← Book details Ƙanwar Maza Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 30 OF 47

Sashe 30

Ƙanwar Maza Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Ina fatan dai ba a gaban wadda ta dake kin ki ka yi kukan ba? Wallahi da ina gidan nan sai kin fita kin rama, dan ubanki yaushe ki ka koma shashasha har aka dakeki aka fitar miki da jini, 'yar uban waye da baki taka mini ita ba"

BuÉ—e baki mama ta yi, ta kalli Aliyu ta ce "Gadanga, maimakon ku tayani yi mata faÉ—a, ku ke mara mata baya? Ba sai ku ce Allah ya sa hakan ya zama silar shiriyarta ba"

Aliyu ya girgiza kai ya ce "A'a Addu'a ce kawai za ta shiryata, amma ba a daketa a waje ta tsaya tana kuka ba, babu rago a gidan nan, ko ɗan uban waye ta daka zamu bada haƙuri, amma wallahi aka kuma dukanki a waje, ki ka zo mana gida ki na kuka, sai na ƙara miki wallahi, idan mazane kawai ban yadda ki yi faɗa da maza ba, ki zo ki gaya mini, amma mace dai 'yar uwakki, ki tattaka mini kowacece"

Aikuwa mama ta haÉ—asu gaba É—aya ta din ga faÉ—a kamar ta ari baki.

"Kaf cikinku babu wanda na sha wahalr rainonsa kamar ruma, amma kuna zigata ta É—auko magana, rainonta dai-dai yake da rainon fitinannun yara maza huÉ—u, maimakon ku tayani dawo da ita hanya, amma ku ke ingizata"

Gaba daya suka yi wa mama shiru, ta yi ta banbaminta ta yi ta gama.

*****
Karkarwa jikinsa yake yi, tamkar zai hau bori, jikinsa sai wani ƙaƙƙamewa yake yi, tamkar ba jikin ɗan Adam ba.
Wata matashiyar mace ce zaune a kan gadon, tana kallonsa, ido fal hawaye, ya yin da shi kuma ya cigaba da tunkararta.
Girgiza masa kai take yi, amma ta kasa motsawa balle ta gudu.
Yana zuwa ya zauna a gabanta ya tsura mata ido, ya miƙa hannunsa kan cikinta, take jikinta ya hau rawa ta rintse idanuwanta, tana zubar da hawaye. Sautin muryarta ne ya dakatar da shi ga aikata abin da yake ƙoƙarin yi
*Sarki ka ganni, ya na ga sarki da ƙananan kaya, sarki ka kalleni* tamkar a zahiri haka yake jin muryartata a cikin kunnuwansa, a hankali ya buɗe ido ya na ƙarewa ɗakinsa kallo. Sai a lokacin ya gane mafarki yake yi, ba zahiri bane.
A hankali ya tashi ya zauna, ya yaye bargon da ya rufa da shi, ya kalli agogon da ke kafe a jikin bangon ɗakin. Ƙarfe tara da rabi.
ÆŠan guntun tsaki ya ja, me yasa yake yawan jin muryarta ne? Anya ba aljana ba ce ita ma?. Gabansa ne ya faÉ—i da yayi wannan tunanin, da kuma tuna matsalar da yake ciki, yake ta neman mafita a kanta.
Saurin girgiza kai ya yi, ya sauka daga kan gadon, ya wuce banÉ—aki.

****
Cikin matsanancin razani ta ƙwala ihu "Wayyo Allah mama" a gigice mama tayi kanta tana faɗin "Ke lafiyar ki kuwa?"

Tashi ta yi zaune ta na rarraba ido, tana kallon É—akin.

"Lafiya menene?"

"Mafarki na yi na tsorata"

Mama ta ja tsaki ta ce "Ba dole ki dinga mafarki kina tsorata ba, tun da ba kya Addu'a kwanciya bacci".

"Wallahi mama na yi"

"Ke ki ka sani dai, ko a garin neman maganar ki ruma, kya tsokano abin da zai dinga tsorata ki, ya hana ki bacci tashi ki je ki yo alwala, yanzu za a kira sallar asuba.
Haka nan jiki babu ƙwari, ta tashi ta yi alwala ta gabatar da raka'atanul fajr, sannan ta yi sallar asuba.
Jikinta duk yayi sanyi da mafarkin da ta yi, amma ta kasa tuna me ta gani a mafarkin ya tsorata ta.

Babu wanda Ruma ta kula a ajinsu, ta nemi wuri ta yi zamanta ta yi shiru, tana ta takura ƙwaƙwalwarta, ta tuna mafarkin da ta yi ya bata tsoro, amma ta kasa har aka kusa tashi, hankalinta baya tare da ita.

Asiya ce ta zo kan ruma ta tsaya, ta riƙe ƙugu ta ce "Ki je ki wanke banɗakin da aka saka ki, ko na je na faɗa" tamkar ruma na jin tsoron Asiya, haka ta tashi jiki na rawa zata fita daga ajin, sai dai ta yi burki a gaban allo, ta ɗaukko chalk a aljihun rigarta, ta sake zana wata shirgegiyar matar, wadda tafi ta jiya, ta yi labelling ɗin ta.
Ta waiwayo kuma tana kallon Asiya, tare da jiran ko ta kwana.

Aikuwa kamar ruma ta san a rina, Asiya ta kuma nufo ruma, tana zuba ashar, kan ta ƙaraso ruma ta yi ciki da ita, suka faɗa kan wasu ɗalibai.
Hannun Asiya ɗaya ta samu, ta din ga duka kamar ta samu ɓarawo, sai da ta tabattar da ba zata iya kai duka da hannun ba, sannan ta koma fuskarta.

An kai ruwa rana kan a ƙwaci Asiya daga hannun ruma, sai a lokacin ruma ta ji hankalinta ya kwanta, baƙin cikin da ya tokare mata zuciya ya sauka.
Babu wata-wata, malamin su ruma ya saka su kneeldown a rana, ba tare da ya tsaya ya ji ba'asin ma meyafaru ba.

Tun a lokacin Asiya ta ji ba ta iya motsa hannun da ruma ta din ga jibga, ta din ga jin kamar ba a jikinta yake ba.

Suna Kneeldown ruma ta riƙe ƙugu ta ce "Ke kin isa ki dakeni na ƙyaleki, hmm baki sanni bane, kuma wallahi ban huce ba, zaki ga abin da zan yi miki, ki dakeni ki zageni, sannan ki zaci kin ci bulus, ai faɗa ni da ke daga yau har ranar busa ƙaho, ba dai uwata ce tsohuwar banza ba sai ka ce babata sa'arki ce ba? Ai ki yi mini komai ban da taɓa uwata, ban taɓa zagin uwar wani ba, kema babarki  jibgegiyar bayerabiya masu kashi a leda"

Gigicewa Asiya ta yi, tana kuka tana son kaiwa ruma duka, amma ta kasa sarrafa hannunta ga ciwon da jikinta yake yi mata.
Ruma ta durƙusa ta dinga dumbuzar ƙasa hannu bibbiyu tana watsawa Asiya a fuska. Ban da kuka babu abin da Asiya take yi.

Ranar ma sai da aka tashi sannan aka sallame su, aka ce gobe da safe za su cigaba da punishment.

Rumaisa ta riga Asiya tafiya, ta je ta samu hanya, ta tattara duwatsu, ta tara su a cikin jakarta. Ta kuma datsar Asiya a hanya, ta dinga kabbara tana jifanta. "SheÉ—aniya gara na jefeki na huta, na ga haka ake yi idan an je makka a jefi sheiÉ—an, gobe ko cewa aka yi ki kalleni, ba zaki sake ba balle ki dakeni"

Sai da ruma ta gama abin da Allah ya nufeta da yi, sannan ta wuce gida. Yau kam bakinta har kunne, jin ta take wasai ba ta da wata damuwa ko banza ta rama abin da aka yi mata har da riba, malamai kuwa ko zasu kwaÉ—ata su cinye bai dameta ba.

Abdallah ne yake ta shiri, ruma sai tambayarsa take ina zashi?.

"Ke wai kin aikeni ne?"

"A'a, amma dan Allah ka gaya mini"

"Cikin gari zani ziyara"

Ta haÉ—a hannayenta biyu ta ce "Dan annabin rahama ka tafi da ni" hararta ya yi ya cigaba da shirinsa.
Ta dinga bin sa tana lallaɓa shi, har ya amince zai tafi da ita.
Mama ta ce "Hmm in dai ruma ce zata baka kunya, Allah ya sa kar ta É—auko maka magana"

"Ta É—auko ma, dakuwa zata yi wallahi"

Ruma ba ƙaramin daɗi ta ji ba, ganin ta a cikin gari cikin 'yan uwa, akwai 'yan uwan mama sosai a cikin gari, sai dai mama ba ta zuwa da ita, saboda ta din ga neman magana da dukan 'ya'yan mutane kenan.

Akwai wata 'yar cousin ɗin mama, da rashin jin su ya kusa zuwa ɗaya da na ruma, duk da ruma ta fita. Ta ce "Ruma, zo mu je yakasai, akwai ƙawata a gidan Turakin Kano, jikarsa ce biki ake a gidan, kuma za ayi kilisa, kan Abdallah ya dawo mun je mun dawo, mu je mu ciyo banza"

Ruma ta ce "yauwwa hauwwaliya, yi sauri ki shirya mu tafi kan ya dawo ya hana ni zuwa"

"Ke har da babbar leda zan ɗauko, idan mun ci mu ƙullo sauran"

Haka suka shirya, suka yi sallama a kan zasu je biki su dawo.

Suna tafe a hanya suka sai masara, suna tafe suna ci suna hira.

Tabbas idan ka ji wane ba ƙarya ba, gidan ya tsaru yayi kyau sosai da sosai, gini ne na sarauta da aka ƙawata da kayan alatu, ruma sai rarraba ido take yi.

Ƙawar hawwaliya ta din ga murna da ta gansu, ta kai su wani falo suka zauna.

Ruma kuwa hankalinta na kan wata mata, da ta sha ado sai kai wa take tana komowa tana wani hura hanci, tana dakawa mutane tsawa.

Ruma ta ce "Taɓ, wai wacece waccan?"

Yarinyar ta kalli wadda Ruma ta nuna ta ce "Laa Anty Samha ce, ƙanwar mama ce, ba mata bace ba ta da aure".

Ruma ta ce "too na ganta wata gwabjejiya, sai masifa take yiwa mutane, ni na zaci matar sarki ce ma, yakamata a samu mai kwaÉ—eta ya zata din ga hantarar mutane?"

Hauwwaliya ta daki cinyar ruma ta ce "Ke, ƙanwar mamanta cefa"

Yarinyar ta yi murmushin yaƙe ta ce "Bari a kawo muku Abinci, sai mu je wurin kiɗan ƙwarya da kilisa"

Ruma ta miƙe ta ce "Hauwwaliya, ni dai zan je wurin da na ga an ɗaure dokuna na kallesu, idan an kawo Abincin ki ƙulle mini nawa a ledar da ki ka zo da ita" buɗe baki Hauwwaliya ta yi, da jin hansfreen da ruma ta yi musu.

Kai tsaye ruma ta fito tana cigaba da kallon gidan, da yadda manyan mata ke shiga suna fita, da shiga kala-kala.

"Ke ba kya gani ne, meye haka?" Ruma ta É—aga kai ta kalli wadda ta daka mata tsawar. Matar da take ta hantarar mutane ce.

"Eh bana gani, sandata na fito nema, ke da ki ke gani meya hana ki kauce?" Ruma ta yi maganar tana tsare Samha da ido.

Wata mummunar faɗuwar gaba ta ziyarci Samha, da ta yi tozali da idanun ruma, ga ta ƙarama amma wani abu mai kaifi ne a idanun ruma.
Ruma ta raɓata ta wuce abinta. Da sauri Samha ta bi bayan ruma, amma ta nemeta ta rasa.
Chapter 30 · 0% Book details