← Book details Amani Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 4 OF 19

Sashe 4

Amani Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

bari a wulakantani ba, wai don nayi laifi na kuma gane na yi laifi na tuba. Mamma don Allah ki hyi hakuri ki sa min albarka Mamma ta kora ruwan tataccen inibi a tambulan na tangaran mai garai garai ta dube ta yanzu da rahma a idanun ta, ta ce idan da gaske kike kin tuba, Shi Ubangiji mai afuwa ne kuma yana son masu yawan tuba daga laifin da suka san sun aikata. Ni kuma zan taya ki da adddu a a kan Allah ya huwwace miki zuciyar sa, ya baki dukkan soyayyar da ke zuciyar sa, ya kade fitina a zaman ku, ya baku zuria mai albarka Amani ta ruga da gudu ta rungume Maman ta tana na gode Mamma, na gode sosai Sun kwana suna tattauna al amarin nan cikin tu ajjibi da mamaki iri-iri, Mukhtar dan baiwa ne hakika, wanda bai taba alaqanta kan sa da wata daukaka irin haka ba a inda ya tabbatar ba a san ko shi waye ba, amma hakika wasu attributes nasa da yawancin personality din sa masu tsinkaye a cikin su irin Mamma, sun ce sun sha alaqanta shi da babbar sarauta ko babbar nasaba. Suka kwana hira da tsarkake tsarkin mulkin Ubangiji. **** **** ***** Haka suma Uba da dan da mahaifiyar sa, sun kwana tare a turakar Sarkin Diffa, kamar su maida dan nasu Mukhtar cikin su. Wani abu ne da Mukhtar bai taba samu tare da su ba tun haihuwar sa, wato closeness sai yau. Don haka (he can t control his tears). Maina ina ka je? Maina ina ka shiga? Maina ka bar mu, shekara goma sha biyar ba kwana goma ba Maina in ji Ummami, tana share hawaye da gefen laffayar ta. Ummami I thought kun fi son hakan, kun fi son in yi nisa da ku din, ba kwa so in rabe ku, kamar ba ku kuka haife ni ba. Na yi kokari na jure hakan tun haihuwa ta amma dana fara girma sai abun yake neman zame min ciwo a zuciya ta, dole na zabi in tafi in yi rayuwa a inda bazaku ko samu labari na ba, tunda zamana tare da ku bai da wani amfani a gare ku. Daga baya kuma kullum na yi kokarin juyowa gida bana iyawa sakamakon dabaibayin dake zuciya ta. Rana daya Allah ya yaye min wannan dabaibayi, naji hankali na ya yo gida, I m so sorry Ummami, har aure na yi babu jimawa bada sani da yardar ku ba, but I have no choice, saboda mahaifin ta has been my savior, my shelter for a very long time Nan ya gaya musu cewa bayan ya karbi kwalin kammala karatun sakandire tare da yan bayin gidan a makarantar gwamnatin Diffa da yayi ya kasa cigaba da zaman kasar Nijar, ya yanke shawarar shiga duniya ya nemi ilmin da zai taimaka masa ya dogara da kan sa. Tunda sun nuna basa bukatar shi a rayuwar su sun bar shi a bangaren bayi yana rayuwa tare da yan bayi, karkashin kulawar Jakadiya da mijin ta Sarkin fada, wato Bafade Katchalla wanda shi ya fara gane shi yanzu ma da ya dawo. Ya ce tunda na taso na ganni a hannun jakadiyar Ummami, ita ta raine ni, saidai lokaci lokaci ta kaini gun Ummami ta kuma dawo dani bangaren da take wato bangaren bayi. Dana fara girma, ma sai ta rage kai ni gun Ummami, itama ba koyaushe take wuni da ni ba tafi wuni a cikin gida, sai dai in yi ta wasa da yaranta maza guda biyu sa anni na, sai na dauka ma su suka haife ni wato ni dan jakadiya da Baba Katchalla ne, musamman da suka saka ni a makaranta tare da Shettima da Ari, wato yan su, muke zuwa tare kullum muna dawowa. A hakan sai na fara mantawa da Ummami, wadda nake gani lokaci lokaci, kai kuwa Maimartaba dama ba a zancen ka, don tsakani na da kai sai dai in hango ka a turakar ka ko a fada, ko a kan Rakumi idan ana wani festivities din kamar misali bikin sallah ko na aure ko na nadin sarauta. A baya Baba Katchalla na zuwa da ni fada mu zauna a gefe nida shi, bazan manta ranar da kayi masa tsawa ba, ka ce kada ya kara kawo ni fada, mai bakin baya ne ni, tunda ga kai na ko batan wata ba a kara yi a gidan ka ba. A ranar ne ma wasu a fada suka san ni dan Sarki ne. Nan ne aka yi ta kuskus a gari wai ashe Sarki yana da Da namiji amma baya son yaron. Ya barwa bayi shi. Wannan zance har a makaranta an yi min gorin sa, lokacin ina karatun sakandire. A wani dare na tsuye jakadiya ina tambayar ta da gaske ni dan sarki ne? Kuma Mowar Sarki wato Ummami da muke zuwa wajen ta lokaci lokaci har wani lokaci ta bani apple ita ce mahaifiya ta? Jakadiya ta tabbatar min haka ne, amma bata san dalilin ku na ajiye ni tare da su ba, kodayake tace Sarki da Mowar gida basu da trusted servants a cikin bayin su kamar ita da Katchalla. Tace Sarkin Diffa ba mai yawan haihuwa bane, shiyasa yake ta aure daga kasa-kasa don ya samu haihuwa, a irin haka ne ya auro mahaifiya ta daga wata kasa cikin kasashen Afrika, yan sa biyu kacal kuma duk mata ne tare da matar sa ta lalle wato uwargidan sa da mai bi mata wato mata ta biyu. Daga kan su bai kara samun haihuwa ba sai da ya auri Ummami, kuma tun haihuwa ta suka bata ni, shayarwa ma a boye Ummami ta shayar da ni don sai ta bita cikin sirri ta roke ta. Bayan ta yaye ni ma kuwa bata bukatar a kai mata ni inda take. Ni ne dai dana yi hankali na ji ba wanda nake so a duniya irin ki Ummami, sai nake satar jiki ina zuwa inda kuke, wani lokacin inna leka inda kuke zama da la asar zan same ku kuna sallah tare ke da Sarki, ko kina zuba masa abinci ko kina masa yankar farce, har rannan wani bafade ya kama ni ina leken ku ya taska min mari, shine fa ban kara leken ku ba daga ranar. Watarana Baba Katchalla yace muje ana bikin Yaya ta a cikin gida, nan na bishi muka je har fada naga irin auren gata da aka yi wa yar uwata, akan taguwa aka kai ta Tahoa inda ta auri dan sarkin Tahoa, ni kuwa inna shiga cikin gidan na hau rabe-rabe kenan kamar mara gaskiya, hatta sittiru na tare ake din ka mana da Ari da Shettima, babu wani banbanci tsakanina da su. A makaranta ma ajin mu daya da su. Dana fara hankali sai nake tambayar kaina to meye dalilin hakan da sarki da Ummami suka zabarwa rayuwa ta? Na sa a raina bakin bayan da ya taba ambata min ne dalili, wato daga kaina ko batan wata wata matar sa bata kara yi ba har ita Ummamin. Amma ai wannan bai isa dalilin da zasu sarayar da rayuwa ta a hannun bayin su ba, sai ma dai yayi dalilin da zasu daukaka daraja ta fiye data kowa a masarautar. Bani da wata shakuwa ko kusanci da ku da zai sa na iya yi muku wannan tambayar. Ban ma isa in je inda kuke kai tsaye ba. Na yarda iyaye na kun haife ni ne da gaske, amma kuma baku kauna ta! In na tuna hakan sai wani irin bakin ciki ya murde ni, har ya zame min habit, daga baya bayan na kammala sakandire na ji bazan iya cigaba da zama a Diffa ba, gara in tafi inda bazaku kara jin labari na ba, tunda kun haife ni bisa kuskure amma bakwa kaunata ko miskala zarratin. Wannan abu ya cigaba da bakanta min dare da rana, har na koma tamkar depressed, na daina walwala, na daina shiga cikin sa anni na, na yarda bakin baya na zai iya shafar kowanne yaro iyayen sa su tsane shi. Duk da babu abinda Baba Katchalla da Jakadiya suka raga min, suna ma kula da ni ne har fiye da yadda suke kula da yan su Ari da Shettima. Rana daya na yanke shawarar barin Diffa, to amma ina zani bani da ko sisi? A hakan ne aka ce sakamakon mu na sakandire ya fito, kuma na ci jarrabawa ta da sakamako mai kyau wanda yafi na kowa, don haka gwannatin kasar Nijar ta dauki nauyin karatun mu ni da wasu dalibai zakakurai iri na zuwa kasar goyon mu wato Faransa. Aka damka min admission dina da tikitin jirgi, na so in gayawa Baba Katchalla amma zuciya ta ta kwabe ni, kan cewa zai iya hana ni tafiya, ku kuwa dama na san ba damuwar ku bace rayuwa ta ce, baku da matsala da wannan, hasalima na yi amanna farin ciki zaku yi in yau aka ce na bar Diffa. Hatta malaman makarantar mu basu san cewa ni Maina ne ba, sun dauka ni dan bawa Katchalla ne wanda kusan kullum shi yake kawo mu makaranta ya kuma zo ya dauke mu. Don haka da aka fara jigilar daliban da suka samu scholarship na sulale na tafi Agadez tare da sauran dalibai yan uwa na, inda daga can jirgin mu ya daga zuwa France. Acan ne aka rarraba mu zuwa jami I daban daban a cikin Faransa, ni aka bar ni a Jami Paris Saclay University ***** **** **** RAYUWA TA A FARANSA ayuwa ta a matsayin dalibi a birnin Paris, rayuwa ce irin ta kowanne dalibi mara gata sai na gwamnati, mai fafutuka da neman ilmi da gumin sa, gwamnatin kasar mu na bamu alawus wanda da shi muke rike kan mu. Na yi wani dogon rashin lafiya bayan tahowa ta kamar bazan rayu ba, don sai da na kwashe watanni biyu a asibiti bansan inda kaina yake ba, bayan na farfado da kyar, na ji a cikin kaina bani da buri irin na kara nesanta kaina da gida, kuma har Paris din ji nake ta min kusa da Nijar amma hakika ina son samun kwalin degree dinnan, shiyasa na tsaya. Da kyar na samu
Chapter 4 · 0% Book details