Sashe 12
Amani Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
mutum. Don haka yar uwa bamu makara ba zamu samo kan Yaya Mukhy din mu, ke dai ki tabbatar kin canza din da gaske kuma da zuciya daya, ki kuma tabbatar masa da canjin naki ta hanyar nagartattun halaye sababbi da zaki yafa yanzo, ki koyi bayyana soyayyar dake zuciyar ki a gaban sa da ladabi da biyayya, Sahibah ki nuna kulawa koda zai miki wata fassarar, to na dan lokaci ne, don na tabbata Mukhtar na son ki Da sauri Amani ta damke wayar ta sosai a kunnen ta, hawayen farin cikin kalaman Balewa ya tsirgo mata ta ce da gaske kike Hamida Mukhtar yana so na? Kuma zai cigaba da son nawa bayan duk abubuwan batanci da tozarci da na yi masa? Zai cigaba da son nawa bayan ya dawo cikin gatan sa, ba zai fassara ni da wata fassarar ta daban ba? Hamida har ce masa na yi yana kama da .. Astagfirullah bana so in maimaita don na koyi sakawa harshe na linzami Maganar ta yi wa Hamida gingiringin, amma ta san Amani neman wanda zai kwantar mata da hankali ta a ke yanzu, shi yasa har ta neme ta, tana neman mai bata support da assurance na cewa in ta gyara kurakuran ta za a yafe mata, tunda ta ce ta koyi sarrafa harshen ta ta hanyar yin furuci mai kyau ga kowa, ance matar na tuba bata rasa miji. Hamida tayi ajiyar zuciya. Sun tattauna extensively kuma heart to heart yadda ya kamata aminai na kwarai su magantu, a kan wata mas ala data sha kan dayan su. Hamida ta gaya mata cewa har abada Mukhtar ba zai guje ta ba, ta gaya mata dalilan ta; inda tace bayan soyayya ta jini akwai soyayya gangariya a zuciyar sa a kan ta. Sannan ta gaya mata wasu maganganu na sirri na yadda zata nunawa Mukhtar cewa da gaske ta canza da zarar sun tare a gidan su. Amani da Hamida yau sun raba dare suna tattaunawa kuma Hamida ta taya ta murnar duk abubuwan da suka faru din. Kuma ta ce zata zo har dakin ta a Diffa watarana idan Allah ya nufa. Tun daga ranar dokin ta ga son dawowar Mukhy ya karu, har practicing/rehersing yadda zata yi masa sannu da dawowa take yi, da irin kallon da zata ke masa mai nuna kunya da ladabi ba irin na baya ba da take ware idanuwa ta zuba masa harara, yadda dai Hamida ta gaya mata, ya zama duk dare da tunanin Mukhtar ta ke iya barci, ta kuma gan shi cikin mafarkin ta, a yanayin da take kwadayin ganin nasu. Ummami bata san hakan ba ita, domin ta koma fara yi wa dan ta yakin neman soyayya, a fakaice (kamfen). Daga ranar data fara koyar da Amani karatu, in suka yi karatun addini suka gaji don ko wajen Mai bata zuwa sosai yanzu kullum tana like da Amani, don ta fahimci itama irin Mukhy ce ba soyayyar uwa ta tashi, gara ita ta samu ta uban shi kuwa fa? A kokarin ta na son kara cusa soyayyar tilon dan ta a zuciyar yar uwar sa kuma matar sa, tunda ta ji yaa ce bata son sa duk da ta musanta hakan, sai ta ga bari tayi amfani da damar wajen fayyacewa Aman tarihin Mukhy wataila hakan yasa ta tausaya masa a matsayin ta na yar uwar sa, tausayi da fahimta ta sani suna tasiri sosai wajen kimsa SO. Don haka rannan bayan sun gama karatu na addini da Karin Al ani da take mata kullum sai Ummami ta sako zancen Mukhtar. Tace Aminatu kin san labarin mijin ki Maina? Cikin jin yar kunyar gaske da ta fara samun muhalli a tare da Amani yanzu, ko da yake in bata kunyar kowa tana kunyar Ummami, ta sunkuyar da kai, a lokacin tana taje ma Ummami dogon gashin kan ta da furfura ta soma samun muhalli, Ummami ta ce ta raba shi gida biyu ta yi mata tufka biyu ta gaji da shi a tsefe, mai kitson ta ta yi tafiya. Amani ta ce. ah Ummami, ni dai kawai na tashi na gan shi karkashin kulawar Alhaji na, ban san inda ya samo shi ba kuma ban taba tambayar Daddy ba don bama jituwa ni da Yaya Mukhy ko kankani, shi baya son hali na nima bana son nasa, shi yasa kika ji yana cewa wai bana son sa! Ta karasa fadi cikin karamar murya mai nuna kunyar idon uwa, amma gara ta gaya mata gaskiya a kan ta ci gaba da rikon ta a ran ta a kan bata son Mukhy, ba uwar da zata so a ce dan ta na auren macen da bata son sa sai dai ta yi kawaici, idan mai kawaicin ce irin Ummami kenan. Ummami ta gyada kai ta ce wato Amani, a duniyar Subhana ina tsananin tausayin Mukhtar Amani, shi yasa nake so kema ki tausaya masa, ki bashi soyayya wadda ban bashi ba, ki jiyar da shi dadin da mata hudu zasu jiyar da shi a lokaci daya, ki kuma kula da shi da rayuwar sa yadda nake kokari akan mahaifin sa ba don bai da wasu matan ba. Ummami ta nisa, sannan ta cigaba da cewa kin ga yadda ya bar gida duk gatan shi a shekarun balaga, a shekarun da ya dace a ce yana kusa da mahaifin sa a fadar sa yana koyar da shi sha anin mulki, amma ya zabi ya tafi uwa duniya sabida rashin samun kulawar iyaye. A hakan ma don baki san irin rayuwar da yayi tare da yan bayi, a kuma sassan bayi ba Idanun ta ya ciko da hawaye ta ce shi da ni sai dai leke daga nesa, ban taba goya shi a baya na ba, duk hakan bai isa ba aka zo aka bi shi da mugun asiri wai kurciya ya kara yin nesa da gida, kuma Baban sa bai damu ba ya cigaba da gudanar da harkokin mulkin sa rai kwance hankali kwance. A kan idanuna babu irin gatan da bai yi wa yan uwan sa mata Sayluba da Sa adiyya ba. Tun ba lokacin auren su ba. ya zaba musu mazaje na fita tsara ya kuma yi musu auren gata. Kema kin san kafin uwa ta jure wannan kin san akwai wuya, meye laifin Maina don kawai ya zo a namiji? Amma haka na jure don farantawa miji na bisa ra ayin sa, ban taba kalubalantar sa ba tunda aka ce abinda babba ya hango yaro ko ya hau rimi ba zai hango ba. Kullum jakadiya ta kawo min shi don in shayar da shi, nuna mata nake bana so, in ta isheni da roko sai in karbe shi, amma kuryar daki nake tafiya da shi ina shayar da shi ina kallon shi ina kuka. Ya kan kura min ido kamar yana tambaya ta dalilin mu na yi masa haka .??? Ummami ta share hawayen da suka kawo a idon ta, itama Amani zuwa lokacin nata idon ya ciko da kwallah, ta cigaba da cewa na san yana leken mu a shigifar sarki ko wajen hutawar sa da yamma a yawancin lokuta, wanda ba komai ke kawo shi ba sai bond din nan na soyayyar iyaye, wannan yasa na ke yawan zuwa wajen da Mai yake hutawar yammaci, dan mu yi sallar la asar tare, in mun idar in yanke masa akaifa ko in taya shi hira yana daga zaune bida karagar sa ina daga kasan kafafun sa cikin ladabi mai yawa, ba don komai ba sai don in ya zo leken namu nima ina samun damar ganin sa a sace. Ranar da aka ce min ya gudu ni na san dalilin sa, na kuma yarda da hujjar sa, tunda bamu taba zama da shi mun masa bayani, wanda zai gamsu da hujjar mu ba, don haka duk abinda zuciyar sa ta gaya masa ko ta fassara masa a kan mu a wancan lokacin a wurin sa shine dai dai. Suma na dinga yi ba tare da kowa ya san dalili ba, ana zuba min ruwa ina farfadowa. Daga ranar kuma ban kara sallah na tashi ban yi masa doguwar addu a ba, kan cewa duk inda ya shiga Allah ya zama gatan sa, ya kare mun shi da karewar sa da kiyayewar sa, ya kuma kula da shi. Domin na yarda kulawar Ubangiji tafi tamu ta iyaye, kuma itace ta kawo Mukhtar yau inda yake. Ya yi rashin duk wata soyayya ta iyaye a kuruciyar sa, ina jin damuwa idan na tuna hakan. Da wannan nake rokon ki, a kan ki dubi girman Allah ki kula min da Mukhtar kin ji AMINA! Ko da a kasan ran ki babu soyayyar Amani sai ta saka kukan data ke rikewa tun dazu a bakin ta, kuka mai sauti sosai, ta rasa abinda zata ce da Ummami wanda zai sa ta gamsu ba ta kin Mukhy yanzu, it s true Mukhy had a traumatic childhood, and he deserve happiness a yanzu. Matsalar ta da shi riko . Ya ki sakin ran sa da ita su mori auren da kuruciyar su sai tsananin rikon ta da laifukan na baya da ya bari suka yiwa ran sa kaka-gida. Ko yayi kokarin sakin ran sa da jikin sa da ita wani time din, rikon dake zuciyar sa sai ya hana shi. Bayan rayuwar bakidayan ta sai ana ma juna afuwa, saboda rashin tsayin ta da rashin tabbas din ta. Life is very short and transient . Amma ai Allah ya san ta yi nadama, wadda ba lallai wanda ya santa a baya ya karba ba, za a ce ne don ta gan shi da gata ne a yanzu. Don haka ta hadiye duk wani tunani a ran ta, nadamar ta da damuwar ta a kan Mukhy bata iya ta cewa Ummami komai ba, sai sheshshekar kuka take tana hadawa da ajiyar zuciya. Ummami ta ce to yanzu meye abin kuka daga magana? Ni labara kawai na baki don ki tausaya masa. Ba don in saka ki kuka ba. Koda yake Jal an ma haka take da saurin kuka, da abinda ya isa a yiwa kuka da wanda bai isa ba duk abin kuka ne a wurin ta tana karama, kin