Sashe 9
Aisha Saddiqah Part 4 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Yanzu dai Petel ki fada masa komai da bakinki ya ji
Aisha ta maimaita wa Baba Barau kalaman Murjanatu kakaf. Da yadda ta tada bori sai ta taho. Baba Barau ya sunkuyar da kai na
yan dakikai, kafin ya dago ya ce,
Na ji, kuma sun yi da dan halak. Kin haifu Indo, daya tamkar da dubu ga iyayenta, kuma mun gode da wannan karramawa da kika yi mana. Allah yayi miki albarka tunda arziki, mulki da daular da kika samu kanki ciki rana daya basu sa kin sarayar da mutunci da martabar mu ba.
Ni kuma na yi miki alkawarin yadda na hada wannan auren haka zan tsaya in kwato miki martabarki. Taiwo ta ke ko Tuwo, sai ta san ba
a cin zarafin bafillace a kwana lafiya don ko sune Qaruna da Fir
auna don mulki da dukiya kin gama auren dan su
Ya ce,
Kuma a gidana za ki ci gaba da zama, don Zainaba tsaf kawarta za ta kalallameta ta zugeta su maida ki. Tunda uwarsa da ubansa kadai ke son auren. Shi dinma nataba ganin kafarsa a gidannanya zo gaishemu? Kullum saidai ace baya nan kamar wani tsuntsu. Don Zaynaba kam sanyin halinta bazai bari ta kwato miki
yanci ba, kuma kin san kawancennan nasu itada Sappa sai Allah
Farin-cikin goyon bayan da ta samu kadai daga iyayenta dattawan kwarai ya wanke mata zuciya ta saki numfashi na samun kwanciyar hakali. Ta san da wasu iyayen ne cewa zasuyi zasu maida ta kada sarauta da mulki ta wuce ta kansu.
Baba Barau ya sa murya ya kira matarsa Furera, ta shigo ya ce,
Maza Furera share wa Aisha dakin can na kusa da naki, ki kuma kama kaji a yanka ki mata farfesu yanzun nan. In kuma gashi take so sai a kaiwa Ayuba ya gasa mata. Ko me ta ke son ci a yi mata (baba Barau na kiwon kajin gidan gona masu yawan gaske a wani bangare na gidansa)
Sai bayan fitar Baba Furera ya tambayi Aisha,
bani wayarki kada ma ya kiraki. Shin kina da iddarsa a kanki??
Kunya sosai ta kama Aisha. Ta sunkuyar da kai ta kasa amsawa.
Baba Barau ya ce,
Magana nake yi da ke Indo
Aisha ta girgiza kai a hankali, wato babu iddar Prince akanta. Wayarta kuma tace ai a wurin ta aje masa abarsa. Ba waya a hannunta yanzu.
Baba Barau ya kara fusata ninkin ta baya, yayi kuta ya ce,
Allah ne shaidata, ni ban yi la
akari da komai nasu ba na yarda na ba su aurenki, amma in suna ganin akwai wata manufa daga gare mu, ko in hankali bai kwanta ba gara da suka maido ki gabanmu da wurwuri.
Amma miji ya jingine mace mai lafiya har watanni tara babu sunna, kuma da sunan aure, sannan suna tare a gida daya ai wannan auren ma da alamar gurbacewarsa.
Babu inda zaki koma kin zo gida kenan inyaso su biyo ki da takardarki ni za
ayiwa iya shege da wulakanci?.
Idan kuma sun ki, na rantse ko da shari
a sai na raba auren nan. Mu za a wulakanta? Mu ake wa kallon kwadayayyu matsiyata?
Baba Barau har ya fi Malam Yunus daukar zafi. Nan ya tafi ya bar Aisha a gidan Baba Barau yana ta ja wa Furera kunne kan lallai kullum ta kama kaza da zabuwa ta yi wa Aisha farfesunsu da suya ko gashi.
Nenne ta kira mahifiyarta ta ta gaya mata Aisha ta taho Gombe, sakamakon abinda Taiwo ta yi mata, da abinda ya biyo baya, wato tahowar Aisha gida.
Nenne ta nuna ma Oummana damuwarta sosai kan abinda ya faru a bikin na Princesses dinta, ga jama
a sun gayyato daga ko
ina ba damar ta barsu ta taho, sai an kai amare, shi ne Nani Oummana ta tace ta kwantar da hankalinta su gama bikin twins lafiya.
**** **** ****
Siddiqah ta wayi gari lafiya a gidan babanta Barau Hamza, amma zuciyarta ta ki yin dadi yadda ya kamata duk da gatan da ake gwada mata kamar ana goyonta, ta kowanne bangare zuciyarta ta rasa sukuni don da dazun da safe ma Ummanta ta yi danmalele mai rai da motsi ta aiko Sunusi ya kawo mata har gidan baba Barau. Danmalelen ya sha manja an shirbineshi da yajin tafarnuwa yadda Petel keso, ga salad da tumatur an yanka masa da albasa
da cocumber.
Siddiqah wadda rabonta da danmalele har ta manta, watakila tun farkon zuwanta Lagos. Tayi matukar jin dadin samunsa, musamman da Umma ce tazauna ta yi mata shi da hannunta.
Furera matar Baba Barau kuma tana ta cika umarnin Baba Barau na fige kaji da zabbi har sun ginshi sha
awar Siddiqah.
Washegarin rana ta biyu ma cikinta baci ya yi saboda canjin cima da ta samu, ta saba da cin abincinsu na yarbawa fresh veggies. Don haka Danmalelennan sai da ya saka ta zagayawa toilet har sau uku tana saukeshi, sabida uban yajinsa.
Aisha data zo barci sai ta kasa koda runtsawa, saboda tunanin magananun Taiwo. Suka zo suna ta sukarta a kirji kamar allura. Hamma da rashinsa a gefenta, sabonsu ita dashi, na wasu watanni bai yi yawan da za ta kasa barci saboda rashinsa ba, amma abin mamaki barcin baya samuwa saboda tunani da damuwa akan halin data baro Hamma a dakin da Nenne ga sauka. Ita ta san bai mata laifin komai ba, Prince ya darajata ya mutunta yana kuma kan daga darajarta da soyayya abinda kowa baiyi zato ba,
Amma a ranta ta yanke ba ita babu komawa aurensa, duk da yadda can wani nesattaccen sako na zuciyarta ke bala'in kewarsa.
**** **** ****
THE PRINCE
Har ya dauki hanyar dakin da ya baro Taiwo wato inda ta sauka sai kuma ya fasa, ya juya da baya-da-baya ya koma masaukinsa na gidan Kakan nasu.
Wani tunani ne ya shige shi wato kada ya kulata sai a gaban Nenne da Dade, ba zai so su raba abin fada a cikin dangi ba, ya san dakin da su Taiwo suke ciki akwai sauran matan family dinsu a cikinsa ba Firdausi ce kadai a dakin tare da ita ba, alhalin ana musu kallon wadanda suka fi kowa hadin kai, kyakkyawar rayuwa, kaunar juna da kwanciyar hakali a kafatanin zurri
arsu ta Sarki Abdulrasheed dan Abdullateef Akanni.
Don a yadda zuciyarsa ke tafarfasa dinnan bai san hukuncin da zai yankewa Taiwo yau ba, he is afraid ya kai hanu jikinta da sunan duka, in ya yi ido hudu da Taiwo a lokacin yana iya marinta, kuma abinda zai biyo bayan hakan sai wani ikon Allah ne zai sanyaya shi.
Don haka Prince yayi koyi da maganar Annabi (S.A.W) ne, da ya ce, kada, kar ka yi hukunci a lokacin tsananin fushi.
In kana tsaye ne abun fushin ya sameka ka zauna, in kana zaune ne ka koma ka kwanta. That was why he decided not to talk at the moment.
Amma ya kudurce sai a gaban Dade da Nenne.
Su Nenne na dawowa dakin da Prince yake suka nufa kai tsaye. Nenne ta same shi a kwance, ya rufe fuskarsa da zara-zaran tafukan hannunsa, shi ya tabbata Taiwo
yar uwarsa ce, kuma makusanciya mafi girma a gare shi.
Amma wannan attitudes din data ke yi wa iyalinsa na mene ne? ya kasa fahimtar Taiwo. Mene ne haka wai a zuciyar Taiwo a kan matarsa?
In haka ne kawai Taiwo ba ta sonsa da rayuwar iyali kome? Tafi son shi da zama a gwauronsa har gobe, saboda ita tana aure har ta aje masu yi mata addu
a kome da shi zata kashe masa nasa auren? Don in banda haka ai in bata godewa Aisha-Siddiqah ba wadda iyayenta suka lankwasata har ta yarda ta yi biyayya ta aure shi da girmansa ita da yarintarta, bai kamata ta saka mata da zagin iyaye da gori mai tsinka zuciya ba. Ya rasa me ke damun Taiwo a kansa sai ka ce a kanta aka fara tagwaitaka.
Duk da cewa, tun asali halin Maman Kiki wani iri ne da shi kadai yake iya tolarating, amma shi ma yanzu ya yarda Taiwo annamimiya ce. Halinta bai da kyau, she
s full of pride and arrogance, watakila shi ya sa hatta mijinta uban
yanta Toafeeq ba ya iya zama inuwa daya da ita na lokaci mai tsaho zai gudu, ya gwammace ya yi nesa da ita. Ya dinga ganinta lokaci-lokaci tunda ta zame masa dole.
In da ya bi hudubobin Taiwo na tuntuni kadan-kadan a kan Aisha, kafin ya gama fahimtar manufarta akan Siddiqah din gabadaya yanzu, da tuni ba su samu fahimtar junan da suka samu shida Siddiqah yanzu ba, da bai samu farin cikin da ya soma dandana da canjin rayuwar da ya soma samu ba.
Shi Aisha ce daidai da rayuwarsa. Ta ishe shi, ta masa daidai, more than enough, tayi kunnen doki da duk wani burinsa a kan macen kwarai. Ba ya so ya yi wa Taiwo hukuncin da a gaba za yi nadama, shi ya sa ya dawo daki, ya jira dawowar iyayensu.
Sai ga Nenne ta shigo dakin nasa fuskarta kamar hadari. Prince ya yunkura ya tashi zaune da kyar, idanunsa sun kada sun yi jazir sun kuma kankance. Nenne ta dube shi idanunta fal takaici da zallar bacin rai, ta ce,
Hammansu yau na maida Aisha ga iyayenta, kamar yadda na dauko amanarta, tunda haka ku ke so kai da abokiyar tagwaitakarka.
Tunda tsoron Murjanatu ka ke, to shi ke nan, ta kashe maka aure, na amince na kuma yarda ta auro maka Haseenah da uku bayan Haseenah. Tunda itace uwarka ita ta haife ka.
Amma kada ka sake ka saka ni a maganar bikon Aisha, bazani ba, saboda ina tattalin mutuncina a idon masu ganina da kima, ba kaida Taiwo dinka da baku daukeni a bakin komai ba, inaso iyayen Aisha wato Zainaba da Malam Yunusa su yanke duk irin hukuncin da yafi musu daidai
Daga bayan Nenne Dade shi ma ya shigo, ya dora daga inda Nenne ta tsaya, ya ce.