← Book details Amani Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 19 OF 19

Sashe 19

Amani Part 3 Complete Hausa Novel · about 4 min read

nadamar tata, amma ba yanzu da tsoron sadaka ne yafi rinjaye a ran ta ba, ba soyayyar sa ba (a ganin sa). **** **** **** AMANI wajen da Mukhy ya bar ta ta ci kukan ta ta koshi, tana gayawa kan ta Mukhtar baya ta tata yanzu tunda ya zo cikin gatan sa, ko dama can yaya lafiyar Kura? Dubi dai irin lallashi da roko da bada kan ta data yi amma yayi funfurus! Itama kawai gara ta koyawa zuciyar ta hakuri da shi ta yi zaman Ummami cikin gidan nan, tunda uwar ta ce ko ba Mukhtar a tsakani, tunda in tace ta barwa sadakoki Mukhtar din, ita a maida ta Katsina ba sauraron ta za ayi ba, ba kuma maida ta za a yin ba, ta san ta shigo gidannan kenan har abada ba saki ba yaji, sunan auren nan mutuka raba in ji Ummami, zata koyawa kan ta juriya ta rabu da shi ya auro ko goma ne ta koma gefe ta yi kallon su. Tunda shi baya amsar tuban dan adam, ba a kuskure a nemi gyarawa ya yarda ya bada second chance , Allah da kan sa mai afuwa ne, kuma yana son bayin sa masu afuwa, yana amsar tuban bayin sa idan sun yi repenting, sun tsarkake zukatan su daga sake aikata wannan kuskure, then why not him? Wanda shima ba sama yake da aikata kuskure ba, tunda ba ma asumi bane ba kuma Annabi b. Ai bari kawai ta nuna masa har gobe tana nan a Tafisun ta, ajin ta bai tsinke ba, halin ta na banza na girman kai da raina mutane da wulakanta su kawai ta bari. Tana wannan sake-saken tana hadiyar zuciya sabida kukan data ci, daga bisani ta wuce uwar dakin ta ta kwanta bisa gado, da tunanin Mukhy barcin wahala ya sure ta a wajen. Cikin barcin ta, tsabar yadda ta saka Mukhy a ran ta, da son ya lallashe ta koda da kalaman fatar baki ne, amma ya saka kafa ya fice ya yi banza da kukan ta, ba tare da ya ce ya fasa amsar sadakokin da aka yi masa tayi ba wadanda tunanin su kadai neman haukatata yake. Ta tsinci kan ta a duniyar mafarkin ta tare da MOUKHTAR ISSOUFFOU MASSAOUDOU cikin wani nau I na soyayyar auratayya mai shiga jiki da zuciya, tare da dan Issouffou jikan Massaoudou Balaraben Diffa mai abun mamaki, ta gan su cikin mafarkin Mukhtar yana sumbatar ta iya sumbata, yana juya ta duk ta yadda yake so, daga hakan sai kawai ta ji ya dauke ta suna tafiya zuwa turakar sa, yana rada mata cikin kunnuwan ta cewa. Tafisu kin fi sauran mata a zuciya ta! Irin mafarkin da in dan adam yana yi baya so ko sauro ya cije shi ya farka. Sai kawai Amani taji muryar Baba Sahura a cikin kwanyar ta. Uwa Uwa, Uwa, ke wai lafiya kike barci haka a kasa, ko fadowa kika yi daga gadon, da baki na faman motsi kamar kina cin tsutsa, ga hawaye kina faman yi, kuma a bakin kofar daki kamar wata wadda uwa ta yi wa baki? Sai lokacin ta ankara wai ashe duk wannan a mafarki ne, kenan ita tata soyayyar bata zo da wasa ba, Mukhtar har a cikin mafarki neman zautata yake don ya ga ta gama mika wuya ga soyayyar sa. Ta mike zaune, bata san yaushe ta fado daga gadon har ta mirgina kofar daki ba, ita dai ta gan su suna mirginawa a cikin korran ciyayi ita da Mukkhy, sannan ta dubi Baba Sahura, ta tabbatar mafarki take hakan bai faru ba, Mukhtar tunda yasa kafa ya fice bai dawo gidan bama, ta kama Babar ta Sahura ta rungume jikin ta na kyarma, sai ta fashe da kuka, ta ce Baba Sahura wai kin ji sadaka za a bashi? Sahura ta ce, Au! Shine kike neman haukata kan ki Uwa? Yo in dai a kan zancen sadaka ne Uban ki ma ya auri mata yana saki sun fi goma, shi a kan me zaki hana shi cika al ada? Gaki ke ban ga alamar kina masa wani amfani ba sai shegen kaudi da rashin kunya da kika fi kowacce mace iyawa **** **** **** SANADIN KENAN-4 TAKORI SHAPE \* MERGEFORMAT SHAPE \* MERGEFORMAT PAGE \* MERGEFORMAT Times New Roman Times New Roman Symbol Symbol Arial Arial Arial Black Arial Black Calibri Calibri SimSun Tahoma Tahoma Courier New Courier New Wingdings Wingdings Cambria Math Cambria Math !%),.:;>?]} $([{ Light horizontal Light horizontal Light horizontal Light horizontal SummaryInformation DocumentSummaryInformation WpsCustomData user Normal TECNO LD7 WPS Office 982090ce22b14f25b9e8bba15ca464e9
Chapter 19 · 0% Book details