Sashe 14
Ƙanwar Maza Complete Hausa Novel · about 8 min read
Kamar yadda ruma ta saba kwatsa zance, bayan kowa ya halarra, haka yau ma sai da kowa ya halarran, an gama cin abinci sannan ta gyara murya ta ce "Yasir, wai yaushe ku gama karatun É—azu da naje ajinku".
"Ban sani ba" ya bata amsa.
"Mhmm ai dama ba zaka sani ba, nifa gaba ɗaya mutuncin malamin nan ya zube a idona, wallahi mama idan kin ji me yake gaya musu sai kin riƙe baki, duk da wani abun bana ganewa, duk basu san daga waje ina jiyowa ba, kuma maimakon Yasir ya fito daga ajin nan, amma ina yana zaune ana koya musu abin da bai kamata ba.
Saroro yasir ya yi, ya ji me aka koya musu da bai kamata ba, suna haɗa ido da ruma, ya tuna karatun da aka yi musu, kan ya kai ga ɗaukar mataki ta ce "Ina ji ai yana ce muku, wai ko idan mutum ya rungume mace alwalarsa ba ta karye ba, ko kiss, dan Allah wannan mama ba iskanci bane da ɓata tarbiyya, nan idan muna kallo aka nuno kiss ɗauke tashar ake yi, amma wai malaminsu yake gaya musu.
Kuma naga ai turawa ne kawai suke rungume-rungume da kiss, mu wannan ba ɗabi'ar mu ba ce amma yake gaya musu, wallahi makarantar nan ɓata tarbiyya ake yi".
"DANƘARI!!"
GODIYA GA TARIN MASOYA MASU BIBIYAR LITTAFIN ƘANWAR MAZA, COMMENT ƊIN KU NA SANYA NI NISHAƊI, KAR A MANTA DA SUBSCRIBING YOUTUBE CHANNEL ƊIN MU DOMIN SAMUN DAƊAƊAN LITATTFAN HAUSA NA SAURARO.
AYSHERCOOL
08081012143
[25/06, 4:11 pm] JAKADIYAR AREWA: ƘANWAR MAZA
        Â
Na Aisha Adam (Ayshercool)
MIKIYA WRITER'S ASSOCIATES
https://www.youtube.com/@CoolhausaNovels
Ku yi subscribing YouTube channel ɗin
@Cool Hausa Novels, domin samun daÉ—aÉ—an litattafan hausa na sauraro.
P7
Dafe goshi Yasir ya yi yana murzawa a hankali, ruma 'yar bala'i ce, ba zata tashi yi maka hansfree ba a cikin jama'a sai kowa ya hallara kamar mai sanar da wani abu mai muhimmanci, in da ya gode wa Allah da ya kasance, a makaranta ta ji ana koya musu, da bai san da wasu kalaman zai amfani wurin kare kansa ba.
Ita kuwa ta zaƙalƙale tana ta jawabi, babu wanda ya tanka mata, karo da idanun Umar ne ya sanya mata aya a jawaban da take kwarowa babu ƙaƙƙautawa.
"Zo nan" yayi maganar cikin bada umarni.
Kamar mara gaskiya haka ta tashi ta je gabansa ta durƙusa.
"Je ki É—auko mini jakarki ta makarantar boko da ta islamiyya"
"Dummm ta ji gabanta ya faÉ—i, har gara jakar islamiyyar ta ma, tun da ba a daÉ—e da sakata ba litattafan da mutuncinsu, amma ta makarantar boko dai kam sai dai Allah ya kyauta.
Jiki babu ƙwari ta je ta kwaso jakunkunan, ta zo gabansa ta ajiye su.
Ya kalli jakarta ta makarantar boko, duk ta ci ubanta da jagwalgwalon biro, har da zanen 'yan aljanu a jiki da su ABCD a jikin jakar, sunan 'yan gidan nan kuwa babu wanda ba ta rubuta a jiki bs. Tun daga nan ya san cikin jakar ma ba za ayi abin arziki ba.
"Oyaa zazzage litattafan na gani"
Babu musu ta janyo jakar ta zazzage, Innalillahi wa Innalillahi raji'un, litattafan nan sun ga duniya, tamkar ɓera ya ci rage mata. Kaf litattafan babu bango a jikinsu, sun yi kaca-kaca, wasu ma nannaɗe su tayi, wasu ta ninka su biyu, a taƙaice kai ka ce bolar wani office ɗin ce. Sai uban fensura sun kai biyar a cikin jakar, ga su ulu da farar ƙasa da sauran goriba duk a ciki.
Umar ya kalli ruma, ya kalli bolar dake gabansa, dan ba zai ce litattafai ba.
"Yanzu wannan sharar ce litattafan karatun naki?" Tayi shiru ta sunkuyar da kai.
Ya sanya hannu ya É—au littafi É—aya yana dubawa, ba uwar da take yi a ciki, littafi É—aya sai ta yi duk subject É—in da ta ga dama a ciki.
A hankali ya cigaba da duba litattafan nata, ga class work da tarin assignment, wasu tayi ta ci zero wasu makin da take ci ma gwanin ban haushi, subject É—aya ya ga ta mayar da hankali tana yi yadda yakamata, kuma ba ta faÉ—uwa shine maths.
Yayi ajiyar zuciya ya É—aga kai ya kalleta ya ce "Ashe asarar kuÉ—in tara kawai ake a banza ko? A biya miki kuÉ—in makaranta idan zaki tafi sai an baki abin tafiya makaranta, amma ki je kina wannan jakancin, kalli wai wannan ne litattafan ki na karatu, kalli wannan wai 4\20 ki ka ci, ba zaki iya kawo abin da baki iya ba gida a koya miki, wasa da surutun banza faÉ—i ba a tambaye ki ba shi ki ka saka a gaba ko?"
Ta girgiza masa kai alamar a'a.
"Ƙarya na yi miki kenan? To bari ki ji na gaya miki, ina nan zan zuba ido a kan result ɗin da zaki kawo wannan karon, wallahi idan bai yi mini ba sai an miki repeating "
Ras! Gaban ruma ya faɗi "Na shiga uku, dan Allah ka yi haƙuri, zan daina surutun in dinga karatu".
"Kar ma ki yi, wallahi primary 1 zan saka a mayar da ke, ki cigaba da daƙiƙanci, kuma ina samun information a kan abin da ki ke a islamiyya, ke kin zama jan wuya zaman ajinku ma ba kya yi, ke kin sakawa kan ki ba zaki iya karatu ba ko? Oya buɗe Alqur'ani nuna mini a surar da ku ke"
Ai nan ma badan-badan tayi ta yi, domin kuwa ba ta san a ina suke É—in ba.
Carbi ya bata, ya biya mata aya biyu, ya ce tayi ta maimaitawa sai tayi ƙafa dubu.
Da haka yaya umar ya ƙwaci yasir, ta zauna ta dinga nanata karatu har barci ya fara ɗaukar ta, da ta fara bacci yake zuba mata carbi a ƙafa, ta tashi a gigice ta cigaba da karatun, da haka sai da ta haddace rabin shafi, bai ƙyaleta ta kwanta ba sai wurin ƙarfe ɗaya na dare, da kuka haka ta kai karatun nan, ya sa ta kwashe bolar litattafan ta ya sallame ta.
Washegari, har makarantar boko, yaya umar ya je ya iske ta, ya kai mata sababbin litattafai, ya sanya aka kirawo ta ofishin shugaban makaranta, nan ma ba abin da suke yi, sai wassafawa yaya Umar halin ta na rashin ji.
Ya bata litattafan, yayi mata kashedi tare da jadadda mata, idan har ta cigaba da daƙiƙanci, sai ya sa an yi mata repeating.
*********
Zaune take a kan makeken gadonta, É—akin cike da kayan alatu kai da gani ka sam mai É—akin 'yar gata ce.
Ta dunƙule wuri guda a kan gadon, idanunta sun yi jawurr alamar ta sha kuka.
Daga ita sai doguwar riga 'yar kanti, kanta babu É—an kwali, kallo É—aya zaka yi mata ka san tana cikin matsananciyar damuwa.
Turo ƙofar ɗakin aka yi, wata babbar mace ce ta shigo ɗakin, idonta sanye da farin gilashi, hannunta riƙe da tray da cup.
Cikin tausayawa ta kalli yarinyar, ta ɗan girgiza kai, ta ƙarasa ta ajiye trayn, ta rungumota tana faɗin "Haba Iman ɗina, shikenan rayuwa bawa ba zai jurewa ƙaddara ba? So ki ke ciwona nima ya tashi?"
Iman ta girgiza kai, hawaye na cika idanunta.
"To Meyasa zaki takura kan ki, haka Allah ya so dama, ai dama tun farko biyayya ce zaki yi mini, kuma Allah bai yi yiwuwar abun ba, amma ki yi haƙuri kin ji babyna"
Ta jinjina kai lokacin da take sake kwantar da kanta a jikin matar.
Ta ɗakko tea a kofa tana bawa Iman a baki, tana sha tana share hawaye, kai da gani ka san akwai tsantsar soyayya da ƙauna a tsakanin su. Ta gama bata tea a baki, ta dinga shafa gashin ta, tana yi mata nasiha.
**********
Mama ta mayar da hankali sosai a kan ibada, mutane na ta shirin zuwan watan ramadan, mama tana ta azumi ita da su yayyen ruma, amma ban da hajiya ruma da cin abincinta ne kawai ya dameta.
Yanzu haka ta cinye taliya, ba ta ƙoshi ba, ta kwaɗa garin kwaki ta zauna tana ci.
Yasir sai masifa yake mata, wai shegen ci ne da ita kamar akuyar ƙauye, ko saurarensa ba ta yi ba ta cigaba da tura abincinta.
Mama ta kalleta ta ce "Wai ke ruma, ko zuciya ba zaki yi ba, azumin nan da kowa yake yi na neman lada ko guda É—aya ki gwada ba?"
Ɗan ɓata fuska tayi ta ce "Mama ni sai Allah ya kaimu watan ramadan, idan na fara azumi tun yanzu, ai ramewa zan yi kan salla"
"Ke ta ramewa ki ke, dan ubanki ina nuna miki ibada amma ke ba kya so"
Shiru ta yiwa mama tana cigaba da danƙarar garin kwakinta, dan ba ta ji za ta iya wannan azumin ba, idan na du gari ya zo dai ta jarraba.
Bisa ga jajircewar yaya Umar, aka samu ruma take ɗan taɓuka abin arziki a makarantar islamiyya, shima ba wani sosai ba, dan sam ba ta bayar da hadda, tana iya ƙoƙarin ta ko ba duka ba, ta ɗan iya karatun da aka biya musu, saboda idan yaya umar ya titsiyeya ta ɗan samu abin karanta masa dan ya bari ta yi barci, idan kuwa ba baka ba ta san sauran.
Yau ana can ana sallar la'asar, ruma tana zaune tana shan mangwaron ta, tuni ta yi sallarta a cewarta ba za ta iya bin jam'in nan ba, tun tana tsayuwa sai jiri ya fara kwasarta ba za ayi a idar ba.
Ta gama shan mangwaronta, ta tafi wurin alwala wanke hannu.
A wurin alwalar akwai yaran da suma ba sa sallar, suke ta wasan su.
Babu tsammani, ruma ta ji an zuba mata bulala. Tamkar wadda ta fita hayyacinta, haka ta tashi a gigice, tana duba wanda yayi mata wannan É—anyen aiki haka.
Wani prefect ta hango, bayan ya zuba mata bulalar ya tafi kora sauran yaran da bulala.
Cikin kiɗimewa, ta ɗauki ƙatuwar buta guda ɗaya, ta bishi a guje tana ihu, ta dinga watsa masa ruwan. Ya waiwayo ya tsaya yana kallonta, ta ga hakan bai mata ba ta dinga ƙwala masa butar, daga ƙarshe ta durƙusa ta ɗibi ƙasa tana watsa masa tana kuka.