Sashe 15
Amani Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
iyayen ta da suka koma auren su, sai kuma ta tuna bata yi sallahr isha ba, don haka ta tashi da sauri ta shiga inda take tunanin toilet ne, don yanzu bata wasa da lokacin sallah ko kadan sabida nasihun Ummami. Ta idar da sallahr tana addu a ta ji motsin shigar sa dakin da ke kallon nata. Kamar ta je, kamar kada ta je, ta tunawa kan ta cewa ita fa amarya ce no matter how, Mukhtar shi ya kamata ya zo inda take duk mulkin sa. Don haka ta daure ta cigaba da zama akan dardumar da tayi sallah, daga baya tun tana addu a a kan Allah ya gyara mata halayen ta da kowa ke kuka da su, har barci ya dauke ta a kan sallayar. Mukhtar na nasa dakin har washegari yana barcin gajiya, haka kawai zuciyar sa bata amince ya je ga Amani ba, ko ya so hakan zuciyar ta ki amincewa, haka kawai ya koyi juriya daga shiga al amarin ta. Basu suka hadu cikin gida ba sai da safe a falon sa na farko, ta fito cikin sassaukar shiga ta atamfa Holland, ta yi daurin kai dai-dai misali ba irin daurin ta na baya da ta saba yi ba wato Ture ka ga Tsiya yau daurin Amani kan sa ya russuna, kamar yadda zuciyar ta ta russuna, musamman da ta ga sun kwana gida daya da Mukhy amma ko da wasa bai neme ta ba. Jikin ta duk ya yi la asar ya jikakken tsumma. Mukhtar na kwance cikin kujerar zaman mutum daya a falon nasa ta shigo ba tare da ta san yana ciki ba, don ta duba abinda suka shirya musu na Karin kumallo, ya yi wata irin kwanciya kamar mai barci amma a zahiri ba barcin yake ba, yana tuna maganar da suka yi da Mai ne, na cewa Mai Diffa yana so ya karbi sarautar Diffa tun yanzu, sabida shi tsufa ya cimmasa abubuwa da yawa baya iyawa yanzu, sabida rashin karfin jiki. Ya tuna amsar da ya baiwa Mai a lokacin. Allah ya taimaki Mai Diffa, ina rokon a bari zuwa gaba kadan, tunda Allah ya hore maka lafiya da koshin lafiya da abinda lafiya zata amfana, ina so in kara samun nutsuwar da zan kara fuskantar yadda sha anin mulkin yake daga gare ka Takun sawun Tafisu da kamshin turaren ta ne ya ankarar da shi isowar ta, a daidai kafafun Mukhy Amani ta zauna, har yanzu gajiyar tafiya bata sake shi ba, shiyasa yake ta kwanciya tun jiya ya kasa fita yau, ya bita da kallo tana zama a daidai kafafun nasa, har ta zauna fuskar ta ba yabo ba fallasa sai damuwa da kulawa, ga dukkan mamakin Mukhtar sai cewa ta yi. An dawo lafiya Ya Mukhy? Sai kuma ta tuna zaman da Ummami ta ce irin shi zata dinga yi in tana gaban Maina, ai kuwa ta gyara zaman nata da irin zaman Ummami din, kamar zata shige cikin jikin sa russunawa da kulawa kamar baiwa a gaban Sarki, shi dai Mukhy kallon ta yake daga kwance yana cewa cikin ran sa wannan canjin nata ba na kalau bane, don ganin abun yake banbarakwai, wai namiji da suna Hajara. Haka nan dai ya daure ya amsa mata (with straight face), sai kuma ta ce masa ka ci abinci? I mean breakfast? Ya dan kalle ta da wutsiyar ido yana mamaki, sai ya biye mata da yadda ta zo, ya ce ah ban ci ba tukunna, wani abu ne ya faru? Tashi na kenan daga barcin da na koma bayan sallahr asubahi, shine na zo nan nake hutawa, kafin lokacin fita ta ya yi Mukhtar yayi bayani, don ya kasa gane inda ta dosa da sabon canjin, yafi sawa a ran sa wani abun take so shiyasa, don bai saba da concern din da yake gani yau daga gareta ba. Amani ta karya kai, Allah ya taimaki Maina to ai ga abincin can sun shirya shi tun dazu a kan dining-table, Maina ko zaka taso mu je mu karya tare? Mukhtar ya kasa hadiye mamakin sa har ma da dariyar sa, ya ce Amani ce kuwa? Don hatta lafuzzan ta da wani irin taushi da rangwada suke fito masa. Tayi murmushin jan hankalin miji, sannan ta ce ko a kawo maka abincin nan ne Ya Mukhy? Idan ba ka son tashi daga nan din? . Sai ya ce kawai, ya koma yadda ta zo ta same shi a kwance, ya sake maida hankalin sa kan wayar sa, don ya kasa gasgata abunda yake gani daga gare ta dinnan. Maiyuwuwa gizo idaun sa ke masa. Amani sai ta tashi ta tafi ta kawo abincin daya bayan daya, ta shimfida ledar cin abinci a gaban sa, ta hau hadawa Mukhy black tea mai kamshin kanimfari da citta, don Ummami ta ce mata lallai su duka su dinga yawan shan kaninfari, tana cewa ni bana shan da madara fa, ban sani ba ko kai ma haka? Mukhy ya tashi zaune sosai, sannan ya harde hannuwa a kirji, ya kuma harde kafafun sa, ya zuba mata kyawawan idanun sa, ya sake cewa , kawai, yana ta mamaki dai, don still ya kasa yarda ita ce, sai ta mika masa kofin shayin da ta kammala juyawa da Zuma maimakon sugar, ta bashi cikin girmamawa. Mukhtar sai ya karba, ba tare da ya ce komai ba, ya kuma kai bakin sa ya kurba, kamshin kanimfarin ya masa dadi a makoshi, bai ce a ah ba, amma bai yi wata kwakkwarar magana ba har yanzu. Amani ta cigaba da zama a yanda take, abin ki da rashin sabo da kyakkyawar mu amalar data ke son assasawa, duk ta kasa sakewa da zaman da tayi din, shi kuma ya cigaba da sipping shayin sa ko a jikin sa. Ganin ya karba ba tare da ya gwale ta ba har yana sha, sai ta samu karfin guiwar zuba masa farfesun naman kaza, ta sa spoon a ciki ta mika masa. Ya karba again, ya soma shan romon da cokali, yana yi yana daga ido yana kallon ta, ta kara da zuba masa chips and fried egg wanda ya ji albasa da koren tattasai, ta sake mika masa, ya karba babu musu, don yana jin yunwar sosai, rabon shi da abinci tun jiya, amma kuma babu magana a tsakanin su sannan babu nagode. Ta zauna ta cigaba da latsa wayar hannun ta wanda chatting ne suke yi da Balewa, ta ce Bestie, I m done with step one, but he seemed careless da kokari na . Balewa ta turo mata Emoji na jinjina da kwanji, ta ce, t worry, keep up the good work, saura kwashe kwanukan da ya gama cin abinci, ki tabbatar rigar ta zazzago gaba kuma a saitin idanun sa kin masa flashing Dariya ce ta kama Amani ta yi yar sheshshekar dariya ba shiri, ta ce Balewa ba dama! Sai da Mukhtar ya dago daga cin abincin sa ya dube ta, ke da wa Hajjaju? Ya tambaya cike da tsegumi, don kuwa Amani ba mutum ce mai yawan far a ba balle a je ga dariya a iya sanin da ya yi mata. Yau kuwa sai far a take kamar gonar auduga. Yanzu kuma har da kyakyatawa. Ya Mukhy ni da Balewa ne Oh I see! Ki ce Your role model . Ta yi murmushi, domin bata yarda da abinda yace din ba, hakika da aboki yana maida abokin sa role model din sa, da tuni Balewa ta dade da zame mata role model tuntuni ba sai yanzu ba da duniya da kan ta ke koya mata hankali. Domin iyakar hankali da sanin ya kamata, mutunci da sanin ciwon kai da rikon addini suna tattare da HAMIDAH HASHIM BALEWA, ita din ce a baya bata yarda ta yi copying halaye da dabi un Hamida Balewa ba, don a nata tunanin, a sanda take kan ganiyar ta it ace wayayya Balewa bata waye ba, shi yasa take yin simple life duk da kasancewar ta yar gata, kuma a nata ganin simplicity din Hamida yayi yawa, zai sa kowa ya raina ta. Sai yanzu ne ta san Balewa ce wayayya ba ita ba. Ita shirme da kidifiri da girman kan banza kawai ta sani, ta kuma kware a kai. Mukhy ya ci ya koshi, ta tashi don ta kwashe plates da bowl din farfesun, ta yi yadda Balewa ta ce ta yi, kuma cikin sa a Mukhtar dagowar sa kenan idon sa ya fada kai, ba zato ta ji ya mike shima, zata tafi da kwanukan sai ya dan rungumo ta ta baya, ya ce. Na gode da kulawar nan, nagode da dan canjin nan dana gani, honestly I can t resist it! Sannan ya dora karan hancin sa saman gashin kan ta yana rike da ita daga bayan ta, ya mannota sosai zuwa jikin sa, yana sunsuna gashin ta yana cusa dogon karan hancin sa a ciki, wanda hakan ya sa dankwalin Amani ya sabule ya fadi kasa ta baya. Gabadaya gashin da ya shag yara ya zubo bisa kafadun ta. Ya Ilahee! in ji Mukhy. Yadda Mukhtar ya shiga goga tsinin karan hancin sa cikin gashin kan ta ya haifar mata da yar rudewa, daburcewa da bakuwar kasala, duk ta san cewa ita ta tsokano shi, hakan yasa kwanukan dake rike a hannun ta subucewa suka zube a kasa, da na tangaran ne ba abinda zai hana su fashewa su yanke su sabida yadda suka subuce daga rikon ta ba zaton ta, amma hakan bai sa Mukhy fasa abinda yake yi ba, ta fahimci bat un yau ba, babu kamshin da Mukhy yake matukar so a jikin ta irin kamshin tsakiyar gashin kan ta, wanda ya fahimci turaren gashi na musamman ne take amfani da shi a cikin gashin ta, wanda iyayen ta Jal an da Aisata dake bata shi kadai suka san sirrin da ke cikin sa. Kamshin gashin nan ya tsokano abubuwa da yawa da yake ta kokarin dannewa tun dazu, kuma dai dama ko ta ina aka je aka dawo Mukhtar ya san yayi kewar Tafisu, ba ita kadai ba har tsiwar tata, kidifiri da rashin kunyar duk ya yi kewa yadda ba ya zato, a kwanaki goma