Sashe 2
Amani Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
HYPERLINK "mailto:[email protected]" [email protected] 07030137870 TAFIYA ZUWA DIFFA asu iya magana suka ce tafiya mabudin ilmi, wasu kuma suka ce tafiya yankin azaba. To duka dai Alhaji da iyalin sa da yan uwan sa babu wanda basu fuskanta ba a hanyar su ta zuwa jihar Diffa ta kasar Nijar. Ga Karin ilmi suna ta samu a kan garuruwa da Baba Idi ke musu bayani kasancewar ya taba zuwa fatauci N guigmi daga Maiduguri tun yana saurayi, ga kuma yanayi na wahalar zafin ranar sahara wadda tasa hatta A/c din motar daina bada sanyi ta ke yi lokaci-lokaci saboda zafin rana da zafin rairayi irin na sahara. A hakan ma don sun yi zagaye ne ta Maine-Soroa da N guigmi basu bi ta cikin Bama din Maiduguri ba. Kasancewar sun fito tun asubah, tafiya non-stop, kuma mota lafiyayya, zuwa yamma sai gasu a cikin Maine-Soroa, makwabtan Diffa, anan ne suka tsaya suka yi sallah azahar da la asar da ta riske su a hanya, suka sayi gasashshen naman rakumi da madarar rakumi mai dumi sabuwar tatsa da sabon cukui a nan cikin garin Maine-Saroa suka ci, suka sha, Mukhy har Shayin su na Tubawa ya saya ya sha, dama kuma dai sun yo guzurin su yadda ya dace na abinci da abin sha, wanda tun dare Rakiya ta shirya musu suka taho da su, wadanda ba masu lalacewa ba, snacks ne da soyayyun kaji (pepper chicken), don haka basa tare da yunwa har suka shiga jihar Diffa. Shigar su garin ke da wuya komai ya soma kwancewa Mukhtar, (his in-born character) ya soma aiki a kan sa, ta yadda hatta gashin jikin sa dana kan sa sai da ya mimmike da duk wani gashi da ke jikin sa. Amani da ke gefen sa yana tuki, ta lura da yadda Mukhtar ke canzawa a yanayin sa da halittar sa, wata irin kamala da nutsuwa suka bayyana a tare da shi, suka lullube ainahin Mukhy saurayi nan dan gaye suka maida shi cikakken MOUKHTAR din sa, tsigar jikin sa har wani tashi take yi kamar mai jin sanyi. Jinin Issouffou Massaoudou ya soma circulating yana kurdawa a cikin jikin sa, yana sauya shi daga normal Mukhtar din sa da kowa ya sani zuwa Mainan Diffa na asali. Amani bata san me Mukhy yake kwancewa daga leda ba ta ga dai Mukhtar ya saka hannu ya janyo wani farin kyakkyawan tsohon amawali (rawani) daga cikin leda, ya kashe motar su a gefen titi. Rawanin nan ya hau nannadawa cikin iyawa da kwarewa, saida ya nade kyakkyawar fuskar sa tsaf, sai tsinin karan hancin sa da manyan idon sa ne kadai ya bayyana, kwatankwacin yadda taga nadi a fuskar mafi yawancin jama ar garin maza, wato nadin rawani irin na buzayen asali ko kuwa Tubawa, ko kuwa a kira su da yadda aka san su da shi wato Larabawan Diffa. Sai bata yi mamaki ba, don kuwa ta san cewa ba a canzawa tuwo suna, Mukhtar duk dadewar sa tare dasu, idan aka taho gida, shi buzu ne na hakika. Ya ja motar suka cigaba da tafiya. Baba Idi na tsokanar sa wato kowa ya bar gida-gida ya bar shi, kyawun kowanne tsuntsu yayi kukan gidan su . Mukhtar yayi dan murmushin miskilanci ta cikin amawalin sa, bai ce komai ba. Amma ya yarda da maganar Baba Idrisu cewa kukan gidan su har da kururuwar gidan su yake yi yanzu. Zuwa lokacin sun shiga tsakiyar gari, Amani ta bude hanci da ido tana shan kallon al ummar wannan jiha dake cikin janhuriyyar Nijar, ta fahimci cewa sittiru, kamanni na halitta da dukkan al adar su ta barranta da ta inda ta fito, suna ta gudanar da harkokin su na yau da kullum cikin sukuni da godiyar Ubangiji, domin kuwa al ummar wannan yanki na Diffa mafi yawa talakawa ne likis, masu abin yi daga kiwon dabbobi (livestock production), kasuwancin waje (export trade), jimar fatar rakumi da sauran su. Sun kuma kasance ma abota biyayya ga shuwagabannin su, wato sarakunan yankin Diffa. Shiga nan fita can Muktar bai manta hanya ba, bai manta ko ina ba, kamar wanda ake bankado komai daga cikin kwakwalwar sa ana nuna masa, kamar jiyan nan ya tafi daga Diffa. Haka yake ji yanzu da ya dawo cikin ta kamar ba shekara goma sha biyar ba, haka rayuwar sa ta baya ke rewinding kamar kaset din video a cikin kan sa, tana tuna masa duk abinda ya faru a baya. Sai suka hau wani mikakken titi dodar mai nisa, wanda daga shi Amani ta soma hango wani dogon kasaitaccen gini, wanda tsahon sa da fadin sa ya kai daidai da kilomeita (2,988), wani katafaren gini suke dosa wanda daga can sama aka rubuta da harshen larabci Al-iimaarat-al Diffa wato Diffa Emirate da harshen turanci. Suka cigaba da tafiya Amani na cewa a ran ta wato in ka zo garin, sai ka fara kaiwa sarki gaisuwa dole, kafin a bar ka ka tafi cikin gari inda ka zo. Can kuma ta ce Watakila kuma Baban sa bawan sarki ne, shi yasa ya tura shi birni neman kudi maimakon ya makale abin sa su yi bauta tare Ai kuwa ta kasa shiru, ta kasa barin tunanin ta a ran ta, lokacin da ta ga sun hau titi fetal wanda ya mika har cikin fadar Diffa. Masu tsaron babbar kofar masarauta ta farko suka tare su a kofar shiga, amma da Mukhtar ya sauke tagar sa, suka ga wannan nadin dake kansa da wannan amawalin da kuma tambarin da ke jikin rawanin, sai kawai suka daga musu kofa suka wuce ciki. Gasunan gasu nan har gate na biyu, shima kamar na farko daga ya sauke glass sun ga irin nadin sa da amawalin sa sai suka daga masa kofar masarauta suka nausa ciki. Daga nan sai gate na karshe, wanda shine na uku kuma daga shi sai fada. Anan ne aka dan takura da binciken bayan motar su kafin Mukhtar ya sauke glass, Amani na cewa Daddy ashe dan naka bawan sarki ne? Ko ko dan bayi ne ka ga duk sun san shi . Mamma Jal an ta kusa zagin ta, don ita jikin ta ya fara bata abubuwa masu yawa, amma Amani tana haukan ta irin wanda bata san ranar shiryuwar ta ba. Baba Idi ne ya ce mata shi dan bayi ba mutum bane? Ja ira marar mutunci . Sai tayi dif! Wani tsohon bafade tukuf, ya dogaro cikin kayan dogarai na jikin sarki sosai ya zo bakin tagar da Muktar yake, yace Samari, na gan ka da Amawalin gidan nan, Amawalin dana baiwa Mainan Diffa, amma ban shaida ka ba, ko zaka bude amawalin in gan ka sosai, kafin mu yi muku iznin yin parking a kofar fada? Sai kawai Mukhtar ya sa hannu yana warware rawanin kan sa, yanayi wa tsohon nan murmushi idanun sa fal hawaye. A hankali ya ce Baba na Katchalla! Tsoho Bafaden nan sai ya fadi kasa, yana fadin Allah ya taimaki Mainan Diffa, barka da dawowa hasken Diffa! Wannan batu da wannan tsohon bafade ke yi shi ya janyo hankalin sauran fadawa duk suka taho da gudun gaske, wajen hannu goma ne ya budewa Mukhtar kofa a gigice, suna faduwa suna tashi suna fadin Hasken Diffa ya dawo, barka da dawowa hasken Diffa, barka da dawowa tauraron Diffa, Maina ka sauka lafiya ka taka a hankali Allah ya kare tauraron Diffa, haske maganin duhu, hadari malafar duniya Daga nan aka bude musu kofa a ka bazawa Mukhtar babbar riga aka kareshi ya sauko daga motar. Tuni har wani ya sheka labari cikin gida wai ana tsammanin Mainan Diffa ya dawo, zancen nan nan da nan ya isa kunnen Sarki Issouffou Massaoudou, wanda ke kwance a turakar sa a lokacin bayan ya sha magani, ya soma shirin dan mikewa ya kwanta kafin lokacin da zai fita fada. Sai ga wayar sarkin fada wanda ya manta shekaru nawa rabon da ya kira shi a waya, don a ka ida fadawa basa kiran sa a waya. Kamar bazai dauka ba amma sai yayi tunanin banza bata kai zomo kasuwa haka kawai Katchalla ba zai kira shi ba, sai ya daga. Yana dagawa kuwa sarkin fada ya fashe da kuka yana fadin nayi rantsuwa da Allah ga Maina ya dawo, ka san dai cikin kowanne hali bazan kasa gane shi ba ko da bai zo da rawanin sa ba Sarki Issouffou Massaoudou a kwance yake, amma sai ganin sa yayi a bakin kofa ya manta cewa jar hula ce da ake kira Dara da rigar shan iska mara hannu kadai a jikin sa, ya kama hanyar kofar da zata sada shi da hanyar fada. Fadawan da ke tsaron kofa sun kidima da ganin fitowar Sarki a haka yana ta surfa uban sauri, aka kuma rasa wanda zai tare shi ya tuna masa babu amawali da alkyabbar sa a tare da shi. Farin dattijo amma ba tukuf ba, kyakkyawan Balaraben Diffa na gaske wanda yawan shekarun sa bai boye kyawun surar sa na lokacin kuruciya da tsananin kamannin sa da Mukhtar ba. A lokacin har an shigar dasu Mukhtar fada, baka jin komai sai tashin kirarin da fadawa ke zubewa a kasa suna yi masa. Hadari malafar duniya, hadari sa gaban ka inda kake so, gaba salamun, baya salamun, haske maganin duhu Zaki dan Zaki, Majina gishirin yaro, tsawa mai ratsa gidan arna. Kunun bagaruwa cika ciki har makogaro. Dan Sarki jikan Sarki kuma sarki mai jiran gado. (Wannan kirari ba da hausa suke yin sa ba, suna yin sa ne da vernacular language din su wato Chadian Arabic daya daga cikin yaren Diffa Arab). Wani babban bafaden kuma yace Zakin duniya makiyanka fadawan ka, ana kin ka ana rusuna maka, ba yin kan ka bane yardar Allah ne da addu ar iyaye ya dawo mana da kai. Allah Ubangaji ga Mukhtar dan Issouffou Massaoudou ya dawo gida. Hasken Diffa ya dawo, duhu ya yaye! Amani da iyayen ta da ke kallon abinda ke faruwa kamar a majigi, sun kasa ko motsin kirki. Amani ta lura hatta tafiyar Mukhtar ta canza kan ta da kan ta, ba irin wadda yake yi a baya bace. Me ke faruwa ne haka a gaban idon ta? Wanene wannan Mukhtar din? Wane al amari