Sashe 22
Ƙanwar Maza Complete Hausa Novel · about 8 min read
Gwaggo ta jinjina kai ta ce "Ikon Allah"
"Gwaggo wai ina wannan 'yar ta ki, mai kamar ni É—in nan?"
Jin ruma ta tambayi 'yar autarta ya sanya Gwaggo yin murmushi ta ce "Au Lawisa tana nan ƙalau, ta na ta a gaishe ki, ita ana biki sun tafi da tuni tare zamu zo"
Ruma ta yi dariya ta ce "Wai Lawisa, ai har gara nawa sunan ma da nata, wata lawisa kamar za ace lawashi, ta fini girma yanzu?"
"A'a zaku yi tsayi É—aya da ita"
Ruma ta yi murmushi tana kaɗa ƙafa.
Abubakar ya ce "Ruma ɗaga mata ƙafa mana"
"A'a ƙyaleta, ai haryanzu yarinya ce, Allah dai ya kai ni auranku ke da Lawisa"
Ruma ta ce "Amin, ki yi mini Addu'a, Allah ya sa na yi tsawo na isa aure, kuma Allah ya sa na auri kyakykyawa mai kuÉ—i sosai"
Mama ta riƙe haɓa ta ce "Ruma, ƙanƙanuwarki da ke, har kin san wani miji mai kyau mai kuɗi?".
Gwaggo ta ce wa mama "Wai ke ina ruwanki da mu ne, muna hira kina saka mana baki" ta mayar da hankali kan ruma ta ce "Amin 'yar albarka, Allah ya kai ki in da zaki huta, mu ci mu sha mu yi wadaƙa".
"Amin, kuma Allah ya sa na auri me kyau".
Aliyu ya ce"Da wannan shegen hancin naki kamar na aladae zaki auri me kyau?"
Gwaggo ta ce "Ƙarya ka ke dan ubanka, wallahi kamar ta ɗaya da babanku, kuma hanci ne da shi har baka, in Allah ya yarda sirikina kyakykyawa ne kuma mai abin hannu, tun da 'ya ta ba daga nan ba"
"Gwaggo kin san wa nake so na aura?"
"A'a sai kin faÉ—a"
"Kina kallon wrestling?"
Gwaggo ta ce"A'a ni ban san shi ba"
'To ball fa?"
"Ni ina zan ga wannan shirmen"
Ruma ta ce "Da kina kallo, da na gaya miki wanda zan aura a cikin su".
Cikin son katse surutun da ruma ke yi ba kunya ba tsoro mama ta ce "Ruma tashi ki canza kaya, zan aike ki" ruma ta miƙe daga cinyar Gwaggo ta tafi sauya uniform.
Tun da Allah ya sa Gwaggo ta zo gidan nan, ruma taɓara ta ƙaru, don ko me ruma za ta yi ba zata bari a yi mata faɗa ba, gashi kullum cikin faɗa take da mai sunan Baba, dan kome za ta yi idan ruma tayi laifi hukunta ta yake yi.
"Wannan yaro da fuska kamar bajimin sa, ba ka da imani, wannan 'yar tatsitsiyar yarinyar guda nawa take, da zaka dinga azabtar da ita wallahi Hauwa wannan É—an naki mugu ne"
Gaba É—aya ruma da Gwaggo suka gallabi gidan nan, ruma kuwa aka samu tikitin rashin ji dan ma tana tsoron mai sunan Baba.
Yau Malam Habibu yana babban aji, ruma tana tare da shi, yayi musu ƙari, tana ta wasanninta da ciye-ciye, sai da ya kammala yana amsa tambayoyi sannan ruma ta ce "Malam ka ce idan mace tayi mafarkin namiji sai ta yi wanka zata yi salla, to ni kuma kullum sai na yi mafarkin yayyena, Kuma ni sai zan tafi makaranta nake wanka watarana kuma mama ta ce bana fita tayi mini wanka, to yan.....
Kan ta ƙarasa 'yan ajin suka hau dariya, dan ba zaka taɓa cewa hankalinta na kan abin da yake koyarwa ba.
Malam Habibu ya ce " 'ya ta ta kaina, ai wankan da mama take yi miki ya wadatar, duk É—ayane"
Ta ce "Au ho, na gane"
Tana dawowa daga islamiyya ta turke Abubakar ta ce "Yaya Sadik yau ka san meyafaru a makarantar islamiyya ?"
Sadik ya ce "A'a"
"Ka san na canza aji a islamiyya, saboda malaminmu baya ƙaunata, Ajin su Yasir kuma ya ce idan na ƙara zuwar musu aji sai ya dakeni, sai na koma ajin malam Habibu gaba ɗaya ajin 'yan sauka"
Abubakar ya ce "To ban da abinki kin taɓa ganin an fara gini daga roofing, ai daga tushe ake farawa"
"Oho dai koma yane, wani karatu aka yi nake son na tambayeka, da zan tambayi malam Habibu na manta"
"To ina jin ki"
" 'yan ajin ne da su da wasu na ga wataran ba sa salla fa, ko su ƙi zuwa da Alqur'ani izifi sittin wai Haila suke yi. Na tambayesu sai suka ce mini wai ai mata ba kullum suke salla ba, idan ba su yi salla ba haila suke yi ko biƙi. Aikuwa nima na ƙi yin salla, wata prefect ta ce me yasa ba na salla nima na ce biƙi nake"
Gwaggo da ta idar da salla ta ce "Subhanallahi" jin maganar ruman kamar saukar aradu.
Ita kuwa ko a jikinta, ta cigaba "Shi ne ta ce dan ubana ni na isa in yi biƙi, na ce ba dai ubana ba sai dai na ta, kuma tun da nima biƙi nake ba zan salla ba, ashe wataran mata ba sa salla amma ni kullum mama sai ta ce sai na yi"
Abubakar ya ce"To, wannan zancenku ne ke da maman ita zata baki amsa".
Ruma ta ce "Mama....."
Mama ta katseta ta hanyar cewa "Rufe mini baki, kar ki sake ki yi mini shirme, kuma ki tashi ki yi sallar da ki ka ce baki yi ba dan ubanki"
"To mama ai idan ana biƙi ba a salla"
"Biƙin ubanki, ke kin san meye biƙin ne?"
"To meye biƙin?"
"Ba zaki tashi ki yi sallar ba, sai na zane ki da bulugarin nan?"
Ta kalli Gwaggo ta ce "To ke gaya mini"
Kamar wadda ta tambayi meye wani babban zunubi Gwaggo ta ce "A'a ni babu ruwana, ga uwarki nan ta baki amsa ni zaki tambaya wannan babban al'amari ba a bakina ba, 'ya'yan binki wayewar ku ta yi yawa".
"Ohh ni ruma, komai na yi laifi ne, ai shikenan"
Tun daga lokacin ba ta kuma kula kowa ba, ta koma tayi shiru wai ita ta ji haushi.
Har zuwa sallar magariba, ba ta sake kula kowa ba, Gwaggo ma ta gaji da yi mata hirar, amma Ruma taƙi saurarata.
Yaya Sadik ne yayi gyaran murya ya ce "Ruma, wai ni kuwa idan kin girma me ki ke son ki zama ne? Da na je taron PTA É—in ku an ce da kun shiga primary 6, za'a fara shirin common entrance, shi ne na ce idan kin shiga Sakandire me ki ke sha'awa Art zaki yi ko science?"
Ta kalle shi ta ce"Wai in din ga drawing?"
"Wane irin drawing kuma?"
"To ai ji na yi ka ce Art, Art ba drawing ba kenan?"
"A'a ba wannan ba"
"Ni dai kawai sana'ar da zan samu kuɗi nake so, ko kuma in zama 'yar sanda, in dinga tsayawa a titi ina bada hannu masu mota suna bani kuɗi, ko kuma a buɗe mini kanti, ko na zama mawaƙiya ko 'yar film!"
Ayshercool
08081012143
A TAIMAKA AYI SUBSCRIBING YOUTUBE CHANNEL ƊINA NA COOL HAUSA NOVELS, KO IN KOMA POSTING SAU ƊAYA A SATI 😒*
[11/07, 4:25 pm] JAKADIYAR AREWA: ƘANWAR MAZA
        Â
Na Aisha Adam (Ayshercool)
MIKIYA WRITER'S ASSOCIATES
https://www.youtube.com/@CoolhausaNovels
Ku yi subscribing YouTube channel ɗin
@Cool Hausa Novels, domin samun daÉ—aÉ—an litattafan hausa na sauraro.
P11
Girgiza kai kawai Abubakar ya yi, ya ja bakinsa ya tsuke.
"Yaya ya na ji kuma kayi shiru?"
"To ruma ba dole na yi shiru ba, kowa yana nemawa kansa mafita a rayuwa, amma ke in da ki ka dosa daban?"
"To wai me na faÉ—a ba dai-dai ba?"
"Yanzu ke tsakanin ki da Allah, kin taɓa ganin mace a titi tana bada hannu a ƙasar hausa?"
Ta ɗan yi shiru sannan ta girgiza masa kai ta ce "A'a, to mawaƙiya fa ko film?"
Abubakar ya ce "Ba kushe sana'ar wani zan yi ba, amma ki yi tunanin wani abun daban"
"To ba sai a buÉ—e mini kanti ba"
"Yanzu a unguwar nan gaya mini shagunan da ki ka ga mata ne a ciki suke sayar da abu?"
Ta yi farat ta ce "Ga maman Olu beyerabiya"
"To ke bayerabiya ce?"
"A'a amma dai....."
"Kin ga, ya isa haka, dama ni a kan career ki nake magana, tun da baki gane me nake nufi ba shikenan" ita sam ba ta ga aibun abin da ta ce tana so ba, dan haka ko a jikinta ta share.
Gwaggo ta fara shirin tafiya, su Yasir suna ta murna, dan dama duk ta ishe su da faÉ—a da azabar saka ido.
Shi kansa mai sunan Baba murna yake ta tattara ta tafi ta bar musu gida su huta, dan ta saka shi a gaba da yawa, dan ma Allah ya taimaki Abubakar bai fi sati ba ya koma makaranta.
Amma kullum cikin surutu takewa mama "Hauwwa wannan zagada zagadan yaran naki, duk sun isa aure amma kin tare su a gaba kina ado da su a gida, ga ƙauye can muna da mata burjik, amma dan mugunta kin tare su kin hana su motsi'
Mama ta ce "Haba Gwaggo, guda nawa yaran suke, haryanzu su Baba basu haɗa talatin ba fa, duk girman jiki ne, kuma kina ganin irin rayuwar da ake sai godiyar Allah, babu mai ƙwaƙwarar sana'a sai ƙarfin hali, idan suka ɗauko aure da yaya za su riƙe?"
"Ba wani nan, idan mutum yayi aure Allah zai warware, amma kallesu dan Allah tuma-tuman gwauraye ki na ado da su a gida, babu mai mata, kalli dai wannan zagaren, sai dai ya shigo fuska kamar bajimin sa, ya zo ya É—au abinci ya fita yana zazzare ido kamar wani zaki, ko fara'a ba ya yi, kai haka zaka yi wa matar ma idan an aureka?, ko da yake ma wace macence za ta auri mutum ba fara'a ba komai fuska kamar kunun kanwa ba rahama"
Lomar Abincinsa kawai yake kawai, ko motsi bai yi ba, balle ya nuna ya san da shi take, yana jin ta ya share ta.
Ruma kamar ta kwashe da dariya, jin an ce fuskar yaya Umar kamar kunun kanwa, amma sanin ruwa ba sa'an kwandon ba ne ya sanya ta ja bakinta ta tsuke.
"Umaru da kai fa nake" A hankali ya É—ago idanunsa ya yi mata wani irin kallo, ya mayar da kan sa ya cigaba da cin abinci.