tayi abin da ba ta taɓa ba.
"Malam to idan an idar da salla dan Allah a sanar"

Wani malami ya kalleta ya ce "A sanar da me?"

"Na yi ƙoƙari a makarantar boko mana, har na ciyo kyauta, word kusan ɗari biyu da hamsin fa na haddace yadda ake spelling ɗin su"

"To amma ai nan ba makarantar boko ba ce ba, ki bari idan ki ka yi bajinta a nan ma, sai a sanar wa É—alibai"

Ruma ta ce "A'a malam gara ai a sanar, saboda masu ce mini daƙiƙiya su san ƙwaƙwalwata na aiki, wataran zan bayar da mamaki".

Malam Habibu ya yi caraf ya ce "Ƙwarai kuwa, dole a sanar da ɗalibai wannan namijin ƙoƙari da ki ka yi, nima ba rannan na yi ƙari kin iya ba, duk za a sanar kar ki damu" cikin jin daɗi ruma ta ce "Yauwwa malam na gode"

Bayan tafiyarta ya yi dariya ya ce "Yanzu idan ba ku yi yadda take so ba, Allah kaɗai ya san wace tijarar zata yu, amma yanzu idan aka faɗa ɗin, za ta ji daɗi da ƙara samun ƙwarin gwiwa".

Ruma da ta ga an idar da salla, ana neman a watse ba a sanar ba, ta tafi ƙofar masallacin maza, ta leƙa ta ce "Malam Habibu kar ka manta fa, na ji ba a faɗa ba".

Malam Habibu ya ce "To bari a sanar, ai yakamata wannan abin arziki haka"

Haka malam Habibu ya tashi ya ce "'yan uwa ɗalibai da malamai, a taya 'yar uwa murna, wato 'ya ta rumaisa, bisa nasara da ta yi a wata gasa da aka shirya a makarantar bokon su, har ta samu kyaututtuka dan Allah ayi mata Addu'a, Allah ya ƙaro nasarori"

DaÉ—i kamar ya kashe ruma, masu dariya na yi, masu jin haushi na yi.

Huzaifa da suka yi salla sahu É—aya da Yasir ya ce "Ka ji abin da wannan mara kan gadon ta yi ko?"

"Bar motsatsiya, suma malaman da suka biye mata, idan ba tayi wasa ba sai na ƙona banzayen litattafan da aka bata, kowa ma ya huta".

Cike da annashuwa ruma ta tafi gida, ta je ta bawa mama labarin yau har a wurin salla, aka sanar da ta ci kyauta a makarantar boko. Tana shiga gidan ta tarar da Yaya Abubakar ya zo hutu, da kuma waa dattijuwar mata a zaune a tsakar gida.
Da sauri ruma ta nufi dattijuwar ta faÉ—a jikinta ta ce "Gwaggo Atine, yaushe rabon da na ganki?"

Dattijuwar ta washe baki ta ce "Dama ina zaki ganni, nayi-nayi da babarki ta din ga kai mini ke ina ganinki, amma ta ƙi saboda ina ƙauye".

Mama ta ce "Haba Yaya Atine, wallahi ba haka bane ba, kin san yanayin makaranta kuma ruma ba ta ji idan aka kai miki ita sai ta gallabe ku"

Ruma ta haye kan cinyar matar cikin jin daÉ—i ta zauna.

Matar ta ɗora da cewa "Ba wani rashin ji, a kawo mini ita a hakan ina son ta, duk rashin jin ta. Ɗan uwana ya ƙallafa rai a kan ta yana son ta, nima ina matuƙar ƙaunarta da na ganta shi nake tunawa amma ba za a kawo mini ita ba, sai wannan ƙartin ne kawai suke zuwa in da nake" ta yi maganar tana fashewa da kuka.

Mama cewa take "Allah ya baki haƙuri, in Allah ya yarda za a dinga kawota".

Ruma kuwa ta kalli Gwaggo ta ƙyal-ƙyale da dariya ta ce "Dan Allah Gwaggo ki daina wannan kukan, ni wallahi fuskarki dariya take bani idan ki na yi, kin ga yadda ki ke yamutsa kuwa?"

Yaya Aliyu ya ce "Ai gara ta fara gwada miki halin"

Gwaggo ta tsaya da kukan ta ce "Rumaisatu, kukan nawa ne yake baki dariya?"

Ruma ta ce "Eh mana, amma ki daina ce mini wata rumaisatu, sai ka ce wata masara, kowa aka saka masa suna mai daÉ—i a gidan nan, amma aka saka mini wata Rumaisa kamar masa"
Chapter 21 · 0% Book details