Sashe 27
Ƙanwar Maza Complete Hausa Novel · about 8 min read
****
Sati biyu kenan da fara zuwan ruma makarantar sakandare, kullum sai ta yi gugar kaya, wai kar ta je da ƙazanta kamar ba 'yar sakandare ba, amma idan ta tashi dawowa tamkar ta yi dambe da kura, kayan nan duƙun-duƙun haka take dawowa da su.
Haka kawai yau zuciyarta ta raya mata, ta bi ta hanyar gidan mai unguwa, kasancewar a hanyar makarantar da take gidan yake.
A layin gidan mai unguwar, ta ga manyan motoci a fake, da alama wani abun ake yi. Hankalinta na kan lambun da ta taɓa zuwa ta ɗebo mangwaro mai gadi ya ce mata ɓarauniya, dan haka ba ta tsaya jin me ake a layin gidan mai unguwar ba.
Sai dai ko da ta ƙarasa layin lambun, wasu manyan motoci ta tarar guda uku a ƙofar lambun.
Lelleƙawa ta shiga yi, ta na haɗiyar yawu, saboda yadda take iya hango cincirindon bishiyoyin mangwaro da yadda suka yi 'ya'ya, ban da sauran 'ya'yan itatuwa.
"Ke uban me ki ke yi a nan wurin?"
Da sauri ta waiwaya, ta ga waye yake yi mata tsawa haka.
Ɗan gidan mai unguwa ne dai, da ya taɓa kamata.
"Taɓ dama kana nan?"
"Eh ina nan, yau ma satar ki ka zo yi?"
Ta tsuke ɗan bakinta ta ce "Ba yayana ya ce kar ka sake ce mini ɓarauniya ba?"
"Oho miki dai, ai É—iba ki ka yi ba a baki ba"
"Eh amma ai dai ya biya"
Cikin hanzari ya ce "Wai me ma ki ke yi a nan wurin ne?"
Ruma ta ɗan riƙe haɓa ta ce "Hmmm, ashe haryanzu ka na nan, ba ka cigaba ba, ni gashi har na gama primary na shiga sakandare"
"Ke dalla ware, tun kan a haife ki na yi sakandare na gama, fitsararriya wai wani ban cigaba ba, ɓace ki bar nan wuri muna da baƙi"
Ta ɗan yi ƙasa da murya ta ce "Wai su waye suka zo, na ga ƙofar gidanku ma da mutane"
"Ban sani ba, ba zaki wuce ba sai na zane ki?"
"Dan Allah É—an uwanmu mangwaro zaka san mini, ka ga dai yau ba sata na yi ba ko?"
Dariya ya kwashe da ita ya ce "A ina na zama É—an uwanku?"
"Ai kai É—an uwanmu ne na Musulunci"
Girgiza kai ya yi, zai wuce ta ya shiga cikin lambun, amma ta biyo shi.
"Wai ke baki da hankali ne, na ce miki muna da manyan baƙi masu wurin ne suka zo"
Cikin ko in kula ta ce "To ni ina ruwana, koma suwaye ai mutane ne ba mala'iku ba, dan Allah in biyoka ka san mini, ni sai na je na tambayo mai unguwa ma, na san shi zai ce ka bani"
Ya ƙarewa ruma kallo tsaf, a rashin hankalinta, tsaf za ta aikata abin da ta faɗa, na zuwa tambayo mahaifinsa, gashi yana tare da baƙi, ya dubeta ya ce "Yanzu abin da za ayi, ki zauna ki jirani, bari baƙin su tafi sai na baki"
"To, bari na je na zauna, kuma idan baka fito ba, biyoka zan yi"
"Wallahi ki ka shigo, zane miki jikinki za su yi"
"Su waye wai?" Ta yi maganar tana sake leƙa lambun.
"Kin ga tsaya, bari na je na samo miki" ya ƙarasa maganar tare da shigewa cikin lambun.
Dandamalin wani gida ta samu, ta ajiye jakarta, ta É—ebi duwatsu ta hau 'yar carafke.
Tun 'yar carafken na ɗauke mata hankali, har ta gaji da jiran ɗan gidan mai unguwa. Ta zube duwatsun ta tashi, ta je ƙofar shiga lambun ta tsaya, ta ɗaga murya ta ce "Ka cika alƙawari, zan shigo fa" magana ta fara ji ƙasa-ƙasa na mutane, alamar za a fito, ba ta yi niyyar matsawa daga bakin ƙofar ba, sai da ta hango akuya na shirin watso mata litattafanta, ta ci, ta nufi wurin jakarta, ta ɗau jakar ta na zagin akuyar, har da kiranta mayya mayuwanciya kamar tana magana da mutum.
Tana waiwayo wa, taga mutanen sun fito, sai dai kusan duk sun yi rawani, sai mutum É—aya da suke takewa baya, shi kuma suit ce ma a jikinsa.
Da gudu ruma ta kwaso, ta tsaya daga baya ta ce "Laaa sarki ne wannan?" Jin 'yar shilar muryarta ya yi, tamkar busar wata 'yar sarewa a kunnensa, duk da akwai dandazon yara da suke wurin, galibi suna zuwa idan har ya zo, saboda ya kan basu kuÉ—i. Har ya É—an juyo, zai waiwayo ya ga wacece a cikin yaran, bai juyo gaba É—aya ba, dogon hancinsa kawai ta iya ganowa, ya É—auke kansa ya shige motar da aka buÉ—e masa.
"Sarki ka ganni, ka juyo ka kalleni, ko dai ba sarki bane ba, na ga sarki ba ya saka ƙananan kaya ai"
"Ke! Hattara yarinya 'yar talakawa, ba a yiwa takawa karan tsaye"
Shiru ta ɗan yi ta dube shi ta ce "'yar talakawa kuma, to wallahi gidanmu akwai abinci, mu ba talakawa bane ba, kuma ba gara ni ba ma, Idan mu ka je kallon hawa mandawari, mama ta ce mini masu irin kayanka bayi ne, sayar da su ake yi zamanin baya a karɓi kuɗi"
Kowa waiwayowa ya yi yana kallon ruma, ya yin da dogarin ya zabura ya yo kan ruma, aikuwa ta kwasa da gudu ta tayar da uwar ƙura, shi kuma ya bita yana a tare ta.
Da ƙyar ruma ta kai gida afujajan, ta na ta haki kamar numfashinta zai ɗauke, ta shige ɗakin mama ta ƙule ta na ta sauke numfashi.
Mama ta biyo ta É—akin ta na faÉ—in "Ke!ke ruma ke da waye haka? Yanzun ma tsokanar ki ka yo ko? Tun yashe aka tashi 'yan makarantar ku, amma Allah bai nufe ki da shigowa ba sai yanzu ko? Ba zaki fito ba ina yi miki magana?"
Sumi-sumi ta fito, tana waige-waige sannan ta mayar da idonta kan mama.
"Daga ina ki ke?"
Ruma ta ɗan ɓata fuska ta ce "Mama ba ko ina fa"
"Zaki gaya mini ko na bari sai ya shigo?" Cikin kiÉ—ima ruma ta ce "A'a, dan Allah kar ki yi mini haka, wallahi kallon sarki na tsaya, a lambun mai unguwa, shi ne wani bawa ya ce mini 'yar talakawa, shi ne" sai kuma ta yi shiru.
"Shi ne me?"
"Cewa na yi, ai gara ni ba baiwa ba ce, shi fa kayan bayi ne a jikinsa, wanda ki ka gaya mini É—in nan ranar da muka je cikin gari kallon hawa, shi ne ya biyo ni da gudu"
Tafa hannu mama ta shiga yi tana faÉ—in "Innalillahi wa Innalillahi raji'un, dama can na aike ki, na ce idan an tashi ki dinga zuwa wani wur?" Ta girgiza kai.
"Saboda tsabar rashin kunya da rashin hankali, ki ka tsaya kina cewa babban mutum bawa, daga yi miki bayani ranar, ke ba zaki taɓa hankali ba ko? Ina ma ya kama ki ya yi miki dukan tsiya, na gaji da halinki ruma, ki na girma ki na sake shiga dawa, gaba ɗaya babu alamar hankali balle nutsuwa a tare da ke. Ki je ki cigaba da abin da Allah ya nufe ki da yi, Allah ya gani na yi iya yi na, ban yi miki irin wannan tarbiyyar ba Allah ya shiryeki"
Ruma ta yi shiru, tana sunkuyar da kai kamar gaske.
A ɓangaren karatu, an samu sassauci daga halin ruma, kullum Usman ya na ba ta ƙwarin gwiwa, a kan kar abin da ya bata tsoro, duk wani abu da wani zai yi, ita ma za ta iya.
A makarantar islamiyya kuwa, tun da malam Habibu ya taɓa hannunta garin karɓar bulala ta daina bin sa, sai dai yau ta zauna a ajinsu, gobe ka ganta a wani ajin, ɗaukar magana kuwa ba ta fasa ba. Dan saboda tsaurin ido, har manyan 'yan matan nan haka take zagewa ta yi musu rashin kunya, ba abin da ya yi mata zafi. Kuma ku san ko yaushe ta na cikinsu, ba ta yawo da sa'aninta.
****
"Allah ya taimake ki Hajjaju Mummy"
Murmushi ta yi cikin isa da izza ta ce "Abin ƙauna, ka yi breakfast ɗin ne?"
"Eh, na yi" ya yi maganar ya na zama a kusa da ita.
Ta saka hannu ta shafi sumar kansa ta ce "Mahmud, ya kamata a rage sumar nan"
Yayi murmushi ya ce "Haba Mummy, wannan sumar yadda ki ka ganta ki bar ta kawai"
"Hmm to ai shikenan, ya shirye shiryen komawa school?"
"Alhamdilillah, ina nan ina yi, very soon zan koma"
Fauziyya ce ta fito falon riƙe kofin shayi, ta kalli Mahmud ta ce "Yaya Mahmud, barka da safiya"
"Yauwwa, ina Ruky, ban ganta ba?"
Ta nemi wuri ta zauna ta ce "Ba ta tash ba, bacci take yi" ya kalli agogon hannunsa ya ce "By this time?"
Mummy ta ce "Ka san ta na karatun dare, dole ta yi bacci da safe"
Ya jinjina kai ya ce "Haka ne".
"Amm Yaya Mahmud, takawa ya dawo fa, yakamata ku haÉ—u kan ka koma, kun daÉ—e baku haÉ—u ba" tsuke fuska ya yi, ya kalli Fauziyya ya ce "Yaushe ki ka fara tsara mini abin da zan yi a rayuwata? Ubana ne shi da lallai sai na ganshi? Na gan shi jiya mana so what?"
Mummy ce ta katse hirar, ganin Mahmud har ya ɗau zafi ta ce "Is ok, ya isa haka, ku dai idan ya shigo ku je ku yi masa sannu da zuwa, bana son ƙananun maganganu irin na gidan nan".