Sashe 6
Amani Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
mutane irin ku, masu mayar da dan kowa nasu Ya dubi Daddyn Amani yana murmushi ya ce yadda ka rike min Mukhtar da amana ba tareda ka san komai a kan sa ba, haka nake fatan in rike Amina daga nan har karshen rayuwar mu, ko da bata kasance yar uwar sa ba. Allah ya saka maka da alkhairi ya kuma baka lafiya. Sai ga Mukhtar ya shigo dakin daga shi sai farar jallabiyya kal da bakar hular larabawa a kan sa, kallo ya koma gare shi suna mamakin yadda cikin kwana daya tal ya canza ya koma tamkar ba shi ba, yayi kyau, yayi wani irin fresh tamkar balaraben Madina. Kamar da ka latsa shi jini zai yi tsartuwa. Nan aka gaya masa ko me ke akwai, wato Jal an kanwar Ummami ne ta jini, uwa daya uba daya. Mukhtar sai kamar bai yi wani mamaki ba, cewa yayi ai ni naso in gane hakan tuntuni, kawai ban san komai akan Ummami bane ko dangin ta, wanda zai karfafa zargin nawa, amma tabbas na ga alamu, tun sanda na ga cindo Ummami a hannun ta da wasu attributes da dama, sannan jiki na ya bani, son da na samu kaina ina ma Mamma, kamar na Ummami ne, musamman da ita ta sake da ni sosai ba kamar Ummami ba cikin yan kwanakin da nayi tare da ita Nan aka shiga mayar da zance, aka dauko tarihi tun daga farkon sa, tarihin masarautar Diffa da yadda kakan sa Sultan Oumarou ya bada sarautar ga dan sa Sultan Massaoudou tun yana raye, bayan rasuwar sa Sarki Issouffou ya gaji sarautar daga hannun mahahifin sa Sarki Massaoudou. Ya ce sun kasance su masu karancin haihuwa ne a jinin su, shiyasa suke aure-aure daga kasashen Africa daban daban daga kyawawan matan Africa, wadanda suke saye suna sa-daka dasu (concubines) basu cika maida su matan aure ba. Ya ce amma ita tunda aka kawo ta gaban mahaifiya ta ta ganta da tabon sujjadah a goshin ta, sannan aka gaya mata daga Saliyo take sai tace aure za a daura mana bata yarda in yi sa-daka da ita ba. Marigayiya mahaifiya ta tace matan Saliyo mata ne na musamman, daban suke a halitta da sauran matan Africa, Allah yayi musu baiwa ta auren manyan mutane, tace sanda zata kwace Mowar Diffa daga hannun Ummu Aymana, bazan sani ba Sarki yayi murmushi yace and that s exactly what happened today, Aisata Mowar Diffa! Kafin ita ina da matan aure guda biyu, uwargida Ummu Aymana yar sarkin Zinder tana da ya daya; Sayluba. Sai Tarha diyar sarkin Agadaz wadda itama na samu haihuwar diya mace da ita. Sai aka daura mana aure na Sunnah da Aisata, na bata dakin mace ta uku a gidan sarautar Diffa. Kasancewar duk matan da ake kawomin matsayin sa-daka nake basu, wannan ya tada hankalin mata na; Ummu Aymana da Tarha. Musamman da ya kasance har zuwa lokacin babu wadda ta samu haihuwar Maina cikin su. Suka daga hankalin su a kan Ummami nima suka daga min, sanda ta samu cikin Mukhtar kuwa ina wuta su saka ta, aka hanamu aure ta hanyar saka min tsanar ta a shimfida, aka saka mata warin gaba, aka saka mata kurarraji kai matsaloli marassa dadin ji iri-iri a dalilin wannan ciki kamar ba zai kai labari ba. Don daga baya ko dokin haihuwar tata na daina. Na koma ganin abinda zata haifa min din a matsayin matsala. Sai malaman fada ne suka saka ta gaba da addu a don kowa yana so Diffa ta samu Maina, basa so sarautar ta bar gida na, don ina da yan uwa a raye, amma ni ko a jiki na. Uwargida na da bakin ta ta gayamin cewa muddin Aisata ta haifi Da namiji sai ta salwantar da rayuwar sa, na kuma san zata iya, a yadda ta cika zuciyar ta da burin ita zata haifa mun Maina. Sai bayan an haife shi an kawo min shi hannu na zuciyata ta cika da kaunar sa, gashi cikin yan uwa na ma da suke da yara maza basu so na samu Maina ba, sun so ya kasance na mutu babu magaji don sarautar Diffa ta koma hannun yan su. Don haka na san ta ko ina Mukhtar yana cikin hadarin makiya musamman da ya kasance kamar an tsaga kara ni da shi a kamanni. Sai na shiga tunanin ta hanyar da zan bi in kare rayuwar sa. Nan na zaunar da Aysata, na ce wannan yaro kin haife shi dai ko? To ki godewa Allah komin runtsi sunan sa dan ki, amma ki nema masa kariya ta hanyar rashin nuna kauna da kulawa a gare shi. Ta yi min kallon rashin fahimta nan na wayar mata da kai, na ce mata na barshi karkashin kulawar bayin mahaifi na na tun tali-tali, wadanda nima gadar su nayi a gun mahaifa na saboda amanar su, wato Katchalla sarkin fada da Jakadiyar dana bata. Na ce ta runtse idon ta daga kan yaron nan, ta bar shi ya rayu a hannnun su. Zasu kula da shi kamar yadda zasu kula da yan su amma rayuwa irin ta yan su. Da yake Aysata mai fahimta ce, mai kuma bani hadin kai akan duk abinda na zo mata da shi sai ta yarda. Amma ta roke ni in bar ta ta shayar da shi ko a boye ne, ko na tsayin shekara daya ne, na amince mata. Don na san muhimmancin nonon uwa, kuma inaso ya tsotso irin kwakwalwarta da kyawawan dabi un ta. A takaice wannan ne dalilin da yasa muka yi wa Mukhtar rainon da muka yi masa, yau gashi Allah ya raya shi yadda nake fata, duk wani da ya nufe shi da sharri na tabbata ya ga abun sa a kwaryar shan sa, domin koda aka gaya min kurciya aka yi masa daga baya ni ban damu ba, na bar shi ya je ya koyi rayuwa har zuwa lokacin da ni da kai na nasa malaman fada suka karya sihirin, tun a daren ne kuma aka gaya min Ummu Aymana ta fita daga gidan nan, ta tafi har Zinder a kafa, ita ba mahaukaciya ba, ita ba mai hankali ba, ta dai koma kamar tababbiya, kuma kalamanta kullum. Mainan Diffa dana yi wa kurciya zai dawo yanzu ya karbi Diffa A halin yanzu tana can hannun iyayen ta ana mata magani amma tace bazata dawo gida na ba in dai Mukhtar na cikin sa. Don haka a jiya na datse igiyar aure na da ita na aikawa mahaifin ta sarkin Zinder. Diyar da muka haifa nida ita (Sayluba) na dade da aurar da ita a Tahoa, tana da ya basu fi uku ba itama ta gado rashin yawan haihuwa ta, sai kanwar ta yar wajen Tarha (Saadiyya) itama tana aure a kasar Guinea kusa da Liberia ga Amabasadan Nijar a Guinea. Bayan Aisata ta haifi Mukhtar shiru shiru babu karin haihuwa a gida na, sai na kara aure da Balqissa, wadda aka kawo min ita daga kasar Abidjan. Har yau itama bata haihu ba, Mukhtar mai bakin baya ka hana ni samun ko ya matan ne sabida alhakin ka Ubangiji ya hana ni Ya karasa fadi cikin zolayar Mukhtar. Sai da kowa a wajen yayi dariya Ummami ta ce kada ka damu MAI DIFFA! Ba da jimawa ba in sha Allah diyata Aminatu zata cika maka gida da . Jal an ta ce ni nafi so a kara mishi da sadakoki yadda yaran zasu fi saurin taruwa dariya kowa yayi, amma banda Amani da Mukhtar, wadanda duk suka bi suka daddaure fuska, kuma kowanne yaki yarda ya kalli inda dan uwan sa yake. A zuciyar ta cewa take ta Allah ba taki ba Mamma Ga dukkan jin dadin ta sai Ummami tace in har ba ya zama (Mai) din Diffa ba (Sarkin Diffa) babu mai bashi sa-daka a halin yanzu. Yanzun Maina ne kawai, ku bar su su mori kurucciyar su don Allah Sai Amani ta hau addu a a cikin ran ta; Ya Allah kasa kada a taba baiwa Mukhtar sarautar gidan su, Allah ka kara nisan kwanan mahaifin sa, yayi ta zama a muhallin sa na Mainan Diffa (Ta manta Sarki ya ce tun da ran sa zai baiwa Mukhtar kujerar sa). Sarki yayi umarni da su Jal an su koma bangaren Ummami da zama har Amani. Gobe-goben nan za a saka tubulin ginin bangaren matar Maina. Ya kuma ce a yau dinnan zai soma aika takardar gayyata zuwa ga sarakunan jamhuriyyar Nijar, wato gayyatar bikin auren Maina da nadin sarautar sa ta (MAINAN DIFFA). **** ****** ****** MOUKHTAR ISSOUFFOU MASSAOUDOU (MAINAN DIFFA) aka jin komai sai tashin bushe-bushen algaita da kade kaden ganguna irin na masautar Diffa, a yau Asabar, wadda ta kasance ranar bikin auren Maina da nadin sarautar sa. Cikin wadanda suka halarci wannan kasaitaccen biki har da Yayar shi gimbiya Sayluba daga Tahoa, mai bi mata da yake tana Guinea, bata samu zuwa ba don tayi nisa sosai, mahaifin ta ya aika mata kan ta zo ga dan uwan ta Maina ya dawo gida, ta ce sai ta haihu zata zo daga baya, tana cikin watan aifuwa. Tunda aka soma shagulgulan bikin nan wanda za a kwashe kwana bakwai ana yi Amani bata saka Mukhy a idon ta ba ko daga nesa, rabon ta da shi tun washegarin zuwan su Diffa, wato ranar da suka gana da iyayen sa, yana can cikin sarakuna abokan Baban sa da yayen su sa annin sa, wadanda iyayen ke kokarin kulla abota da zumunci mai karfi tsakanin yan nasu, kamar yadda nasu iyayen suka yi masu. Ba iya masarautun Nijar kadai Sarki ya gayyato ba har daga bangarorin masarautun Songhai, Mali, Gao, da Kanem-Bornu. Haka ya gayyato aminin sa Sarkin Burkina-Faso, wuri yayi wuri, taro yayi taro sai Rakuma ake kayarwa ana gashewa ana kyafewa. Abinci kuwa duk iya diban ka haka zaka gaji da diba ka bari. Umami tasa an yi wa Amani kwalliya irin tasu, da kaya na shudin karen miski da sarkokin zinare har a hancin ta, an dorata akan kujerar Mowar Diffa, wato kujerar da Ummami take zama a kai koyaushe, abin gwanin ban sha awa, shagalin sai wanda ya gani. Kwana bakwai aka kwashe