← Book details Ƙanwar Maza Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 13 OF 47

Sashe 13

Ƙanwar Maza Complete Hausa Novel · about 8 min read

"A'a, to ni wa na gani a wurin, kuma ma naga ai bishiyar ta Allah ce, Allah ne ya fito da ita, kuma sai ace sai an tambayi wani sannan za a ɗau abin da Allah ne ya fito da shi, kai iskar da ka ke shaƙa wa ka tambaya ka ke shaƙarta?" Saroro ya bi ruma da kallo, wata 'yar cukul da ita sai shegen surutun tsiya.

"Zaki yi bayani, sai na kai ki gaban mai unguwa"

"DaÉ—inta shi mai unguwar ba shi da wutar da zai sakani, kuma duk in da za a je ai bishiyar Allah ce, kuma ka sakar mini hijjabi dan ni ba 'yar iska bace ba.
Bai ko saurareta ba, ya figi hijjabinta ya fara janta.
"Ka dai na ja na haka kamar wata akuya, ba ƙaramin aikina bane na cire maka hijjabin nan na ƙara gaba.

Mama sai kallon agogo take yi, tana kallon hanyar shigowa, amma babu ruma babu alamunta.
Tsakar gida ta fito tana kiran Usman, kasancewar shikaÉ—ai ne a gidan, ya dawo da wuri bashi da lectures.
"Ka ga haryanzu yarinyar nan shiru ba ta dawo ba"

Usman Ya ce "wataƙila tana can tana rashin hankali a titi da ƙawayenta, amma maybe ki ganta yanzu".

"A'a zunnuraini, shi biyu da rabi fa take dawowa amma kalli yanzu ƙarfe ɗaya da rabi, hankalina ya kasa kwanciya"
Ya ɗan yi shiru sannan ya ce "Kuma fa kamar ma ga 'yan makarantar su lokacin da nake hanyar dawowa, amma bari na je makarantar ta su" yana rufe bakinsa, suka ji ana ƙwala sallama a waje.

Usman ya amsa, ya nufi ƙofar gidan, aikuwa yana zuwa ya tarar da an riƙo ruma, tana rungume da jakar makarantar ta, sai kumbura baki take, tana cika tana batsewa.

Kallon matashin saurayin yayi, ya ce "Bawan Allah lafiya, ya zaka riƙo yarinya haka kamar ka riƙo ɓarauniya?"

Matashin ya ce "To kusan hakan ne, karɓi jakarta ka duba ka gani"

"Ka saketa mana" yayi maganar a fusace yana fincike hannun matashin daga hijjabinta.
"Me tayi maka haka?".

"Nan matashin ya kwashe komai ya gayawa Usman"

"Wallahi ni ba ɓarauniya bace ba, tun da ta ƙofar wurin na shiga kuma ban ga kowa ba, ai ba haurawa na yi ba"

Usman ya fizgi jakar ruma, ya buÉ—e ya ga mangwaro ya kai takwas a ciki manya, nunannu da É—anyu, sai goba guda huÉ—u.

Ya kalli ruma, sannan ya kalli matashin ya ce "Yanzu kai a kan wannan zaka danƙota ka keto layi da ita haka? Ka taɓa kamata ta shiga ta ɗaukar muku abu ne?"

Matashin ya ce "Ban taɓa kamata ba, amma ana haura mana, ayi sata"

"To kuma sai aka ce maka nice nake yi, ni wallahi ban taɓa shiga ba sai yau".

Usman ya zura hannu a aljihunsa, ya ɗauko dubu ɗaya, ya miƙawa matashin ya ce "Na san dai abin da ta ɗauka, bai kai na hakan ba, gashi nan na biya, kuma kar ka sake kiranta ɓarauniya Please, ba halinta bane ba ba ta taɓa yi ba, dan ka ci sa'a da na biyewa zuciya sai na kifar da kai, saboda yadda ka riƙo mata hijjabi, ka keto unguwa da ita, saboda ɗanyen mangwaro"
Yana gama maganar, ya ingiza ƙeyar ruma zuwa cikin gidan, suna shiga gidan ya danƙota ya ƙwace jakarta, ya durƙusar da ita ya ce "Oya tsallen kwaɗo maza"

Waiwayo ruma tayi, ta kalleshi cikin mamaki, amma taga babu alamar wasa a tare da shi, cikin tsawa ya kuma cewa tayi tsallen kwaÉ—o.

Mama ta fito tana faÉ—in "Lafiya, me aka ce tayi, sallamar da ake kenan?"

Usman ya ce "Ƙyaleni da ita mama" nan ruma ta kama tsallen kwanɗo.

Duk yadda mama tayi a kan Usman ya gaya mata me aka ce ruman tayi, amma yaƙi, sai dai ruma ta ci ƙwal ubanta, dan ko miƙewa kasa wa tayi.

Duk yadda mama ta kaÉ—a ta raya, amma bai gaya mata ba, kuma babu wanda ya gayawa abin da ta aikata.

****
Islamiyyar su ruma, sanya mata ido suka yi, dan ba ta iya karatu balle kawo hadda, ko karatun aka zo sai dai a tsallake ta, dan ba iyawa take yi ba.
Malamin ajin ko sabgarta ba ya shiga, tun daga ranar da ya dake ta ta ce ita sikila ce. Yau dai ya kasa jurewa yace mata "Wai ke ba kya jin haushi yadda 'yan ajin ku suke karatu, amma ke ba kya iya wa?"

"To malam karatun yayi mini yawa, yaya zan yi?"

"Su sauran da suke iyawa, da me suka fiki?"

Ita kanta ruma gaba É—aya malamin bai yi mata ba, dan bai fi sa'an Abdallah ba, shi ma É—alibi ne a makarantar, amma ya dinga takura mata.
Tayi masa banza tana kallon wani gefen daban.
"Magana fa nake miki?"

"To ya sayyadi me zance maka? Ni wallahi ba zan iya karatun nan ba, ni fa tun farko ba son makarantar nake ba, kawai dan yayana ya kawo ni ne".

Ita gaba É—aya kanta tsaye take faÉ—ar magana, ko tayi maka daÉ—i ko kar ta yi maka kai ta shafa.

Tsaki yayi ya ce "Daƙiƙiya mara zuciya"

Ɗagowa tayi ta kalleshi ta ce "Malam wannan ba halin musulmi nagari bane ba, ba koyarwar addinin Musulunci bace. Saboda bana iya karatu dama duk ka bi ka tsaneni Allah ya buɗa mini ƙwaƙwalwata nima. Zuwa zan yi a canza mini aji" ta tashi ta ɗau jakarta ta bar ajin, ba tare da ko izini ta nema ba.

Ta bala'in jin haushin cin mutuncin da ya yi mata a gaban 'yan ajinsu, wai daƙiƙiya mara zuciya.
Ofishin shugaban makarantar ta nufa, dan ta sanar masa a canza mata aji, malaminsu ya tsaneta, amma ta tarar baya nan.
Azuzuwa ta shiga dubawa, aikuwa ta ganshi a ajin su Yasir yana yi musu karatu.

A ƙofar ajin ta tsaya ta ce "Headmaster ina wuni?"

Ya É—ago ya kalleta, ba wanda yake ce masa wani head master sai yau a bakinta.

Ya ce "Lafiya lau"

"Malam zuwa na yi ka canza mini aji, ni na gajj da ajin nan, malamin ya tsaneni"

Dariya 'yan ajin suka fara yi, Yasir kuwa ya sunkuyar da kai ƙasa.

Yayi murmushi ya ce "To shikenan, ki je ki jirani, idan an tashi sai mu yi magana"

"To, Yasir in jiraka idan an tashi mu tafi tare?"

Wani mugun kallo ya yi mata ya ce "Da tare muka zo"

MurguÉ—a baki tayi, ta koma kan barandar ajin ta zauna, shiru-shiru ta gaji basu tashi ba, ta kaÉ—a kai tayi tafiyarta gida.

A hanya ta biyo ta filin ball ɗin su Yaya Aliyu, maza sun yi cincirindo, ana kallon ball, ta tsaya tana leƙawa ko zata hango yaya Aliyu.
Kutsawa ta dinga yi, sai gata ita É—aya a cikin maza.

"Ruma me ki ke yi a nan?" Ta É—aga kai ta kalli mai maganar, abokin Aliyu ne.

"Yaya Aliyu nake nema"

"To ai yana cikin fili, ball yake"

"To ai na sani, kallonsa zan yi"

Ya jinjina kai ya ce "To ai shikenan"

Kamar daga sama ya ji ana kiran sunansa, da 'yar siriryar muryarta.

Duk da yadda ya taso ball É—in a gaba, amma sai da ya tsaya ya waiwaya.
Ruma ya hango a gaban garada, tana É—ago masa hannu.

Waro ido ya yi, ya nufi in da ruma take.
Coach É—in su Aliyu ya fara masifa, dan ajiye ball É—in da ya yi, ya waiwaya aka ci su É—aya.

"Ke me ki ke yi a nan?"

"Wucewa zan na ce bari na zo na ganka"
Ya dafe kai ya ce "Innalillahi wa Innalillahi raji'un, ki wuce ki tafi gida"

"Dan Allah ka bari na gani"

Hankalinsa na kan ruma, coach kuma na ta masifa.
"Kai dalla wacece wannan, ku koreta daga wurin nan".
"Wallahi ba inda zani, ai wurin yayana na zo".
Aliyu ya kalli abokinsa ya cewa "Aminu, dan Allah jire mini yarinyar nan" ya koma cikin filin yana waiwayenta.

Aminu ya bata wata ƙatuwar jaka ta zauna a kai, ita kaɗai mace a cikin maza.

Yana ball É—in amma hankalinsa yana kanta.

Ta dinga yi masa tafi tana bashi ƙwarin gwiwa, kusan duk hankali ya dawo kanta, gaba ɗaya ta bawa wasu dariya a wurin.

Da yaya Aliyu ya ci ball kuwa, ta dinga tsalle tana murna, ya ci ball biyu.

Da aka tashi har hoto aka yi mata, ita da Aliyu ta riƙe kofin da suka ci, kasancewar ball ce ta cikin unguwa.

Ba a tashi daga ball É—in ba, sai ana kiran sallar magariba, mama tana can ta sa an yi sahu ya kai uku a makarantar su, ana nemanta.

Suna tafe a hanya tana yabawa yaya Aliyu, abokansa sai tsokanarsa suke yi a kan ruma.

"Yaya Aliyu, akwai wani wanda kuna ball ɗin, ya dakar maka ƙafa, na ji haushi idan na ganshi sai na buga masa dutse wallahi".

"Ni ban saki ba, kuma baki ga an bamu pk ba da ref ya gani"

"Oho ni na san wani pk, amma da ka tsaya ja masa duka ka rama, daga wasa sai cin zali"

Haka suka ƙarasa gida, mama na tsaye da carbi a tsakar gida, tana tunanin ta ina ruma zata dawo.

Sai gata ita da Aliyu, yana riƙe da hannunta.

Mama ta kalleta ta ce "Ke daga ina?"
Sai a yanzu ta tuna daga islamiyya ko gida ba ta zo ba, ta kalli ya ya Aliyu ya kalleta.

"A ina ka ganta?" Mama ta tambaye shi tana kallon ruma.

Aliyu ya ce "wallahi mama nima kawai ganinta na yi a filinmu, ban san ina za ta tsaya ba idan na ce ta taho, shi ya sanya na ce ta tsaya"

"Kina mace uban me ya kai ki filin ball?" Huzaifa yayi maganar a ƙufiule, dan takalminsa har tsinkewa ya yi saboda nemanta.

Hararsa tayi ta sake noƙewa a jikin Aliyu.

Duka Huzaifa ya kawo mata, Aliyu ya tare ta, ya ce laifina ne duk Allah ya baku haƙuri.

Mama ta fara tunanin anya ba zata kai ruma wurin malaman ruƙiyya ba, abin na ta ya fara bawa mama tsoro sosai da sosai.
Chapter 13 · 0% Book details