← Book details Ƙanwar Maza Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 29 OF 47

Sashe 29

Ƙanwar Maza Complete Hausa Novel · about 8 min read

Samha ta gyara zama, ta na yiwa Adam wani irin shu'umin kallo, ta É—an murmusa sannan ta ce "Takawa, ni fa kwance jaka na zo yi, daga zuwa wurin su Fauziyy, na ji suna cewa za su shigo yi maka sannu da zuwa, na ce bari na biyo su in yi sannu da zuwa, kuma a bani tawa tsarabar"
A hankali ya É—ago idonsa, ya kalli Samha, ya É—an yi murmushi tare da girgiza kai amma bai ce komai ba.

Jabir ya dubi Iman ya ce "Iman, duk kin maƙalƙale mana shi, kamar ke kaɗai ki ka yi kewarsa, ki barmu mu ma mu gana da shi sosai mana" yayi maganar da sigar wasa.

Noƙe kafaɗa ta yi kamar ƙaramar yarinya, sai dai suna haɗa ido da Samha, samhan ta sake yi mata wani mugun kallo, da ya tilasta mata sunkuyar da kai.

"Jama'a ya shirin bikin Jamilu Turaki, Takawa akwai kilisa fa ranar Juma'a"

Adam ya girgiza kai ya ce"Kai, ƙyaleni da wata kilisa, duk na gaji, ni ban so ku ka san na dawo ba ma, ina buƙatar hutu sosai "

"Amma ba dai ka na nufin, ba zaka yi hawan ba, Jamil É—in guda?"

"Sai na yi tunani tukuna, idan ina da time"

Jabir ya ce"Ba ruwana, kai da shi"

Tsarguwa da rashin sukunin da idanun Samha suka sanya Iman ne ya sanya ta miƙe ta ce "Ni dai sai an jimanku, zan je na huta"

Samha ma ta miƙe ta ce "Mu je, ina son na gaida Ammi kan na tafi " jikin Iman ya yi sanyi, dan ta san akwai wani abu a ran Samha data ce za ta bita ta gaida Ammi.

Suna shiga ƙofar da zata sada su da sashin Ammi, Samha ta riƙo hannun Iman, ta tsayar da ita suna fuskanta juna.

Cikin raunaniyyar muryarta kamar mai shirin yin kuka Iman ta ce "Me na yi miki?"

Samha ta ƙarewa Iman kallo, sannan ta ce "Wai wace irin yarinya ce ke, kin manta kashedin da na yi miki ko sai na sake nanata miki?"

Iman ta ɗan ɓata fuska, ta aro jarumta ta ɓoye tsoron ta ta ce "Anty Samha, ni babu komai a tsakanina da takawa, ki yarda da ni mana, ina jin sa kamar wanda muka fito daga ciki ɗaya, ni ba zan iya aurensa ba"

Samha ta ce "Ƙarya ki ke yi, ba wani ki na jin sa kamar wanda ku ka kwanta ciki ɗaya, ai ba ki da kimar da zaki kwanta mahaifa ɗaya da Adam, ko kin manta wacece ke?"

Iman ta girgiza kai ta ce "Ban manta ba, 'yar karere ce ni, wadda ba ta da gado a gidan Galadima, wadda aka taimakawa aka riƙe, ina sane ba sai kin tuna mini ba".

Samha ta yi wani murmushi sannan ya kuma duban Iman ta ce "Ƙwarai kuwa kina sane, ban da Ammi ta nace da a cikin barorin gidan nan ya dace ki tashi ba 'yan gida ba, dan haka ki kiyayi shiga gonata"

"Amma ta yaya, a tare muka tashi da takawa, ta yaya za ki ce sai na nesanta da shi?"

Ta É—age kafaÉ—a ta ce "Wannan matsalar ki ce, ba tawa ba, dan na ga alamar tun da ba ki samu wancan ba, wannan zaki hara ki shiga hankalinki".

Iman ta girgiza kai ta ce "Ni babu abin da ki ke tunani tsakanina da takawa, amma ke ma Anty Samha bana tunanin zaki samu abin da ki ke so, akwai katangar ƙarfe a gabanki, kuma kin san takawa kin san halin sa sarai, ki bi a sannu" daga haka tayi gaba ta bar Samha a tsaye.

*****
Kamar yadda ruma ta yi alwashi, haka ta yi, ta je ajinsu ta zana wata shirgegiyar mata a kan allo, ta yi labelling ɗin ta. Gefe kuma ta zana ƙarama wadda ba ta kai matar ba, ta yi labelling ta rubuta Asiya shu'aibu.
'yan ajin suka dinga tuntsira dariya, saboda yadda zanen ya yi.
Ita kuwa Asiya ba ta san me aka yi ba, sai dai tana shigowa ta ga 'yan aji suna kallonta suna dariya.
Saroro ta yi, tana son gane me suke yiwa dariya, ba ta kula ba ta je ta zauna, sai dai ta na zaman idonta ya sauka a kan allon, ta ga ta'asar da ruma ta yi.
A firgice ta tashi tsaye, tana zazzare ido "Uban waye ya yi mini wannan rashin mutuncin"

Ruma ta miƙe ta ce "I am madam"

"Saboda tsabar kin raina wa kan ki hankali, kina nufin wannan babata ki ka zana?"

"An zanata É—in, ni ba cewa ki ka yi babata tsohuwa ce ba, ashe ma babata ta fi taki kyau"

Kan ruma ta farga, Asiya ta diro gaban ruma ta shaƙe ruma da hijjabinta. Kan ruma ta farga Asiya ta rufeta da duka, ta kaita ƙasa saboda ta rufe mata fuska da hijjabi. Kan ruma tayi wani yinƙuri, Asiya tayi mata duka.
Da ƙyar aka kirawo wani malami, ya janye Asiya daga kan ruma.

Malamin ya tasa su a gaba zuwa ofishin malamai, dan hukunta su, ruma ta shafa bakinta ta ji jini, tun da take a rayuwarta ko da za ta yi dambe a fitar mata da jini, to tabbas a duba wanda suka yi damben ta lallasa shi shi ma.
Gaba ɗaya Wani irin baƙin ciki ya mamaye ruma, gaba ɗaya ta rasa abin da yake mata daɗi, tun da take ba a taɓa galaba a kanta ba sai yau.

Ko da aka je staff room ana mayar da yadda aka yi, ruma taƙi magana, sai idonta da ya yi jawur, aka yo caaa a kan ruma, malamai suka din ga yi mata faɗa a kan bata kyauta ba zana babar Asiya da ta yi, suna kiranta mara ɗa'a.
Haryanzu malaman basu san wacece ruma ba, dan tun da Allah ya sanya ta zo makarantar ba ta taɓa gwada musu halinta ba.
Aka ce sai ruma ta bawa Asiya haƙuri, sannan za ta yi wankin banɗaki na sati guda, ita kuma Asiya zata yi sharar aji na kwana uku, saboda ɗaukar mataki da ta yi suka yi dambe da ruma.
Juyin duniya ruma ta yi magana taƙi, ƙememe taƙi bayar da haƙuri, dan haka aka sakata Kneel down har aka tashi a rana.
Babu abin da take tunani sai abin da za ta yiwa Asiya ta huce daga wannan baƙin cikin.

Ko da aka kaɗa ƙararrawa, ruma ba ta jira malaman su sallameta ba, ta tashi ta tafi aji ta ɗauko jakarta, Asiya ta din ga yi mata dariya har da gwalo. Wata nutsuwa ce ta shigi ruma a lokacin, dan a lokacin ji take da da wani abin dukan a kusa da ita, to tabbas sai ta illata Asiya.
Ta É—au jakarta ta fice, har ta je gida kamar zararriya jikinta a sanyaye.

Tun da mama ta ga ruma ta shigo babu ko sallama, ga uniform ɗin ruma a duƙunƙune ga busashshen jini a gefen bakin ta, ta san yau ta yi halin na dambe, ga takalminta da jakarta a hannu ta shigo da su, gwiwar wandonta ta yi kaca-kaca da ƙasa.
Ta zubar da su a tsakar gida ta shige É—akin mama kawai ta nemi wuri ta kwanta.
Ba ta tashi ba sai bayan azahar, ta tashi ta yi wanka, ta yi alwala ta yi sallar azahar, ta kuma neman wuri ta zauna a tsakar gida.

"Mutuniyar, wai ya aka yi ne? Zo ki sayo mana kifi mu ci Abinci, tun da na dawo nake cigiyarki" yayi maganar yana leƙa fuskarta.
Maimakon ta amsa masa kawai ya ga hawaye a fuskarta.

"Ke, menene mama ce?"

"Yaya Usy"

"Na'am rumaisa"

"Ni za a daka a hana kuka? Zuciyata zata fashe" tayi maganar tana sake fashewa da kuka.

Rarrashinta ya shiga yi, yadda ya ga tana neman ta shiÉ—e, idanunta duk suka yi ja.
Ya din ga lallaɓata ta gaya masa abin da ya faru.

Mama da take jin su ta ce "Allah ya ƙara miki, Allah ya sa yau da ki ka samu wadda ta zane ki, ba zaki sake dambe ba, dama ban da iskanci meye na zana uwar wani, idan ke aka zana taki uwar zaki ji daɗi?"

"Mama cewa fa ta yi babata tsohuwa"

"To sai me? Tsufa ai arziki ne, ruma ita duniya 'yar siyasa ce, ba komai ƙarfi yake baka ba, amma kin kasa gane hakan"

Wani irin kallo take yi wa mama, wato ita mama ko a jikinta kenan.

Usman ya kawar da fuskar ruma daga kallon mama. Abu ne mawuyaci ruma ta yi fushi, ko an ɓata mata rai sai dai ta yi kuka, idan ta gama kuma shikenan ya wuce sai a shirya, amma yadda idanunta suka yi yau ya tabattar masa da ta kai maƙura a ɓacin rai, ba a taɓa defeating ɗin ta ba sai yau. Irin zuciyar mai sunan baba ce da ita, idan rai ya ɓaci silently suke fushi, sai dai suna shiga mawuyacin hali, har gara shi Umar yana shouting wasu lokutan, amma ruma gaba ɗaya kasa komai take idan tana cikin matsanancin ɓacin rai. Wata irin ajiyar zuciya kawai take yi.

"Yaya ni raguwa ce ko? Aka zageni, a kan gaskiyata kuma aka hukunta ni, ni ko?"

Usman ya yi ƙasa da muryarsa ya ce "Ke ba raguwa ba ce, kowa shaida ne, kamar yadda nake gaya miki, ki fuskanci duk wani abin da yake baki tsoro, gaba da gaba na tsaya miki"

Ta ɗaga kai ta kalli Usman, ya jinjina mata kai alamar ƙwarin gwiwa, ta jinjina kai ta mayar da kai ta kwanta a jikinsa, tana cigaba da ajiyar zuciya.

Duk wanda ya shigo ya ga ruma a haka, sai ya tambayi ba'asin meyafaru, ko ba ta da lafiya ne?
Mama ta ce "Ina fa, lafiyarta ƙalau, yau bori ne ya kar boka, ta tsokano wadda ta fi ƙarfinta, aka naɗa mata duka, shi ne take nema ta suma ki cigaba kar ki fasa halinki"

Aliyu ya tsaya a kan ruma ya ce "Ke, ki na wani sokwancin ki ka yadda aka dake ki har ki ke wa mutane kuka?" Ruma ta yi shiru ba ta amsa ba.
Chapter 29 · 0% Book details