Sashe 10
Amani Part 3 Complete Hausa Novel · about 3 min read
manta previous situation din nasa. Wannan yanayin nasa na rashin walwala da bacin rai a yanzu ya zama tarihi a tare da shi. Ya gane hakan ne da ya ga har ya ga Amani duk da fushi da yake da ita amma kuma ya kasa ignoring din ta, karshe sai gashi ya bige da sumbatar ta, wanda ya jima da hana kan sa sake bari wani abu makamancin wannan ya shiga tsakanin su, sabida abubuwan data faffada masa ana I gobe zasu taho Diffa a dakin ta na gidan su sun kara kwaba waccan maganar ta farko. Duk da cewa ya rama da mai zafi har fiye da nata tun a lokacin, daidai da yadda yake so ya rama din, amma tsatsar maganganun har yanzu bata bar ran sa ba. Mukhtar, Alhaji, Mamma, Baba Idi da wadanda sarki ya wakilta su raka su har mutum biyar, sun tashi a jirgin sama zuwa makwabtan su wato Burkina Faso, ya zama sai ita da Ummami da Sahura da tarin bayi mata da ke shige da fice suna ayyukan su a bangaren Ummami. Tunda Mukhy ya kira Ummami yace sun sauka lafiya bai kira Amani ba, hakan yana cikin sababbin techniques da ya dauka don yana so ya koyawa kan sa tolerance a kanta, ita kuma ya koya mata sanin darajar sa, har zuwa lokacin da zata koyi son shi don radin kan ta, irin son da ya samu kan sa yana yi mata, ba wai so na tursasawa ba ko na cin alfarma, ko don idanun iyayen sa da take tunanin bashi da su a baya, ko na dangantakar jini da ke tsakanin su. Ummami tasa aka shirya musu zuwa wajen kishiyar ta wato Hajja Tarha domin Amani ta gaishe ta, an musu karba ta musamman a sassan Tarha ta kuma kira yar ta Sa adiyya dake Guinea a waya ta hada su suka gaisa da Amani. Ummami ta yi haka ne don samar da sanayya tsakanin Amani da yan Sarki guda biyu mata, wato Sayluba da kanwar ta Sa adiya kasancewar su yan uwa biyu kacal da Maina ya mallaka a duniya. Kuma dai dama tsakanin ta da Tarha babu muguwar gaba ta azo a gani sai kishi, wanda ba a iya kaucemawa, wannan sai Ummu Aymana, wadda Allah ya raba su a yanzu. Sayluba kuwa sun hadu tun a wajen bikin auren su data zo, har ta koma Tahoa tun kafin a kammala bikin, halayen yan Sarki Issouffou mata kwata-kwata bai yi kama dana iyayen su mata ba. Suna da saukin kai sosai da son mahaifin su, don bai raga musu komai na soyayyar Uba ba. Sannan tasa aka kai Amani gun amaryar Sarki ta yanzu wadda ita daga Somaliya ya auro ta. A daren Mukhy ya kira Mai Diffa, ya gaya masa in sha Allahu akwai alamun nasara a maganin da akewa Alhaji, don haka Sarki ya gayawa Ummami, inda ya ce ta gayawa Amani ta cigaba da yi wa mahaifin ta addu ar neman lafiya mai dorewa. **** **** ****