← Book details Ƙanwar Maza Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 17 OF 47

Sashe 17

Ƙanwar Maza Complete Hausa Novel · about 8 min read

Dariya yaran suka kwashe da ita suna sake leƙa ƙafarta.
Cikin takaici, ta juya zata tafi, amma wata zaƙaƙurar yarinya, ta biyo ruma tana ɗage mata zani.
Mai jiran ƙiris ya samu a sarari, tuni ruma ta yi watsi da kwanuka, ta fara sana'ar ta ta dambe.
Kasancewar a ƙule take dama, ta rasa in da zata sauke fushinta, dan haka ta zage ta kama yarinyar nan ta dinga jibagarta kamar Allah ya aikota.
Suna cikin damben Allah ya bawa yarinyar sa'ar ketawa ruma hijjabi, hakan ya ƙara tunzura ruman, ta danne yarinyar tana duka.

"Wannan yarinya an yi jarababbiya, duk in da ta tsuguna sai dambe, sai ka ce annoba" cewar wani mai awo a gefe, da bai raba su ba sai zance.

ÆŠagowa ta yi cikin masifa ta ce "Wallahi ni ba annoba bace ba"

Ta duƙa ta cigaba da dambenta.  ji tayi an yi sama da ita, ta fara kokowar ƙwacewa tana kai duka.

"Zaki nutsu ko sai na kakkarya ki" yaya Aliyu ne ya tsare ta da ido.

"Dama abin da ta aiko ki kenan?" Ta yi shiru tare da sunkuyar da kai.

"wuce mu tafi, dage uwar faÉ—a"

Haka ta kwashi kwanukan, da yagaggen hijjabinta a hannu ya tasa ta a gaba, zuwa gida.

Mama na ganin ruma ta shigo tare da Aliyu, a yadda ta shigo kawai mama ta gane halin ta je ta gwada a waje.

"Damben ki ka je ki ka yi kenan ko, mara kintsi?"

Wage baki ruma tayi zata fara yiwa mama bayani, amma mama ta katseta ta ce "Ban tambayeki ba ruma, ki je ji yi tayi, bakin mutane kawai ya ishe ki"

Gefe ta koma ta zauna, tana jin yadda ba ta gamsu da dukan da ta yiwa Hauwwa ba, saboda dariyar da suka yi mata.

Yaya Umar ne ya fito daga ɗakin su, cikin wata dakakkiyar shadda dark blue, ya karya hula sai ƙamshi yake zubawa.
Tsuruu ruma ta yi da ido, tana jiran ya sauke mata masifa, tun da ya ji ance ta yi dambe.

Nufota ya yi, ita kuma ta ƙura masa ido ko ƙiftawa ba ta yi.

Ya kalleta ya ce "Na canza miki ne?"

Ta girgiza kai ta ce "A'a ka yi kyau ne"

Murmushi ya yi, ya miƙa mata leda ya ce "Je ki ka gwada wannan" da sauri ta tashi, ba tare da sanin meye a ciki ba ta karɓa ta shiga ɗaki.

Doguwar riga ce ta shadda kalar kayansa, da mayafi da sabon takalmi da yari da sarƙa.
Ko da ta saka ta fito ba ƙaramin kyau ta yi ba.

"Mama kin ganni, na yi kyau"

Aliyu ya ce "Saboda son kai, shine ku ka yi kaya iri É—aya babu ko labari"

Cikin tsananin farin ciki ta ce "Yaya Ussy, kalleni dan Allah na yi kyau?"

"Eh to, babu laifi sai ki ka zama kamar budurwa, duk da ƙwaila ce".

Cikin tsananin farin ciki, ta faÉ—a jikin yaya Umar tana murna "Yaya na gode sosai, Allah ya saka maka da alkhairi ya sa ka gama da duniya lafiya"

Ganin yadda take murna ya sanya shi yin murmushi na gefen baki ya ce "Allah ya sa ki daina rashin ji".

"Iyee, lallai mai sunan Baba, ni sai ka haɗani da atamfa kala uku, amma kai da ƙanwarka ka yi muku kaya iri ɗaya, wato an fi son ta a kaina" mama tayi maganar cikin sigar wasa.

Murmushi ya yi, dan ya san halin mama da barkwanci wasu lokutan.

Mama ta shiga ɗaki, ta fito da wata ƙatuwar leda, ta miƙawa ruma ta ce "Gashi nan, ba dan halinki ba, kayayakin da suka yi miki ne, na wannan sallar naƙi nuna miki dan in hora ki"

Rikicewa ruma tayi, dama suna yi mata ɗinke-ɗinke, amma sallar bana bata san sun yi mata ba, dan a ƙalla ta tashi da kaya ku san dozen, banda hijjabai da abun hannu da sauransu.

"Wayyo Allahna, dama kuna so na haka? Duk nawa ne wannan mama kin ga fa duk nawa ne"

Gaba daya suka kewaye ta suna murmushi, ganin yadda ta rikice tana murna.

Bin su ta dinga yi É—aya bayan É—aya tana yi musu godiya, tana zuwa kan Huzaifa ya wani maze ya ce 'Kar ki damu, wannan fa bakomai bane ba, idan har zaki dinga biyayya".

"Ba zan yi biyayyar ba, na san ma ba uwar da ka saya mini, duk gidan nan waye ya kai ka talauci da son banza?"

"Laaaa, ke fa ba a abin arziki da ke ko?"

"A'a yi haƙuri mama, shi ɗin ne zai ɓata mini rai, yanzu a cigaba da zuzzuba tuwon ina kaiwa, amma wallahi duk in da na san ba za a bani kuɗi ba, sai dai Yasir ko Huzaifa su kai"

Haka tayi ta rabon Abinci cikin annashuwa, gidan da aka bata kuÉ—i tayi ta murna, idan ba a baya ba tayi ta jin haushi.

********
Ba zata iya ƙayyade rabonta da gidan nan ba, dan haka ta ɗaga kai take ta na kallon sauye-sauyen da aka yi a gidan.
Ya ƙawatu, duk da ginin yana nan a yadda yake, amma an yi wa gidan gyara sosai.
Da haka ta ƙarasa cikin ƙaton falon da ke cikin gidan.

Hadimai ne ke ta kaiwa suna komowa a cikin tangamemen falon, suna aikace-aikace.

ÆŠaya daga cikin hadiman ce ta kalli Iman da fara'a ta ce "Maraba da zuwa".

Iman ta ce "Yauwwa sannunku da aiki, Ummma fa?".

"Tana cikin turaka, bari ayi miki iso"

Babu jimawa hadimar ta fito, ta kalli Iman ta ce "Bisimillah, ta ce ki shiga"

Bayan hadimar Iman ta bi, zuwa turakar Ummma.
Shigarsu ɗakin ke da wuya, gaban Iman ya faɗi, bisa tozali da mutanen da ba ta son ko haɗa hanya da su, ba dan jinin Ummma bane su, to tabbas da kai tsaye zata iya cewa mutanen da ba ta ƙauna.

FaÉ—aÉ—a murmushi Ummma tayi ta ce "Masha Allah, Iman dama talaka na ganinki?"

Murmushin yaƙe iman ta ƙaƙalo, ta durƙusa a kan gwiwoyinta tana gaida Ummma.

Cikin mutuntawa Ummma ta amaa mata, tare da tambayarta ya Ammi.

"Hajiya Iman, manya manyan 'ya'ya a gidan Galadima, ya kike ya school?" cewar wata matashiya da ke zaune a gefen Ummma.

Ko ba a gaya mata ba, ta san da biyu budurwar ta yi wannan maganar, ta dake ta ce "Lafiya lau Anty Soafy, an yi salla lafiya?"

"Hmm lafiya lau, irin wannan ado haka, Ummma wannan leshin kamar irin sa Khairiyya ta saka ranar kamunta ko?" Tayi maganar tana ƙarewa Iman kallo.

Umma ta ce "Eh irinsa ne"

"Wow, it worth 120k fa, lallai autar gidan Galadima, kin riƙe wuta".

Iman jin ta take tamkar a kan wuta, dan haka a gurguje ta ce "Ummma dama abincin salla ne, Ammi ta ce na kawo miki, kuma nazo mu gaisa, bari na tafi".

"Kai Iman tun da wur haka, ke dai ba kya son mutane, shikenan bari na baki barka da salla".

"A'a Umma, ai na girma da barka da salla" iman tayi maganar tana miƙewa .

"Ƙaniyarki, tsaya ki karɓa mana" girgiza kai iman tayi, ta fice daga ɗakin da sauri.

Har ta kai tsakiyar falon, ta ji an riƙe mata jaka.
Ta waiwayo tana kallon wadda ta riƙeta.

"Duk na san kin ci kin ta da kai, Ammi tana ji dake, na san kina da kuɗi baki rasa komai ba, amma yakamata ki karɓa tun da kin san baki da gado a cikin dukiyar gidan Galadima?"

Cikin rauni Iman ta ce "Anty Soafy me kuma ya kawo wannan maganar?"

Cikin ko in kula Soafy ta ce "Yau aka fara gaya miki irin wannan maganar ne, ai gara a dinga yi ana tuna miki, ko ba haka ba?" Ta fizgi jakar iman, ta saka mata kuɗin, ta saƙala mata jakar a kafaɗarta ta koma ciki.

Gwiwa a saɓule, iman ta nufi fita daga falon, tuni idanunta suka cika da hawaye, sai dai tana fitowa ya sha gabanta, ya ƙureta da idanuwansa.

Ƙoƙarin ratsewa take ta wuce, amma ya ce "Me ta ce miki ne, har ta saka ki kuka?"

Girgiza masa kai tayi alamar bakomai.

Yayi murmushin gefen baki ya ce "Anyway, kin yi kyau sosai a outfit É—in nan, ashe yayanki yana Saudiyya babu ko sallama?".

"Uncle J, am sorry sauri nake, Ammi na jirana" daga haka ta wuce ta bar shi a wurin a tsaye.

**********

Zuwa yamma mama ta saka ruma a gaba sai sa ta cire shaddar nan, dan idan ta bar ruma da ita sai shaddar ta fita daga hayyacinta.

Kwanukan da aka ɓata, Yasir ya tattara yana wankewa, mama ta ce "Ke, shiga ɗakinsu ki dudduba mini idan da kwanukana, cokula ko kofi, duk ki fito mini da su, dan na san hali, sai a kai mini kwano ɗaki a ƙi fito da shi"
Ruma ta tashi ta nufi É—akin samarin nan, ba tare da ko sallama ba.
Usman ne a kwance yana waya, kuma da alama da mace yake wayar.
Buɗe baki tayi, ta tsaya tana kallonsa. Zumbur ya tashi zaune, ya katse wayar ya ajiye ya haɗe rai ya ce "Zo nan" ba musu ta ƙarasa in da yake.

"Me ki ka ji?"

Ta ce "A ina?"

"Ina tambayarki kina tambayata? Nace me ki ka ji?"

"Wallahi ban ji komai ba, kawai dai na ji ka ce....." Sai kuma ta yi shiru.

"Ba zaki faÉ—a ba sai na taka ki?"

Ta tura baki sannan ta ce "Na ji ka ce, wai kwalliyar ta tayi kyau, kamar farin wata".

"Sai kuma me?"

"Shikenan na ji wallahi "

"To na rantse da girman Allah, idan ki ka sake ki ka faɗa, wallahi sai na yi miki dukan tsiya, ƙanwar abokina ce ba wata ba"

"To ai ni dama ban ce zan faÉ—a ba, mama ce ta aikoni" daga haka ta shiga duddubawa mama kwanukanta.

Aikuwa ruma ta fito da kwanuka a hannuta tana faɗin mama "Kin ga kofin ki, an sha fura a ciki sha zumamu ya siɗe miki kofi tas, har ɓera ya fara ci. Kin ga plate ɗin ki har da sauran alalar da ki ka yi tun sati biyu da suka wuce".

Yasir ya ce "To munafuka, uban waye ya saka ki wannan sharhin?"
Chapter 17 · 0% Book details