← Book details Ƙanwar Maza Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 20 OF 47

Sashe 20

Ƙanwar Maza Complete Hausa Novel · about 8 min read

"To Meyasa ki ka wanke nawa kayan?"

"So nake nima na yi abin arziki, ban zaci zai zama na tsiya ba"

Ya girgiza kai ya ce "Zubo mini Abinci" ta tashi tana ta tsuma, ta je ta zubo abinci ta kawo masa tana kallonsa.

Ya karɓi Abincin, ya ajiye a gabanta ya ce "Ci Abinci"

Fuska duk hawaye ta ce "Dan Allah ba zaka saka ni kama kunne ba?"

Ya girgiza mata kai ya ce "Ba zan saka ki ba" yayi maganar yana É—ebo Abincin ya kai bakinta.

"To ka haƙura?" Ya jinjina mata kai alamar eh.

"To dan Allah ka yi haƙuri, tsautsayi ne"

"To, ci abinci" sai a lokacin ta ji ranta ya yi sanyi, har ta fara cin abinci, babu wanda bai yi mamakin yadda mai sunan Baba ya ƙyale ruma ba, basu taɓa kawo zai rabu da ita ba.

Sai da ta ci ta ƙoshi sannan ta ce "Me sunan Baba"

"Na'am"

'Dan Allah ka yi haƙuri, zan karɓi kuɗina na wurin mama sai na saya maka wata "murmushin gefen baki ya yi ya ce 'To Shikenan".

Bayan yaya Umar ya fita, Huzaifa ya lallaɓa ya bi ruma ɗaki yana cewa "Ruma, wace addu'a ki ka yiwa mai sunan Baba ya ƙyale ki ne? Zo ki gaya mini"

Usman ya ce "Wallahi nima na yi mamaki duk ɓarnar nan da ta yi masa ya ƙyaleta"

Babu wanda ta kula a cikinsu ta kwanta tana yiwa Allah godiya.

Hidindimun Salla suka wuce, aka koma makaranta, ruma ta koma makaranta, sai dai fafur ta ƙi zaman ajinsu, wai malaminsu baya son ta, wani malam Habibu ɗan mai makarantar ta liƙewa, duk ajin da za shi ya yi ƙari sai ta bishi, gashi ta maƙalewa Auwal, yaya sama yaya ƙasa haka take kiransa saboda yana sayen tsami gaye da goriba ya bata.

Yanzu ma 'yan ajin su Yasir suna jiran malam Habibu ya zo yayi musu ƙarin Alqur'ani, sai ga shi ya shigo shi da ruma.
Yasir yana ganinta ya tsuke fuska, dan tun wancan hansfreen da ta yi masa a gida, ya hanata zuwa ajinsu, amma sai gata.
Malam Habibu ya zauna, ya ce ta shiga cikin mata ta zauna. Aikuwa ta shiga ta zauna, ta nutsu kamar gaske aka yi ƙarin nan aka idar.
Aka zo kowa yana biyawa, aka zo kan Yasir shi ma ya biya, sai cewa ta yi 'Inyee ashe ka na ja, hmm da ba ka iya ba wallahi da sai na faÉ—a a gida, in ce kai ma baka iya karatu ba"

Dariya 'yan ajin suka hau yi suna kallon Yasir, ya sunkuyar da kai yayi mata shiru.

Kowa ya gama biyawa, ruma ta ce "Malam nima zan karanta"

Ya ce "To bisimillah"

Abun mamaki sai ga ruma ta karanta shafi guda, duk da tana yi ana cin gyaranta, amma ta kai shafi guda, ba ƙaramin mamaki ta bawa Yasir ba, yarinyar da ta ce ita gejinta aya biyu kawai.

ÆŠari biyar malam Habibu ya bata, tare da jinjina mata, dan babu wanda bai san ruma ba ta ja ba.
Da ya kammala ƙarin ya ce ta ta so su tafi, amma ta kalli yadda Yasir ya haɗe rai ta ce "Malam ni ka bar ni a nan ajin"

Malam Habibu ya ce "To shikenan, duk malamin da ya zo ace masa ruma ajiyata ce, sanna ba ruwan kowa da ita kar a takura mata"

Suka ce to.

Yasir kuwa kamar ya zo ya rufeta da duka, dan ba zata taɓa zama shiru ba.

Ruma ta shige cikin 'yan mata, suna hirarsu, ita kuma tana shan farar ƙasarta, amma duk tana jin me suke faɗa.

Yau har aka tashi tana ajin su Yasir, sai da aka tashi ta bar ajin.

Ta je ta samu tsohuwar da take sayar da kayan yara a a ƙofar makarantar, ya titsiyeta wai sai ta bata farar ƙasa kyauta.
Duk shegen son kuɗi irin na iya, sai da ta bawa ruma farar ƙasarar nan, saboda shegen surutun ta da nacin tsiya.

Ta karɓi farar ƙasarta ta yi gida, haryanzu makarantar nan ba ta da ƙawaye, a cewarta ɗaliban ba su yi mata ba, kuma ba komai bane su ɗaliban sa'aninta kowanne ya mayar da hankali a kan karatunsa ne, ita kuwa ruma 'yar abi yarima a sha kiɗa ce.

Tun da ta je gida take tafa hannu tana masifa, "Wallahi an mini laifi a gidan nan, kuma sai kowa ya hallara zan faɗi me aka yi mini" jin kowa ya shareta ya ƙi kulata ya sanya ta ce "Mama yanzu dan Allah abin da ake yi mini a gidan nan ya dace?"

"Da aka yi miki me?"

"Mama a gabanki 'ya'yanki suke ce mini ƙwaila, amma baki taɓa hana su ba"

Mama ta dubeta ta yi murmushi cikin manyance ta ce "To ba ƙwailar bace ba?"

Ruma ta buÉ—e baki ta ce "Au mama har da ke?"

Aliyu ya ce "To meye dan an ce miki ƙwaila, ai ƙwailar ce"

Ruma ta ce "Kutt, ƙwaila fa wadda ba ta da nono kenan?"

Aliyu ya ce "Innalillahi wannan gingimemiyar maganar fa"

Mama ta ce "ke waye ya gaya miki haka?"

"'yan ajin su Yasir ne suke faÉ—a, matan nan ina jin su da kunnen nan nawa, sun zaci bana jin su"

Mama ta ce "To ke nonon ne da ke da ba za ace miki ƙwaila ba?"

"Mama gori dai ake yi mini kenan? Sai in je wurin Mai furar nan na bakin hanya, na sayo nonon, na zo na ƙulla a leda na dinga sakawa" cike da takaici mama take bin ruma da kallo, ta ma rasa me zata ce mata. Usman yana tsakar gida, sai ƙyaƙyata dariya yake ƙasa-ƙasa lamarin ƙanwar nan ta su sai Addu'a kawai.

Aliyu ya ce"Ke da ki ke ƙanwar maza, me zaki yi da wannan abun? Ki yi zamanki a haka ai sai kin fi kyau"

Ta ce "Kuma fa haka ne" ta cire rigar islamiyyar, daga ita sai vest, ta sinsina rigar ta kuma cewa "Mama, dan Allah yaushe zan fara warin hammata, ina son idan na cire riga na sansana na ji tana ɗan warin nan da ƙamashin turare "

"Fitar mini daga ɗaki dan ubanki, shashasha mara alƙibla fita ki bar mini ɗaki".

AYSHERCOOL
08081012143
[08/07, 4:58 pm] JAKADIYAR AREWA:                   ƘANWAR MAZA
                

Na Aisha Adam (Ayshercool)

MIKIYA WRITER'S ASSOCIATES

https://www.youtube.com/@CoolhausaNovels

Ku yi subscribing  YouTube channel ɗin
@Cool Hausa Novels, domin samun daÉ—aÉ—an litattafan hausa na sauraro.

*A TAIMAKA AYI SUBSCRIBING YOUTUBE CHANNEL ƊINA NA COOL HAUSA NOVELS, KO IN KOMA POSTING SAU ƊAYA A SATI 😒*

10

ÆŠan tsayawa ruma ta yi tana kallon mama, cikin sangarta ta ce "Mama wai me na yi to?"

"Ban sani ba fitar mini daga É—aki, mara kan gado, ni ba dan a gida na haifeki ba, cewa zan yi an canza mini 'ya, idan an yi gabas sai ki arta ki yi arewa, me ake da wani wari ban da rashin kan gado irin naki?"
Tsayawa ruma tayi tana kallon mama tana wasa da gashin kanta.
"Ba zaki fita ki bar mini É—aki ba, sai na taso kan ki?"
Fitar ta tsakar gida yayi dai-dai da shigowar Yasir, da shi da Huzaifa.

Yasir ya aika mata da wani irin mugun kallo ya ce "Me na ce miki game da zuwa Ajinmu?"

Ta murguÉ—a baki ta ce "Ni wurinka na zo, ai ba wurinka na zo ba, ni da malam Habibu muka zo"

"To uban me ya hana ki je ajin su Huzaifa?"

Huzaifa ya yi caraf ya ce "Wallahi ta zo mana aji, sai na mata dukan tsiya, ta zo É—in ta gani"

Hararsu ta dinga yi, tana cewa wallahi sai ta je.

Bayan Huzaifa ya canza kaya, ya shiga É—akin mama ya É—au jakarta.
Ruma ta É—aga murya ta ce "Mama, ga Huzaifa nan ya É—aukar miki jaka"

Ya ce "To munafuka"

"Wallahi ni ba munafuka ba ce, mama Huzaifa zai satar miki kuÉ—i"

Huzaifa ya ce "Mama aron naira É—ari zan É—auka"

Mama ta ce "Ajiye mini jakata, ba zan baka aron ba, idan ka É—aukar mini kuÉ—i ba bani ka ke ba"

"Dan Allah mama ki bani, zan baki wallahi"

Daga kitchen mama ta ce "Ba zaka ajiye mini jaka ba sai na zo É—akin nan?"

"Mama wallahi bai ajiye miki ba"

A fusace Huzaifa ya ajiye jakara, yana yiwa ruma kallon banza, kamar ya kai mata duka haka ya fice.

Ruma ta ce "Dana sani na bar shi ya É—auka, nawa nake bin mama ba biyana take ba"

***

Yau za a rufe makarantar su ruma a tafi hutu, yau za ayi spelling B da aka bawa su ruma.
Sai bin malaminsu take tana ce masa ita fa sai an sakata a cikin masu spelling B.
Malamin ya ce "Ki kwantar da hankalinki, zamu san yadda za ayi".

Azabar nacin ruma sai da ya sanya aka sakata a cikin masu spelling B, amma aka ce kar ta yi magana.

Ƙarshe dai ruma ce ta taimaki 'yan ajinsu, gaba ɗaya kalmomin nan babu wanda ba ta haddace ba, ruma ta bawa malaman makarantar su da ɗaliabai mamaki, dan ko bata takardar da aka yi, tsabar naci ne ya sanya a ka bata.

Ai kuwa ruma ta samu kyaututtuka sosai, karo na biyu a rayuwarta, da ta samu wani abun arziki a saboda harkar karatu.
Aka bata litattafai kaya guda, da kayan koyon karatu.

Ruma baki har kunne ta je gida, mama ta ganta da kaya niƙi-niƙi.

"Ke wannan kayan na menene?"

Ruma ta zubewa mama kayan ta ce "Mama, duk nawa ne a makaranta aka bani"

"Meyasa aka baki?"

"Wannan takardar da aka bani ce a makaranta, kowa ya ƙi koya mini, na je na yi ta yi da kaina, shine fa aka yi yau na samu wannan kyautar"

Mama ta ce "Hmm, ai shikenan"

"Mama wai na ga kamar ba ki yadda da bayanin da na yi miki bane?"

"Eh to kusan hakan, dan abin da kamar wuya gurguwa da auren nesa"

Cikin rashin fahimta ruma ta ce "Mama wace gurguwar kuma?"
Chapter 20 · 0% Book details