← Book details Amani Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 14 OF 19

Sashe 14

Amani Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

fadar sarki. Don haka ta roki Ummami Allah Annabi tana son zuwa masaukin su Alhaji. Ummami tasa kuyangin ta wato Sugra da Tahira suka raka ta har inda aka sauki su Alhajin, da gudu ta karasa shiga dakin tana kwarara kiran sunan Alhaji Daddy, Daddy na! Alhajin kuwa ta fara yin tozali da shi yana tsaye a kan kafafun sa yana waya da Matawalle da ke Katsina, da gudu Amani ta karasa ta rungume shi, tana kukan farin ciki, da godiyar Allah. Mamma ce ta hau ta da fada tana cewa ta yi masa a hankali, bashi da kwari, jiya ba yau bace, kuma da da yanzu ba daya bane a gareta ita kan ta, ta daina wannan haukan da take yi a jikin Alhaji. Ita matar gida ce yanzu Ta dube su duk sun murje sun yi gwanin kyau, tsufa duk ya bace, Alhaji yayi kiba yayi haske, ta hau dariya ta ce ai kawai Mamma ki ce honeymoon kika tafi kai Alhaji Burkina Faso ba jinya ba, wannan irin murjewa haka? an uwar saurin hannu nan da nan ta kai mata duka. Amani ta goce tana tana ta dariya, Jal an na fadin na ga alama kin maida ni sa ar wasan ki, ni kike cewa na je honeymoon? Alhaji ya kammala wayar da yake yi ya rufe yasa a aljihu, yace Ya ki nan Uwa ta, kyale ta , sannan ya hau Jal an da fada, ni tunda nake ban taba ganin Uwa mai saurin dukan Da irin ki ba, to in bata yi wasa da ke ba da wa zata yi? Yar guda daya ita kenan Allah ya bani bazaki taya ni tattalin ta ba don ke kina da wasu ko? Amani tayi dariya ta ce ah Daddy, daina mata fada haka, kada ta yi zuciya taki yi min wasu kannen, biyu sun min kadan . Duk suka fashe da dariya har Mamman. Alhaji ya ce ta tashi ta koma cikin gida haka, don mai Martaba ya ce masa an gama ginin su, an saka komai, yau za a kai ta bangaren ta kafin wucewar su gida Katsina. Su kuma in sha Allahu gobe zasu wuce Nigeria. Tuni jikin Amani ya mutu, yar far ar data shigo da ita ta koma ciki, aure da rabuwa da iyaye ba wasa bane ba kuma sauki gare shi ba, damuwa da kewa suka bayyana a fuskar ta tun ma yanzu kenan, ta soma tunanin irin kewar su da zata yi tun basu tafin ba, musammamn Alhaji. Zata soma kukan tun kafin gobe ta yi, Ummami ta aiko jakadiya tayi kiran ta, don haka ta rike hannun Daddy tana hawaye ta rufa tafukan sa a kan fuskar ta, ta ce to yanzu Daddy ni da ku sai yaushe? Kai tsaye Alh. Usman yace sai kin haihu zamu zo, in kin min aboki ko sabuwar amarya, ki sa himma shekara mai zuwa sai ki gan mu gabadaya mun dawo radin suna, har Balewa zamu dauko miki da su Laure, da Kamilu Kunyar da bai san Amanin shi da ita ba ya gani ta zo ta lullube ta, harda kare fuska da hannayen ta cikin jin kunyar Daddy yau. Jakadiya da kuyangin ta suka maida Amani wajen Ummami, aka soma shirya ta don wucewa nata bangaren, wanda ke can gefen dama na masarautar Diffa. Da ka wuce sassan Sultan Issouffou Massaoudou. An kawata ginin a zamanance, hakanan ya tafi da zubin sarautar Al Imaraat Al-Diffa duk da haka. Daga ciki ne aka zuba abubuwa na zamani. Bangaren Maina Mukhtar Bn Issouffou Massaoudou dake ciki Al Imaraat Al Diffa wato masarautar Diffa, zan iya kwatanta shi da Palace din da babu kamar shi a duk cikin fadin masarautar, in ka cire sassan Sarkin Diffa. An shirya musu dakunan barci har shidda, da shigifu (faluka) na alfarma wadanda aka yi wa design da furnitures kala daban-daban, wasu an yi musu zubin royal parlors, wasu kuwa English parlors ne, da kuma Francaise. an na cikin hada kayan ta don gobe da asubah zasu kama hanya, Mai ya basu driver wanda zai kai su har Katsina sannnan ya dawo, Jal an ta ki yarda su yi sallama da Amani ta ce da Ummami a wuce da ita gidan ta kawai, ita bata son koke-koken banza na Amani, sannan duk wani abunda uwa zata fada mata ta san Ummami ta gama gaya mata, don haka Ummami tayi abunda ba a taba yi ba a masarautar Diffa, inda tace da kan ta zata kai Amani har dakin ta. A daren Mukhtar yana tare da Mai, suna cin abinci a kwano guda, yana masa hirar abubuwan da suka faru dasu a Burkina Faso da yadda aka magance lalurar Alhaji Usman ta suga da shanyewar jiki ta hanyar maganin gargajiya ziryan. Mai cikin gamsuwa da taimakon da aminin sa sarkin Burkina Faso yayi masa ya ce da Mukhy, ya saka an warewa Alhaji Usman Rakuma hamsin, a fara yi masa kiwon su anan cikin bargar Rakuman sa, in kuma yana so a kai masa su Nijeriya ne duk zai iya sawa akai masa har can, sannan ya bashi sittiru irin nashi na alfarma da rawanin sarautar Diffa akwati guda, har da zoben azurfa mai matukar daraja. Mukhy ya taya Alhaji godiya sai ya ce Uwa ta fa? Me aka tanadar mata? I mean ita me za a bata? (yana nufin Mamma Jal an). Mai ya ce ya bada bracelet na zinare a bata, har Baba Idi ma ya samu kyautar Rakuma goma daga Mai Diffa, Baba Sahura kuma Sarki yace Ummami ta ce a nan shiyyar Amani zata zauna tare da ita har sai ta saba da gidan da mutanen cikin sa koda zata koma Katsina. Duk da dai an bata wadatattun kuyangi da masu hidimar ta. amma zaman Sahura zai mata amfani. Mukhtar yana can suna wannan tattaunawar da mahaifin sa, ba tare da ya sani ba Ummami da Baba Sahura suka kai masa Amani dakin ta, bai san hakan ba don tun dawowar su bai nemi ganin Amani ba, kuma ko a hanya basu hadu ba, tunda yayi alkawarin daina kebewa da ita sai ta yi hankali ta kuma koyi son shi don radin kan ta, ya fahimci sai sun kebe ne take warware masa lissafi, da haka yake so ya koyawa kan sa hakuri daga shiga lamarin ta yanzu, ya fuskanci muhimman al amuran da ke gaban shi na taimakawa mahaifin sa kan sha anin mulkin sadon sauke nauyin al ummah dake kan su. Don haka yayi gefe da Amani daga ran sa (for the mean time) na yana so ta koyi son shi domin Allah ba don wasu material attachements, ko nasabar da take goranta masa ba. Daga wajen Mai, sai ya wuce suka yi sallama da su Daddy, yana jin wata irin kewar Alhajin nasa, Mukhy har da hawaye ya yi, ya fiddo wayar shi ya yi ma Alhaji hoto, yace Alhaji duk tsayin lokacin nan wai ace bani da hoton ka a waya ta . Dariya Hon. Ya yi ya ce to gashinan ka samu, sai ka ajiye in ka tuno ni ka dauko ka duba. Tunda ni da Uwa bama kama balle take tuna maka ni, Jal an da yake ta fini karfin jini ta kwace wannan . Da kyar suka iya rabuwa don dare ya fara yi, daga wajen su sai ya wuce sassan Ummami. Ya same ta tana shirin kwanciya, sai ta ce Maina tun dazu nake jiran shigowar ka in kwanta don na gaji da yawa, hidima kan hidima yau na sha ta har na gode Allah. Alhamdulillah tunda komai ya nabba a yanzu yadda na tsara Mukhtar ya samu kujerar sofa din ta ya zauna, ya ce ai ga ni yanzu, Sweet Mum, me zaki bani Ummami na? Budar bakin Ummami sai cewa tayi. Amanar diya ta Amina mana! Maina ka sani daga yau zaka soma rayuwar manyantaka, ka kasance mai hakuri da yi wa matar ka adalci da rangwame a kan duk wani ajizancin ta, kai ne babba sama da ita, don haka babba juji, bayan kasancewar ta matar ka yar uwar ka ce, jinin ka ce, da ta fi karfin kowanne uzuri a wurin ka Haka Ummami ta zaunar da Mukhy wajen awa guda tana masa wata irin nasiha mai ratsa zuciya, ta gaya masa ta kai masa Amani gidan sa yanzu haka Ya dan yi shiru na yan sakanni, ya rasa a yanayin da yake ciki, finally, shi da Amani yanzu! A gida daya, daki daya, kuma gado daya. Tsakanin farin ciki ko akasin sa, bai san wane ne yake nukurkusar sa a kasan ran sa ba, a can wani sako na zuciyar sa yayi kewar ta, a wadannan sati biyun da bai sanya ta a ido ba kuma bai ji muryar ta ba, duk da yake busy da kula da Alhaji, amma kullum sai Alhaji ya masa zancen ta, mai nuna yay aye mat aba don halin ta ba, mai nuna tsanannin kaunar da shimahaifin nata yake yi mata, wanda ke sawa ya kara mannata a zuciyar sa shima ko ya ki Allah balle yana son ta, albarkar Alhaji sai son yake ninkuwa kullum. Amma ba don ita ba, ba kuma don halin ta ba, sai don an jarrabce shi da son ta da kaunar ta tun kafin haka, (no matter how worse her behaviours are). A haka suka yi sallama shi da Ummami, yana jin kan sa kamar wani sabon mutum yau da ya mallaki matar aure a cikin gidan sa, kuma yar Alhajin sa, Amani Tafisu da zuciyar sa ke matukar so fisabilillah, ya shiga ratsa falillukan Ummami ya wuce zuwa sassan nasu, dogarai na faduwa suna gaida shi a duk kofar da ya wuce. Tunda Ummami ta ajiye ta a bakin gado bata sauya wajen zama ba, dan irin kukan nan na amare babu shi a idon Amani Faskari, idanun kemadagas, kamar soyayyar gyada marau-marau, amma damuwa da taraddadin haduwa da Mukhy yau, ta mayar dasu yan kanana, data gaji da lullubin ta sauke shi saman kafadun ta, ta daga kai tana kallon irin wannan dukiya da aka zuba musu a wannan daki don su biyu rak, ta dade a zaune tana godiya wa sarki Allah akan komai ma, musamman a kan
Chapter 14 · 0% Book details