← Book details Amani Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 18 OF 19

Sashe 18

Amani Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

cike gurbin mata hudu! Ba wata mace da zai iya yi wa irin son da yake mata. Amma ko me Mukhtar ya tuna? Sai ya fasa rungumeta din da yayi niyya ko ya lallashe ta, ya sa kai zai wuce ta gaban ta ba tare da ya tsinka mata ba, amma a ran sa yana mamaki yana karawa, wato duk shakiyanci ne abun nata, Amani ta san SO. Yau wace irin ranar sa a ce a gare shi? Amani ganin zai tafi ya bar ta a wurin, wato bashi da lokacin sauraron ta, don bai dauke ta mai cikakken hankali ba, bata san sanda ta sha gaban sa ba. Ba inda zaka je Mukhy, na rantse sai ka zaba ko ni ko sa-dakoki Kai tsaye Mukhtar ya wani irin dago, ya zuba mata fusatattun idanun nan nasa masu kama da an diga musu zaiba, ya ce bani hanya in wuce kafin in yi huce kan dami a kan ki, me zaki iya idan na ce na zabi sadakokin, tunda zasu bani abinda Amani-Tafisu bata bani, zasu so ni su kaunace ni, son da Amani-Tafisu bata yi min, zasu so ni duk rashin asali na da rashin kowa nawa. Amma Amani fa? Wadda kyawun Mukhy da ake fadi bai taba bugar da ita ta So shi ba, saboda Mukhtar bai isa komai ba a idanun ta tunda ni hadimin gidan su ne! Amani wadda da ta aure ni, ni da bani da asali, kuma ba dan kowa bane gara ta auri tsohon mai kudi sa an Baban ta Alhaji Sadisu Talle? Ni kuwa me zai hana ni karbar sadaka, idan har ba maza na rako duniya ba kamar yadda Tafisu ta rako mata? Kamar wani wani wanda bai san gatan iyaye ba irin wanda Amani ke tutiya da shi a koda yaushe? Kullum ki saka a ran ki a wurin Alhaji ne kadai kike amsa sunan TAFISU, amma ba a wurin Mukhtar da sauran mutane ba, tun da ni ban yarda Amani ta fi sauran mata komai ba sai iya sai rashin kunya da rashin da a, duk halin banza shi ta fi su iyawa! Maganganun sa sun ratsa ta, domin ta fahimci ya fidda tsatsar duka maganganun ta ne dake kwance a ran sa, duk tsayin lokacin data yi masa su, tana fatan tunda ya furta su yanzu, bayan ta jima da gasa masa su, daga yau ya samu sanyin su daga ran sa, ko ta samu su bar zuciyar sa gabadaya. Ta sunkuyar da kai. Guilty conscience na aikin sa ta ko ina yana nunawa a fuskar ta. Jikin ta duk yayi dan sanyi musamman da ta ji a jikin ta Mukhy ya kafe ta da kyawawan idanun sa, yana karantar reactions din nata, amma Amani-Amani ce har gobe, sai in baka tabo ta ba, masu iya Magana suka ce. A bar hali a ci me? to hakan yake ga Amani yau ma. Domin kuwa share tasirin maganganun sa ta yi gefe ko ince ta hadiye tasirin da suka yi mata ta ce. Tunda ban fi su ba, shine na hakura na bar musu Mukhtar din, tunda a duniyar ka mutum ba ya taba yin kuskure ya dawo ya tuba Ko mai yasa? Ita kan ta Amani bata sani ba. Amma ta san bata taba jin faduwa da karaya sun same ta ba irin yau, duk da dai Mukhy yau cikin subutar baki yayi gangancin gaya mata YANA SON TA, son da baya iya kwatanta shi dana kowacce mace. Sai hawaye ya kara tsinkewa Amani, ji take gabadaya yau tata ta kare. Ta samu kanta kawai da kifa kai a kirjin Mukhtar ta shiga sakin kuka wiwi, tana rera shi cikin zaki muryar ta kamar sarewa Ba kasafai kukan Amani ke bashi tausayi ba, saboda ya riga ya san ita zuma ce sai da wuta, ta hakan ne kawai zai iya rama kadan daga abinda ta dade tana yi masa, hakika Amani ta dade tana cutar da shi da kalaman fatar bakin ta, yana shanyewa yana hadiyewa albarkar mahaifin ta. Amma ganin irin karayar data same ta yau, ga ta kuma kwance akan kirjin sa sai ya ji shima rauni ya shige shi, ya kuma san lallai dagaske Amani ta canza, ko a ce ta fara canzawa, domin a irin zafin kan ta, babu karaya ko kadan a tare da ita cikin tsarin ta. A ajandar halayen ta duka babu given up , ba zai ce saboda sa-daka bane ta fara canzawa, ya dade yana karantar ta, ya san tun kafin maganar sadaka ta samu canji a kan sa a zuciyar ta, haka ya san baka taba kishin mijin da baka so har haka. Zame ta yayi daga jikin sa cikin karfin hali, domin ta saka masa kasala ba yar kadan ba, ya juya zai fita, cikin mutuwar jiki, ba tare da ya kara cewa komai ba. Amani ta sake ruko shi da karfi, murya na karkarwa ta ce, Mukhy! Will you believe me, if I said I LOVE YOU? Sai ya juyo da dukkan idanun sa yana mata wani kallo, kamar na warning din ta daina rike shi, amma kuma ya firgita da jin kalaman, domin sun zo masa a bazata, a cikin idanun sa soyayya da kaunar ta ne tsantsa, haka nata jikakkun idanun abinda ke kwance cikin su kenan, kallon da sukema juna ya shiga tado wata irin sha awar juna ta shiga tarnaki a zukatan su, ta shiga ruruwa tun daga kwakwalen su har yatsar kafafun su, in bai yi kuskure ba kamar yau ya taba jin sunan sa a bakin ta. A yanayin da fuskar ta ta koma yanzu, kamar ta rasa duk wani gatan ta sai shi kadai, a irin kallon data ke masa yanzu, kamar shi kadai ya rage mata a fadin duniya, hawaye na zubar mata wasu na korar wasu ta zame daga jikin sa ta durkusa masa, ta rike kafafun shi tanaci gaba da kukan sosai, tana rokon sa da murya mai ban tausayi ya yi hakuri da duka halayen ta, daga yau ta yi alkawari ta daina! Ya Mukhy, na yarda ka yi min komai don ka huce hali na na banza, na yarda hali na da yawa mara kyau ne, na yarda zan canza daga Amanin da baka so, zuwa Aminar da kake so, na yarda zan zama matar Maina Mukhtar daga daren yau, abokiyar rayuwar sa ta har abada kuma abar hutawar sa karkashin inuwar aure. Amma ka yi min rai! Banda kishiya ko sadaka, saboda bana son su, zuciyata baza ta iya dauka ba Ya Mukhy. Saboda bazan iya sharing Mukhy dina da wasu matan ba. Hakan zai iya manna min ciwon hauka da ciwon damuwa. Ya Mukhy don Allah ka yi hakuri, ka yi min rai, kada ka karba! Kaga ni tun fil azal ba Maina na aura ba Mukhtar na aura, ban san da wadannan traditions din naku ba, na roke ka kada ka bari kokarin tabbatar da culture and tradition na gidan ku da basu zama dole ba a addidni su rusa kyakkyawar dangantakar mu, da rayuwar dana yi mana tanadi daga yau Amani ta russuna ta sumbaci babban yatsan kafar sa cikin roko, duk hawayen idon ta ya koma diga akan kafar sa. Zuwa yanzun kam he s touched, extremely touched! Kuma ya yarda abinda take fada daga zuciyar ta yake fitowa, ba daga fatar bakin ta ba, mamakin hakan da birbishin tausayin da so ke kimsa masa, suka taru suka soma rinjayar dakiyar sa da pretending din sa, suka hana shi magana suka hana shi motsin kirki, ita kuma ta kai sumba yatsan kafafun shi, Mukhtar yayi mutuwar tsaye, amma dai yana gargadin kan sa a kan yayi taka-tsa-tsan da nadamar Amani don akwai gaggawa a cikin ta, kuma sadaka da bata so ne sila, yaushe har Amani ta fara son sa irin haka, da har ta shirya rayuwa da shi haka? Komai aka ce masa mace zata iya, in dai a kan kada a yi mata kishiya ne yau kam zai iya yarda. Mukhtar ya san tsakanin sa da Ubangiji yana matukar son Amani, halayen ta da dabi un ta ne dama baya so. Ganin ta tana neman shidewa a gaban sa yau a kan kishin kada wasu matan su rabe shi ya yi matukar tasiri a tare da shi ba kadan ba, ya kara masa son ta da jin tausayin ta, ya rage masa kuzarin muzanta mata. Duk da haka wani devilish bangare na zuciyar sa bai yarda da ingancin nadamar tata da soyayyar tata ba, ya fi dangana yanayin ta na yau da KISHI. Amma a irin kukan da take yi rike da kafafun sa harda sumbata, sai ta soma saka masa rauni, wato ta soma samun weakness din sa, sabida baya son ganin kukan mace balle matar sa AMANI-AMANAR ALHAJI. Domin ji yake sumbar da take ma yatsun sa na neman sumar da shi daga tsaye, duk wasu tsofaffin feelings din sa a kan Amani na sake dawowa sabbi kar, suna sake sakin sabuwar yabanya ta korran ganyayyaki a fadin zuciyar sa. Yau Ga TAFISU a kwance a kan kafar sa, tana neman gafara da jin kan sa, daga soyayyar sa da kin kishiya, a irin yanayin da yau ko me ya nema zai samu har mafiyin sa, ba tare da ya yi hurting feeling din ta ba. Amma duk da haka taurine rai irin nasa ya ki bari ya dago ta, yana gayawa kan sa kada ya yarda ya bada kai yanzu, sai ya tabbatar da ingancin wannan nadamar tata da canzawar tata, aka ce kowa ya tuba don wuya ba lada, duk da cewa a cikin idanun ta ya ga nadama da soyayya tsantsa, sai dai ya san wasu mata ko basa son miji suna kishin sa, tunda aure ne a tsakanin su. Sai kawai ya janye kafafun sa daga rikon ta a hankali, cikin karfin hali ya taka ya fice ya bar ta a falon, zuciyar sa kamar ta fashe da son Tafisu, da ke kara tumbatsa a kowanne sako na cikin ta. Yana gayawa kan sa Amani Zuma ce sai da wuta, gara ya kara rike sha awar sa a kan ta komai karfin ta, zuwa lokacin da ya dace da ya amshi
Chapter 18 · 0% Book details