Sashe 17
Amani Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
mata ba, ko da sadakan ne don samun nutsuwar sa. Shi yasa muka ga gara a bashi sadakan ko ba yawa kafin ku daidaita kan ku, da sabanin da ke tsakanin ku, ki sani Mukhtar Sarki ne, halittar su daban da ta sauran maza da kika sani a kan mata, kusan in ce miki, duk yawancin sarakuna. A shekarun Mukhtar yayi hakurin da ya zarce kima babu mace, gara kada a kure hakurin a bashi karin wasu matan na hutawa, su kuma yi muku hidima ke da shi har zuwa ku daidaita Ko ita dakikiya ce zuwa yanzu ta fahimci me Ummami ke nufi yanzu, tunda dai ta shiga aji, ba wai bata taba shiga aji ba. Gata suke nufin zasu yi wa dan su, don sun gane bata bashi kulawar data dace mace ta baiwa mijin ta na auratayya. Kasa magana tayi, tayi kokarin rike hawayen ta bata bari sun zubo a gaban Ummami ba, don kada a ga rashin juriyar ta da raunin ta, sannan ta mike ta koma sassan su cikin sanyin jiki, sai Kuyangar ta mai kula da kitchen wato Ramu ce ta biyo ta da wayar ta, don a can dakin Ummami ta manto ta tsabar ta shiga rudu mai yawa, kuma Ummami bata sake bi ta kan ta ba, bayan bayanin da ta yi mata. Ta san ta ahada mata bom yadda take so ya tashi. Duk da sanyin AC mai karfi da ke aiki a falon ta. Amma Amani zufa take yi in ta tuno zancen nan. Idanun ta ba abunda suke hararo mata sai kyawawan yammata abzinawan usli tare da Mukhtar, cikin irin yanayin su da suka kasance jiya shi da ita, wannan al amari ba karamin daga hankalin Tafisu ya yi ba. Fisabilillah me yasa ba a yi ma Mukhtar aure tun sanda ta tsane shi ba sai yanzu da ta soma saka shi a ran ta, ta soma tsara musu rayuwa ta soyayya mai tsafta a cikin zuciyar ta, kiris ya rage mata ta samu dama ta bayyana masa son da take masa? Mafarkin ta na haifa ma Ummami da Mai Diffa jikoki daga Mukhy ita kadai ran ta, ya tashi a banza Kenan muddin aka bashi wasu matan suka riga ta shiga jikin sa? A hankali ta soma sheshekar kuka, bata san cewa Mukhy yana cikin dakin da ta jingina da kofar sa ba. Sautin kukan ta ya dame shi, yana ci masa rai, don bilhaqqi take yin sa, hakan ya fiddo Mukhy daga dakin barcin nasa, ya bude kofar saura kadan ta fadi, don a jikin kofar ta jigina duka jikin ta, tunda ya baro su ita da Ummami gidan sa ya dawo, ya kwanta a daki ya rufe kan sa yana tunanin karbar tayin mahaifin sa ne ko a Ita bata ma san yana ciki ba, ya zo kan ta cikin fushi dama kuma ran sa a bace yake da abinda ta yi masa gaban Ummami mai kama da raini, cikin tsawa ya ce ke lafiya zaki zo ki daga min hankali da kuka haka ina kokarin samun barci? Me aka yi miki? Wani aka ce ya mutu? Koko rashin hankalin ki da kika saba? Amani ta daga jikakkun idanun ta ta galla masa hararar nan tata da ta dade bata yi masa irin ta ba. Sai yau da ji take gabadaya ta tsane shi bata ko son ganin shi a idon ta. Sannan ta juya tana share hawayen ta don bata so ya kama ta tana kukan nan ba, ko don tsira da sauran ajin ta, ta yi masa banza ta cigaba da share hawayen ta da habar laffayar ta. Ba gara mutuwa ba ta san kowanne mai rai mamaci ne. Wannan kuwa tashin hankali ne na har abada ya same ta, in har ta bari ya faru, kishiya daga zuwan ta gidan miji! Mijin ma Mukhy dan uwan ta da ta soma kallafawa a ran ta bada jimawa ba, wanda bata kwatantashi da komai a yanzu, son sa take bilhaqqi. Mukhtar ya sassauta murya ganin cewa fada da daure fuska bazasuyi tasiri a gare ta ba, har ya samu ta gaya masa kukan me take yi, ya ce pls Amani! Na hadaki da Allah ki yi shiru, ki gaya min abinda ya yi sanadin wannan kukan babu gaira babu dalili Don sosai ta firgita shi, don kukan nata ba na wasa bane yau, ko na sakarci irin wanda ta saba a yawancin lokuta, a ah wannan kuka ne mai fita daga kasan zuciyar matar da ke tsananin son mijin ta, kuma dare daya ya zo ba zato ya ce zai mata kishiyoyi, kuka ne take yi bilhaqqi, baka da zuci, mai nuna tsananin kishin ta akan abinda take so da zuciya daya. A matukar fusace Amani ta dago, idanun ta sun yi jawur, hawaye ya hade da majina ta ce ina rokon ka Allah Annabi ka bace min da gani Ya Mukhy, sabida bana son ganin fuskar ka, ka tafi gun sadakan da ka je ka roka a baka sabida na gaza, ka tambaye su kukan me nake yi, tunda kai baka da hakuri, baka da bin komai a sannu. Son da na samu kaina da fara yi maka, ina rokon Allah ya sa ya koma inda ya fito, kada Allah ya bar ni da koshin wahala Mukhtar ya hadiye mamakin sa da dariyar data zo masa nan take, sai yanzu ya gane musabbabin kukan, wanda bai taba ganin Amani na yin mai zafi da cin ran sa ba, ya ce. Tafisu yau ni kike kira mara hakuri? Shin a duniya akwai miji mai hakuri ma iri na? Ni da aka kira bawan Alhaji, mara galihu, mara nasaba kai har mai kama da shegu an ce min kuma na yi hakuri na Manzon Allah, ban taba kallon ki da kalaman bakin ki ba, sai matsayin diyar ubangida na mai daraja a idanu na. Ni tsintacce a bola, ke komai ma na batanci da rashin galihu ni ne. To ki gayamin ya kike so in yi idan ban karbi wadanda zasu so ni a yadda nake ba? Ke da yake yar Qaruna ce kin ki yarda mu daidaita kan mu har yanzu, sabida baki son yaron Alhaji, ni kuma iyaye na na na son ganin ya na da wuri, Maimartaba kuma na son gani na cikin nutsuwar data dace da kowanne dan gata. Kullum in naje fada bani da nutsuwa in na ga babu yan Mai ko daya bayan ni, ina son samun yara wa iyaye na yara masu yawa, tun da su Allah bai basu ya masu yawa ba. Ki fada min yanzu da lafiya ta da komai, an yi mana aure ya kusa rufa watanni nawa amma har yanzu ban san irin nawa ba, Tafisu zina kike so in je in yi in ban karbi kyautar sadakoki ba? Ko kuma durkusa miki zan yi in roki alfaramr ki so ni, ki kuma bani hakki na? Ai gara sa-dakan, ko ba su nake wa Son da nake yi miki ba, a kalla zan dinga rage zafin da kike kunsa min dasu Amani ta zuba masa jikakkun idanun ta da ke zuba cikin tashin hankali, bata ko kyaftawa, bata taba zaton Mukhtar zai iya wadannan maganganun ba, Mukhy mai kawaici da kamewa. Mukhy ya kalle ta yana murmushin tura haushi, ya kara guma mata da cewa. Kuma banda abun ki, banda shirme irin naki Sadaka ai ba matan aure bane na hakika a wurin sarakuna, da zaki yi kishi da su, kada ki damu ababen hutawa ne ga sarakuna kadai Amani na neman zaucewa yanzu ta ce au, bama daya bane har nawa ne ka roko? Yace na roka ko aka bani kyauta? Su biyu ne kawai aka kawomin daga Sultanate of Damagaram A wannan gabar Amani ta kusa dawowa tsohuwar Amanin ta yanzu, domin jijiyoyin rashin kunya sun mimmike, tsigar jikin ta har tashi take, manyan idanun ta suka firfito waje, ta ce. Mukhtar! To kai din wane irin jarababbe ne da za a kawo maka mata biyu a lokaci daya? Plus me, three? Kwatakwata shekarun ka nawa? Mukhtar ya buda hannuwa irin na (ba matsalar ki bace) ya ce har goma in ina so zan hada a lokaci guda, in kika bani dama ko yanzu sai ki ga irin jarabar tawa Ya soma tunkaro ta, idanuwan sa na nuna yau ba mai raba shi da Amani sai Allah yana balle botirin wuya da links din hannun farar shaddar jikin shi, ta ce. Allah ya suwake in hada miji da wasu, wallahi sai ka maida ni gidan Uba na, kafin ka karbo su, ai ba kai kadai ne dan gata ba, nima nan da kake gani na TAFISU ce har yanzu har gobe, bar ganin na yi sanyi, ina nan a Tafisu na da ka sani in aka tabo ni. In banda mugunta na taba cewa kada ka kusance ni? Ko kuwa ba kai kake dakatawa don radin kan ka ba da son saka ni a damuwa Ya Mukhy? Za dai ka karba ne don ka sanya ni a bacin rai, don ka ga na fara son ka Mukhtar ba don komai ba! To idan so cuta ne to hakuri magani ne! na barwa sadakoki kai, ka maida ni inda ka dauko ni gobe goben nan . Ta rushe da kuka, ta ce wallahi Katsina zan koma wajen iyaye na, sai dai ka zaba ko ni ko sadakoki, ai da aka bar ni a nan ba wai an ce gata na ya kare bane Mukhy, yau ji yayi kamar yayi juyi a gaban ta don dadi, murmushin da ke kan fuskar sa sai karuwa yake, for the first time ya fahimci Amani ta fara son sa don radin kan ta, ba abinda yafi dadi ga da namiji irin ya fahimci matar sa na tsananin kishin sa irin haka, yau ga Tafisu na kukan kishi a kan sa kamar ta shide. Niyyar sa da farko shine ya rungume ta, ya lallashe ta ya sumbace ta son ran sa daga nan koma me zai faru ya faru yau, in yaso gobe yace a bar sadakokin baya so, ya yi amfani da wannan damar ya gaya mata cewa son da yake mata mai yawa ne da ya isa