← Book details Amani Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 5 OF 19

Sashe 5

Amani Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

na hada karatun domin banida cikakkiyar lafiya kuma likitocin kasar duk kwarewar su sun kasa gano takamaimai me ke damu na. Akwai wani abokin karatuna Musulmi, Fa iq, da ya zo daga kasar Masar, shi ya bani laqanin kullum in karanta ayatul kursiiyu kafa bakwai in tofa a ruwa da safe in sha kafin in ci komai. Da wannan lakanin na fara samun lafiya har na kammala karatu na da kyakkyawan sakamako. Daga wannan lokacin ne tallafin da kasar mu ke bamu ya yanke mana, wato dama scholarship din mu iya degree ne, sai na shiga tunanin hanyar da zan bi in yi sponsoring karatu na na gaba wato masters, duk dai don in samu damar cigaba da zama a Paris kada in koma gida. Ayyuka na neman rufin asirin dalibi iri-iri babu wadanda ban yi ba, tun daga wanke-wanke da share-share a hotel, direban bus, jiran shago, zaman library da kuma receptionist, da haka na kukkulla na kukkula na dinga biyan kudin karatun masters dina in instalments (a rarrabe) har Allah ya taimake ni na samu shaidar kammala degree na biyu, daga nan na dukufa neman aiki kwakkwara amma ban samu ba, ko in ce ban dace ba, ina tunanin fallewa zuwa Hong-Kong again, don neman aikin yi, Allah ya hada ni da Ubangida na na yanzu, wato Alhaji Usman Faskari Nan ya labarta musu komai na irin haduwar da suka yi da Alhaji, ya biyo shi Najeriya ya bashi gida da aiki ya kuma ja shi jikin sa da amana irin yadda ko yan uwan sa bai yi wa ba, duk tarin alkhairin Alhaji gare shi sai da ya fada musu har zuwa lalurar data same shi wadda tayi sanadin bashi auren AMANI da Alhaji Usman yayi. Yadda a rana daya yaji duk wani dabaibayi da ke zuciyar sa a kan Diffa ya yaye, da kuma karfin zuciyar da ya samu na dawowa gida karkashin umarnin Alhaji duk ya fada musu. Tun kafin Mukhtar yayi nisa da labarin nan daga Maimartaba Sultan Issoffou Massaoudou har maidakin sa Ummami kuka suke yi sosai. Sarki Issoufoou ya janyo Mukhtar jikin sa ya rungume shi yana kuka sosai da hawayen sa, yana rokon sa ya yafe masa, ya ce da Mukhy (cikin vernacular language din su). Moukhtar, duk abinda muka yi dinnnan muna sane, we did it to protect you from envy, hatred, evil eyes, bad luck, and to save you, as the only male child that I have, to make sure you get the throne of Diffa Emirate at an appropriate time. Ni da kaina na hana mahaifiyar ka jan ka a jikin ta, nida kaina na ce ta fidda kai daga ran ta, Allah zai raya mana kai. Ba zaka taba zama sarki ba idan ka samu gatan da yan sarakuna ke samu, kasancewar kai din daban ne, zagaye nake da makiya haka mahaifiyar ka zagayeta ke da kaidin mata yan uwan ta iri iri musamman da ta haife ka, kasancewar ni mutum ne mai yawan aure-aure, amma tunda muka watsar da kai sai duk hankalin su ya bar kan ka, ya koma kan yadda zasu yi su samu nasu yan suma, don na nuna bana kaunar ka ban damu da rayuwar ka ba. Mukhar dauriya iya dauriya irin wadda ba duka iyaye zasu iya ba a kan dan da suka haifa kwalli daya muka yi a kan ka, domin mu tseratar da rayuwar ka, amma duk halin da kake ciki a gidan Katchalla wallahi mun sani. Kuma muna kulawa da komai naka. Hatta tafiyar ka Farisa mun san da ita, nine kuma na sa aka baka scholarship daga ofishin Ba are Mainasara (shugaban kasar Nijar na wancan karnin). Haka daga sanda ka bar Farisa ne muka daina samun labarin ka sannan bamu san ina ka koma ba. Malamai na daban-daban na cikin gida kullum gayamin suke in kwantar da hankali na domin kana raye, kuma a kyakkyawan hannu mai tsafta, amma na kasa kwantar da hankalin nawa. Kullum (blaming) kaina nake yi kan ko dai hukuncin dana yi wa rayuwar ka ba dabara bace karbabbiya? Ko dai kuskure na yi maimakon (saving life) din ka? Wannan tunanin da wannan nadamar su suka taru suka kwantar da ni na lokaci mai tsaho. Musamman da aka tabbatar min ka bar Farisa ba a san inda ka shiga ba kuma. Har gobe a kan treatment nake, mahaifiyar ka kuwa ka gan ta yanzu bata gani sai da Gilashi, sabida yawan kukan tafiyar ka Maina In mun yi kuskure cikin abinda muka aikata muna rokon Allah ya yafe mana, kai ma ka yafe mana. Sannan madallah da jin cewa kayi aure, lokaci ya yi da zan bayyana ka ga duniya. Zan maka bikin aure irin wanda ba a taba yin irin sa a masarautar Diffa ba, zan gayyato duk sarakunan jamhuriyyyar Nijar, in gabatar da kai gare su, sannan zan baka sarautar Diffa tun ina raye. Kafin nan zan maka nadin sarautar Mainan Diffa ka fara zama a fada tare da ni don ka koyi sha anin mulki na lokaci mai tsaho Duk wadannan abubuwa da ke faruwa yau, Mukhtar couldn t believe them, don ya dauka mafarki yake yi, ire-iren mafarkan da dan adam in yana yin ba ya so ya farka, yana rokon Allah da dai ya farka daga wannan mafarkin, gara ya zarce a cikin ni imar sa, wato ya karasa mutuwa a cikin dadin sa ***** ***** ***** WASHEGARIN RANAR Da wayewar gari, Sarki Issouffou Massaoudou ya aiko a tafi da su Alhaji cikin masarauta, yasa aka kai su dakin da yake ganawa da manyan bakin sa, sannan aka shirya musu karin kumallo tare da Sarki da Ummami. Wanda ya kai su shigifar ya ce su jira kadan, Mai Diffa na zuwa tare da Mowa A lokacin Mukhtar na can yana ramuwar barcin gajiya bai ko tashi ba, don kwanan zaune suka yi da iyayen sa, tun bayan da suka dawo masallaci sallar asubahi aka bude masa wata shigifa da ke kusa da na mahaifin sa, yake barci har zuwa lokacin, barci na kwanciyar hankali irin wanda bai taba samu ba. Su Jal an sun nutsu suna kallon sarautar Allah, domin ko a cikin masarautun Nijar Diffa na sahun farko, komai na masarautar mai ban sha awa ne da ban mamaki kuma irin ancient dinnan amma aka zamanantar da shi, suna kalle kalle suna jiran isowar Mai Diffa da Maidakin sa, wadda suka ji an kira Ummami (Mowa). Can suka jiyo takun sa ya durkako inda suke. Cikin taku na haiba da kamala. Yana shigowa duk suka mike domin girmamawa. Haske da kwarjinin addinin Musulunci ya bayyana sosai a tare da farin balaraben dattijon. A nitse ya zauna a kujerar da ita kadai ce kujerar mulki a dakin, wanda yafi dacewa a kira shi palace , ba jimawa da zaman sa sai wata kofar ta kara budewa. Doguwar matar cikin kyakkyawar laffaya da farin gilashi a idanun ta, ta shigo, ita kadai ba tare da kowa ya rako ta ba. Ta nemi guri gefen maigidan ta ta zauna kasan kafafun sa, fuskar su fal annuri da maraba dasu. Kafin kowannen su ya ce komai aka ji Mamma Jal an ta tsinke da salati ta ce Yaya AISATA! A firgice Ummami ta juyo, jin muryar kanwar ta, Jal an. Da gudu Jal an ta sheka ta isa gareta ta rungume ta. Sai kuma ta saka kukan farin ciki. Da kyar Aisata ta banbarota daga jikin ta. Ta ce an, ke ce koko ido na ne? ah ke zan tambaya da gaske ke ce? Kuma Mukhtar dan ki ne kenan? Aisata (burst into tears) tace ban taba gaya miki cewa na haihu ba, sabida bamu kara haduwa ba tun rabuwar mu sai aike ne a tsakanin mu, sabida a ka ida matan gidannan basa fita, ko asibiti bama zuwa saidai likita mace ta zo har daki ta duba mu, sannan da matsalolin da suka biyo bayan haihuwar tasa, da muka fara waya dake bayan kin yi aure na biyu kenan, ni ban san meyasa na kasa gaya miki ina da Da ba, kodayake bana maganar sa sam, balle irin wannan a muhimmiyar magana ta hada mu da wani nawa ta waya, daga baya kuma bama tare dashi ma, daidai lokacin rasuwar Abbu sanda na aiko dan aike na wajen ku, aike na na farko gida Kenema, lokacin Maina ya riga ya gudu. Me ya kai ki Najeriya yanzu? Na dauka kun rabu da mijin ki na can tun su Abbu na raye, har kin yi wani auren da Lukman kin samu yara? Daga baya kika gaya min a waya ya rasu, ta ina kika hadu da yan Najeriya bayan na san kina Kenema? Suka rungume juna ana ta mamakin wannan ikon Allah, Jal an ta gaya mata Alh. Usman shine mijin ta na fari wanda aka aura mata a kasar Katsina, suka rabu bayan ta haihu, itama rabon ta da yar tun lokacin, sai yanzu da kaddara ta sake hada su. Ta nuna mata Amani dake ta sakin fitsari a kai-a kai daga zaune ta cikin wandon ta a lokacin, sabida yadda ta kara firgicewa da al amarin Ubangiji, wato Mukhy Yayan ta ne na jini kuma?! Bayan nadamar data sha jiya bata ko gama fita daga cikin ta ba, yau ga gagarumar nadamar data fi ta jiya ta kara samun ta. Jal an ta nunowa Aisata ita da hannun ta manuni. Kin gan ta itace yar da na haifa na baro a Najeriya sunan ta Amina, sai da girman ta na gan ta, kuma ita ce matar Mukhtar a halin yanzu, domin a hannun mahaifin ta ya zauna a gidan su duk tsayin wannan lokacin Ummami sai ta mikawa Amani dukkan hannuwan ta tana hawaye tana fadin Ya ki nan diya ta, ta kaina! Amma Amani ta kasa tashi sabida yadda ta jika jikin ta da fitsari a zaune, sai da Sahura ta ciccibata, ta isa ga Aysata, ita kuma ta saka dukkan hannuwa ta rungume ta a ciki, tana fadin dukkan godiya ta tabbata ga Ubangijin talikai, mai rahma mai jin kai, mai yawan hikima ga rayuwar bayin sa Sai lokacin Sarki yayi gyaran murya ya ce hakika Ubangiji mai hikima ne, madallah da ku, madallah da kariman
Chapter 5 · 0% Book details