Sashe 3
Amani Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
ne tattare da shi haka? an, wadda ke tura Alhaji cikin wheelchair zamu iya cewa mamakin ta ragagge ne, ko dama a tunanin ta tun ganin ta da shi na farko, bai yi mata kama da komai ba sai dan sarauta ma abocin kyakkyawar nasaba, duk wasu attributes na sarauta sun bayyana kan su a tare da shi da halayen sa. Baba Idi da Baba Sahura sai zare ido suke don kuwa Sahura har fitsari ta yi a wando data ga wani katon Zaki mai rai a zaune, amma bai ci kowa ba, sai daga baya ta gane zane ne da aka yi da ceramic (architect) amma kamar real image na zaki mai rai, tambarin Issouffou Massaoudou Kenan, wato Zaki dan Zaki, zakin Diffa. Alhaji Usman dai hawaye yake sharewa a fakaice, ba tare da ya bari an gane kuka yake ba, Mukhtar ya shammace shi yadda baya zato, ashe dan sarkin Diffa ne mai jiran gado yake masa bauta iya bauta shekaru kusan goma! Dadin abun ya kyautata masa ya kaunace shi, irin yadda ko yan wan sa na jini bai yiwa hakan ba. Allah ne ya hada shi da Mukhy amma bai taba kawowa ran sa wai dan sarki bane mai jiran gado. Yafi dangantawa ma da cewa bashi da kowa a duniya shiyasa baya ko so a yi masa zancen ya je ganin gida. Karyar ku makiya da mahassada, karyar ku ta kare maha inta, yau Allah ya maido Mainan Diffa gida (Maina na nufin Yarima mai jiran gado a Diffa, kamar yadda Biyamaradi yake a Maradi). Ire-iren kirarin da ake ta yi wa Mukhtar kenan har aka bashi kujera kusa data Sarkin Diffa, amma sai ya ki zama ya zube a kasa yana kukan farin ciki da godiya ga Allah. A haka Sarki ya fado fadar, sarkin fada ya biyo shi da Alkyabbar sa da amawalin sa suka rufe kofar fadar aka hana kowa shiga bayan shigewar Sarki. Yana zuwa da Mukhtar ya fara tozali, ya ce Mon pils (Da na) Mukhtar da gaske nake gani? Koko ire-iren mafarkai na ne? Sai yayi baya luuu! Zai fadi, kasancewar dama yana fama da hawan jini tun tafiyar Mukhtar wanda ake treating din sa tun lokacin, cikin zafin nama Mukhtar ya tare mahaifin sa ya rungumo shi a kirjin sa, (for the first time) a rayuwar sa da jikin sa ya shafi na mahaifin sa, suka zube a kasa tare. Nan fadawa suka kare scene din da hannayen manyan rigunan su aka umarci kowa ya fita sai manyan fada kadai. Mukhtar sai firfita yake ma sarki da rawanin sa yana fadin ka yafe ni Ya Abiy, na dawo kenan babu inda zan kara zuwa, koda zan cigaba da rayuwa yadda kake so Da kyar aka samu Sarki Issoufou ya zauna a kujerar sa, sannan ya yi umarni da ayi wa wadanda suka kawo Mukhtar sauka ta alfarma a babban masaukin bakin sa. Ummami na can cikin gida amma tuni labari ya kai mata ta bakin Jakadiyar Sarki marikiya ga Mukhtar, wadda ta shiga turakar ta kai tsaye ba tareda ta jira an mata iso ba, ta same ta tana haki, tana cewa yanzu wani bafade ya gaya mata wai Maina yana cikin fada bata san ko da gaske bane don yace an kulle fada, an hana kowa shiga. Mowar Sarki, sai ta mike ba tareda rakiyar kowa ba aka ga ta kama hanyar fita, akwai wata boyayyar kofa ta cikin turakar Sarki wadda yakan shiga fada ta cikin ta wani lokacin, ta can Mowar Sarki ta bi ta isa fada, Mukhtar sai ganin Ummami yayi a gaban sa, ta dubi Mukhtar shima ya dube ta ta taba shi ta tabbatar dan ta ne kwalli daya a duniya Mukhtar dan Issouffou Massaoudou, wanda ya bar su yau shekaru goma sha biyar! Kafin Mukhtar ya ambaci sunanta wanda ya kakare a makogaron sa ya kasa fita, Ummami ta fado jikin sa luuu! A sume. Mukhtar yana fadin Ummami kada ki yi min haka .. kada ki mutu bamu gana ba, bamu fayyacewa juna zuciyar mu ba. Na yi nadamar tafiya ba tareda na fayyace muku abinda ke rai na ba, kuma kun bani uzurin ku! Yanzu da girma ya same ni na san kuna da uzuri fiye da nawa . Aka yayyafawa Ummami ruwa ta farfado sai ta rike Mukhtar ta fashe da kuka. A lokacin an fita dasu Amani da Mamma da Daddy da su Baba Idi zuwa masaukin da Sarki yayi umarnin a kai su. Wani hamshakin gini ne na sarauta da yaji kujeru royal chairs na alfarma, da dakunan barci da aka kawata da gadaje na kasaita, babu abinda babu a wannan guest house din ga dakunan barci rututu. Aka shiga sauke musu kabakin abinci har da naman Dawisu, aka ce su kintsa kafin washegari Sarki ya gama ganawa da Maina zai neme su. In ka ga fuskar Amani a cikin guest room dinnan ta koma kamar jikakken tsumma, sabida yadda tayi cooling, tana ambaton Ya Salaamu sallim, a cikin ran ta, harda su istighfari, tana neman wanda zasu hada ido ko karin bayani ne ta samu, amma ina! Mamma Jal an ko kallon ta taki yi, sai hidima take da mara lafiyan mijin ta. Wata irin nadama da dana sani suka zo suka lullube Amani, mutumin data raina ta ke wulakantawa, ta cewa shege, ta cewa bawan gidan su, kai babu irin sunan kaskancin da bata kira Mukhtar da shi ba shekara da shekaru ashe ya fi ta kyawun nasaba, dan Sarki ne jikan sarki mai jiran gado, wanda in nasaba za a bi ba ikon Allah ba, da bata isa zama matar sa ba. Ta daga ido tana kallon wannan kasaitattar hamshakiyar masarauta wadda ko masarautar Katsina bakidaya data sani bata kama kafar ta a kasaita da shaharar mulki ba. Kada dai Allah ne yake yi mata talala da laifukan ta, kalaman ta marasa Tauhidi da girman kan ta? Yanzu wace izza zata kara yiwa Mukhtar da gorin nasaba? Dama Jal an ta ce mata ta guji ranar dana sani. Ya Ilahal alaameena na tuba! Na tuba Ya Ubangiji na tuba, daga yau baki na ya daina fadar abinda ba alkhairi bane a kan kowanne dan adam, na daina raina kowa, na daina tunain nafi kowa gata! Ita kadai take furta wadannan kalaman kamar zautatta sabon kamu, cikin kidima, Mamma da Daddy duk suna jin ta, Sahura na yagar cinyar Dawisu ta ce ah to ai duniya makaranta ce, ta ishi kowa riga da wando har da hula. Allah da kan sa yayi hani da girman kai, ya bada misali da Shaidan da Annabi Adamu Alaihissalamu, Ubangiji da ya halicci dan adam ya karrama shi akan dukkan halittun sa, kai dan adam waye da zaka kaskanta dan adam dan uwan ka, don kawai kana tunanin ka fi shi arziki? Ai ko hausawa sun ce rabon bawa da arziki mutuwa ce Baba Idrisu ya ce kwarai da gaske, baka debewa bawa tsammani da arziki sai ya mutu! Uwa ki ji tsoron Allah ki gyara halayen ki na raina mutane, kiyi karatun ta nutsu, nan dai kin gani gidan sarauta ne babu ta yadda za ayi su dauki halayen ki na banza da wofi, idan ma bamu koma tare ba kenan, tunda ke din ba yar sarauta bace, na san kuma yan sarakuna yan sarakuna ya uwan su kawai suke aure Mamma Jal an ta ce da ta fi gane shayi ruwa ne. Don in ba Mukhtar din ba sarkin hakuri da girmama iyayen ta wa zai iya kwasar ta? Ai Amani an rako mata! Yau dai gaki gidan sarautar Diffa, ko ki iya takun ki, ko ki ji ki a kofar masarauta, ko kuma ki kare karkashin azaba da mulkin kishiyoyi Idanun Amani suka wani irin raina fata, zuciyar ta ta tsinke, wai bata san tana da kishi ba sai yau da Mamma ta yi mata fatan kishiya, to ta Allah ba tasu ba su duka, ta san Mukhtar yana son ta ko bai fada ba, ta ga hakan muraran ranar su ta karshe da shi a Saliyo gidan Mamma, ta san ko saboda Alhaji ba zai wulakantata ba balle yayi mata kishiya. Ta san ta yi kuskure ba kadan ba amma a bata dama zata gyara. Ba wai a bita da mugun fata ba. Sai ta saka kuka tana cewa. Mamma ke uwa ta ce, duk abinda kika fada zai iya kama ni, ki fadi alkhairi a kaina da Mukhy ko kiyi shuru. Ta yaya zaki yi min fatan kora ko kuma na kishiya? Baba Sahura ta fashe da dariya tana fadin yau kuma? Lallai Amale ya ga Zaki. Yarinya wa ya gaya miki Bornu gabas take, miji irin wannan ake cewa ba a so banda wauta da hauka? Daddy ne kawai ya ji tausayin ta, yadda suka taru suka yi mata caaa! Ganin yadda duk ta bi ta muzanta. Yanzu kam ta gama saddaqarwa Mukhy ya fi karfin ta, idan bata yi sa a bama tare da iyayenta zata koma Katsina a matsayin sakakkiyar bazawara. Sunan ta ya koma bazawara. Irin iskancin da ta tata masa da kaskanci da rainin hankali da kyar zai iya yafe mata tunda ya dawo cikin gatan sa. Na tuba Ya Ubangiji na tuba! Amani ta fada a fili tana hawaye. Alhaji daga zaune ya mika mata hannu ya ce zo nan Uwata, rabu da su kin ji! Bakin su ya sari danyen kashi. In dai Mukhtar dina ne dana sani wallahi zai yafe miki, kuma shi mutum ne kaifi daya bana jin rashin hankalin ki na damun sa, tunda yace ya amshe ki to da gaske ya amshe ki, bana jin dawowar sa gida zata sa ya canza magana. Ke dai ki yi kokari daga rana irin ta yau ki canza halayen ki, ta hanyar komawa AMINA ba AMANI ba. Aminatu Mamar Manzo ma aobociyar ilmi da hankali da iya zama da mutane, kin ji? Ya shiga bubbuga bayan ta yana lallashin ta domin kukan nadama take yi tukuru. Tana mai addu ar kada Allah ya kama ta da laifukan ta a kan mijin ta Mukhtar. Daddy kai kadai ne ka yi min fatan alkhairi, na gode Daddy har abada na san inada kai, na san ba zaka