Sashe 13
Amani Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
yi gado. Ni dai na baki amanar Mukhtar don dai gashi ya dawo gare mu ne, amma rayuwar sa zata fi yawa tare da ke, ke ce silar duk wani farin ciki da zai iya samu ko akasin sa, domin sai kin faranta masa daga gida ne zai fito cikin jama ar sa cikin annashuwa, ya ji dadin tafiyar da al ummar sa da mulkin gidan su da tarin responsibilities din talakawa da ke kan sa, tun da dai kin ga shi Maina ne wato (Mai jiran gado) Da zata iya da ta gayawa Ummami cewa ta daina bata amanar MUKHY don Allah, don ita Uwar sa ce kuma bata san halin sa ba, amma shi ma ai takadarin kan sa ne na gani kashe ni, wanda baya bari ko da wasa a taka shi, ko a danne hakkin sa da ya rataya a wuyan mutane. Sai ya kwaci abinsa ko ta karfi ne. Kamar misali in tayi masa kwauron gaisuwa kasancewar shi mutum ne mai so a bashi girman da ya cancanta, da son kowacce mace ta kasance da halaye da dabi u na kwarai na girmama miji kwatankwacin irin na Ummamin sa, to fa ba zai hakura ba sai ya nemi gaisuwar nan ko ta karfin tsiya ne da bakin sa, haka in tayi masa rashin kunyar nata mai lasisi, Mukhy ramawa yake yi babu jinkiri babu bata lokaci, wani lokacin da mai zafin da yafi nata zafi, wanda sai ta kwana tana hadidiye bakar maganar sa. Amma tayi relating da labarin da Ummami ta bata na kuruciyar Mukhy, sai ta ga cewa ita kam, duk da babu Jal an, kuruciya ta gata da yanci kuma mai dadi ta yi, har ma da jin dadin tafi kowa gatan uba, he really deserves happiness ko yaya ne a rayuwar girman sa ta yanzu, kamar yadda mahaifiyar sa ta ce. Kuma ba daga kowa wannan farin cikin zai fara samuwa gare shi ba sai daga cikin gidan sa, wato daga hannun ita matar sa. Can cikin kanta ta jiyo sassanyar muryar Ummami, kasancewar ta yi nisa a tunani. Kin min alkawarin kula da Mukhtar da bashi soyayya da farin ciki a rayuwar girman sa AMINA? Ni kuma in kika yi min hakan, na yi miki alkawarin ba dai kiyi kuka akan Da namiji ba, zan tabbatar na zame miki garkuwa a wurin sa, daga duk mai son shiga gaban ki. Fata na kawai shine Mukhtar ya samu kwanciyar hankali a rayuwar girman sa, wadda bai samu ko kadan a kuruciyar sa ba. Ni da ke, babu hijabin surukuta ko yaya a tsakanin mu, sakamakon cewa ke din ya ta ce ta halali, wadda ko babu Mukhy a tsakanin mu zamu kashe mu rufe tare, ba tare da ko Jal an data yi nakudar ki ta ji ba. Hakika Allah Subhana na so na da kwanciyar hankali a tsufa na, wanda ban samu a kuruciya ta ba cikin gidannan, shiyassa ya bani ke wato ya sallado min ke a matsayin suruka ba tare da dabara ta ba, ke da kika kasance ya ta halali a gare ni, bai yi min suruka da wata daga waje ba, wadda zata sa Mukhtar ya sha wuya a hannun ta, don kawai yana son ta, shi yassa na bude miki ciki na yau mu fahimci juna mu tallafawa juna ta hanyar bashi kulawa a farin ciki ni da ke, ki sa a ran ki ni na haife ki ba Jal an ba Amani ta share yan kananan hawayen da suke ta tsatstsafo mata a kowanne furuci na Ummami, wadanda ta san ba na komai bane na tausayin Mukhy da Mahaifiyar sa ne, duk Ummami ta gama kasha mata jiki da kuzari. A hankali ta gyadawa Ummami kai, wato ta yi wannan alkawarin, na kula da Mukhtar, da sanya shi farin ciki da bashi soyayya. Kuma har cikin ranta ta yi din, domin jikin ta yayi wani irin sanyi, ta yi lakwas kamar jikaakken tsumma, jijiyoyin rashin kunya, na girman kai, na alfahari dana dolonci suka shiga tssitstsinkewa suna farkewa da kan su, hankali da nutsuwa har ma da tsoron Allah ya soma ratsa Amani a kusufa-kusufa daban-daban na kwakwalwar ta. Ta gamawa Ummami kitson cikin matsanancin mutuwar jiki, kuma dare ya yi, don haka ta ce mata zata je ta kwanta, kan ta na sarawa sabida kukan data yi mai tsanani. Kuyangin ta da aka bata su suka raka ta har dakin barcin ta, don har zuwa lokacin suna can suna jiran ta a inda suka saba zama su jira ta in ta zo gun Ummami, da suka dawo bangaren ta daya daga cikinsu ta hada mata mai kamshin na a bisa umarnin ta, ta sha a gefen gadon ta, sannan ta kawo mata Panadol ta hadiya, suka yi mata duk abubuwan da suke yi mata kafin ta kwanta kamar kashe kayan wuta, kunna A/C da kunna mata karatun Al qurani a radion bakin gadon ta cikin kira ar Mahmoud Khalil bisa umarnin Ummami, na kullum su kunna mata in zata kwanta daga kanan surori don ta kara iyawa da gyara karatun sallahr ta. Tahira da Sugra kenan, wadanda su tafi sanyawa aiki da ja a jikin ta cikin hadiman nata guda biyar da Sarki yasa aka bata tun zuwan ta, sauran biyun suna kula da girki da kitchen din ta ne, daya kuma sharar bangaren ta da goge-goge da wankin toilets, ta zabi Sugra daTahira su dinga zama a jikin ta ne don su ba yara bane kamar sauran ukun, suna da hankali da nutsuwa, kuma suna da aure har da yara. Ko ina zata shiga cikin gidan suna tare da ita. Tahira da Sugra suna bada baya, bayan sun mata light off da sai da safe, sun bar mata dim light shudiya, kukan ta cigaba da yi, mara sauti, da alama dai Amani Faskari, most at times, finds pleasure and comfort in crying, tana yi tana yin wannan kukan ne don tausayin Mukhy tana comparing rayuwar sa da nata. Sai ta ga cewa, ratar gatan da ta samu da wanda ya samu mai tsananin girma da fadi ne. bama za a kwatanta ba. Da gaske kamar yadda Ummami tace ne Mukhtar yana bukatar kulawar su su duka yanzu, amma ta yaya? Ta ina zata fara tata kulawar? Ko ta yi kokarin hakan ba zai bata dama ba, saboda ya rike ta da yawa a ran sa. Wata zuciyar ta ce da Amani Ai kema Amani mace ce, ko da ake cewa kin rako mata! Ki yi tunanin hanyoyin dadadawa mutum, musamman mijin auren ka, ta yadda zai ji dadi, ya manta da laifukan ka komai girman su, ya sakar maka fuska da zuciyar sa gabadaya koda baya so, albarkacin kulawar ka gare shi. Tunda an ce zuciya na son mai kyautata mata Sai ki hada da abubuwan da Balewa ta koyar da ke na kissa mai kyau ta waya, da kuma naki yan dabarun da bazaki rasa ba, da wadanda Ummami ma ta koyar da ke na tafiyar da Saraki. Daddyn ta ya fado mata a rai shima zai iya taimakawa wajen sayo mata yardarm Mukhy a yanzu, ta tuna tun tafiyar Daddy basu yi way aba sai ta dauko wayar ta, ta kuwa same shi online a kan whtsp. Sai ta yi masa kira ta cikin whtsp call. Yana dagawa ya ce Tafisu! Me kike yi har yanzu baki yi barci ba? Amani ta yi ajiyar zuciya mai nauyi, ta ce yanzu nake shiri ai Daddy, so nake in tambaye ka yaya jikin ka? Kuma Yaya Mukhy yana lafiya? Dadi mai yawa ya kama Alhaji, y ace na samu lafiya sosai Uwata, kuma ina iya mikewa ma yanzu, Mukhtar sai dai in ce Allah ya saka shi a aljannah y araba shi da iyayen shi lafiya, ko ke da na Haifa iyakar abinda zaki yi min kenan a rayuwa. Uwa in har baki bi Mukhtar sau da kafa ba wallahi sai Allah yayi mana hisabi ni da ke, na hore ki da ki bi shi ki nemi aljannar ki babu ruwa na dake duk ranar da Mukhtar ya kawo min karar ki Amani ta saki kukan da ke cin ran ta, ta ce Daddy! Kuna ta dora min abinda yafi karfi na, bayan ba daga gareni bane matsalar yanzu, na riga na gane kuskure na, shine dai ya ki ya yarda da ni ya kuma saki zuciyar sa da ni. Hakika na yi kuskure, ina so na gyara in zai ban i dama, ka roke shi ya karbi tuba na ya kuma bani damar gyarawa. Na yi alkawarin canzawa daga yadda kowa ya sanni dinnan, amma hakan ba zai yiwu ba sai ya yarda da ni Yardar miji kuma yardar Allah ba! In sha Allahu Mukhtar zai karbi tuban ki musamman in kin ajiye girman kai. Nima kuma zan taimaka wajen ganar da shi halayen ki ba laifin ki bane, nawa ne. Musamman a yanzu da muke da lokaci ni da shi kullum muna tare barci kadai ke raba mu. Ina rokon Allah yayi wa rayuwar ku albarka bakidayan ku, ya kuma albarkaci auren ku da zuri ar da zamu yi alfahari da ita mai yawa mai albarka Ta tambayi Maman ta yace ta yi barci tun dazu. Sun dade suna hira irin tasu ta Tafisu da Daddyn ta. Washegarin ranar, a darussan su na yau, ita da Ummami, har yadda uwargida ke zama a gaban Sarki sai da Ummami ta koyawa Amani, da yanayin yin magana da Sarakuna cikin kankan da harshe da tausasa furuci, da hadawa da kirari na kambamawa da nuna soyayya. Wani abun har sai Amani ta rufe ido don kunya. Da gaske Ummami ta janye hijabin surukuta bakidayan sa. Tasaka na malunta. ***** ***** ***** BAKIN BURKINA FASO anar da su Mukhy suka dawo Diffa daga Burkina Faso ana zabga wani irin ruwan sama kamar da bakin kwarya har da kankara. Labari ya isko su cewa Maina ya dawo lafiya tare da jama ar sa, suna fada wajen Mai Diffa. Tsakanin Mukhtar da Alhaji bata san wa tafi dokin gani ba, don an ce da su Alhaji na tafiya yanzu a kan kafafun sa. Wannan ya kusa saka ta shekawa da gudu don ta cimma Daddy har