← Book details Aisha Saddiqah Part 4 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 22 OF 26

Sashe 22

Aisha Saddiqah Part 4 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Nenne tace "Hammansu akan zancen lefen Aisha ne, na maka aure da dukkan hidimarsa amma lefe na al'adar Hausa Fulani na tuna ba
ayi ba na bar maka kayi da kanka. Zaka fi sanin irin dawainiyar dake cikin aure da wahalar sa".
Prince yayi murmushi yace "Nenne kenan, ai da kin fada tuntuni da tuni an yi. Yanzunma bata baci
better late than never
. Nawa zan bayar?" Nenne tace "da yawa. Don sawa zanyi a hada komai cikin kwana uku kafin Aisha ta baro Gombe ta dora hannunta akan lefen nan" shi ya san Aisha sarai bata wani damu da abin duniya ba balle wani lefe, kuma ita a wurinta maganganun Taiwo sun dade da wucewa bata kara waiwayarsu, amma yasan Nennensa sarai tunda ta rike shi a ranta to fa sai anyi. Hamma yace,
"to Nenne bakomai, ayi amfani da 'Black Card' dina dana baki ajiya kafin na taho, ba limit a cikinsa. In ce ko shikenan?"
Nenne tayi murmushi bata yi magana ba. Prince ya sake cewa "in ma kin karar da abinda ke ciki Nenne dana iso zan bada
dollar card
dina a karasa, ince ko hakan yayi miki? Ayi lefe lafiya".
Yana sauka a Lagos kuwa gidansu ya zarce. Yace "Nenne yaya an gama lefen?"
Tace "an kusa dai". Har ya fita zai tafi gidansa ya dawo. Ya baima Nenne dollar card dinsa yace "in case wancan ya kare" Nenne na dariya a ranta tace Hammansu da Dade dinsa
are real Yoruba Demons
akan son matansu basu da na biyu.
Nenne da Taiwo suka hada lefe na gani na fada ranar Friday Taiwo ta taho da lefen Gombe.
Sai Nani Oummana tasa wata Aunty dinsu da matar Uncle Abdulmajeed da tazo a lokacin tareda Taiwo suka kawo lefen gidansu Aisha da daddare.
Sai ga Taiwo har dakin Aisha yau, tana cike da 'guilt' mai yawa, Don gani take hatta lefen nan sabida ita aka yi shi. Ta kara jin nadama mai yawa. Sai ta bige da yiwa Aisha hirar Kiki, ta gaya mata Kiki na tafe sati biyu masu zuwa, kuma da tazo za'a saka ranar aurenta da Tosin.
Nenne kuwa taji dadi da akayi hakan, ko ba komai anyi drawing attention dinsu zuwa ga abinda yake cikon al'adar aure ga Hausa/ Fulani.
Taiwo ta sanar da Haj. Zainab sakon Nenne na cewa ita zata wuce Lagos da Aisha idan ta gama jamb dinta ranar asabar, to lahadi sai su tafi.
Haj. Zainab dai basu gaya mata zasu kawo lefe ba, don haka duk a dame take da rashin shirya musu komai bis
a al'ada su kuma Nenne sun yi haka ne don kada su tasheta tsaye inji Nenne, duk da haka sai ta aika Sunusi ya kira Baba Furaira ta karbi lefen. Suka bada tukuici na kudi Inji Baba Barau. Aka rabu cike da farinciki da godiya ga juna.
Don haka Umman Aisha ta dukufa da yiwa Aisha gyaran da tuntuni take son yi mata cikin kwana biyun daya rage musu. Tasa an yiwa Aisha halawa da Dilka mai kunshi kuma tazo har guda ta rangada mata irin black and red henna dinnan. A gefe kwararriyar mai kitso tayi nata aikin, kitso yiri-yiri ta yiwa Aisha kamar da allura ta tsaga shi irin na 'yan Maiduguri.
Sai ga Aisha ta fito tas a cikakkiyar amaryarta tana sheki da sparkling. Abubuwa ne da tun wancan lokacin Haj Zainab taso tayi mata bata samu dama ba sai yanzu. Don haka Aisha ba karamin gyaran amarci ta samu ba, ta fito tayi das da ita.
Washegari Asabar Malam Yunus da kansa ya kai Aisha yin Jamb a location din da zata zana, Jamb dinda Aisha ta kallafawa rai yau Allah yayi an zana ta. Tun 7:30 suka fita karfe 8 suka shiga kuma kafin 10 Aisha ta gama. Abbanta ya jirata har ta kammala ya dawo da ita gida.
A daren Aisha suke sallama dasu Umma. Sun raba dare suna hira, Nenne ma ta bugo taji yaya Shirin tahowar tasu ta gaya mata ta gama shiryawa, sallama suke itada Umma. Aunty Taiwo tace sai 11 zasu zo su dauketa su zarce airport.
Hakan kuwa akayi. Malam Buhari da Taiwo a kofar gidan su Siddiqah 11 na safe tayi musu. Aunty Taiwo ta shigo suka gaisa da Umman Aisha, sukayi sallama, Sunusi ya kai kayan Aisha mota, ta rungume Umma, ta sake rungumeta. Har ta fita soro ta dawo ta sake rungume Umma ido fal kwallah. Umma dariya da dauriya duka, tace.
"Petel dina, zanyi kewarki! Allah ya tsare yayi albarka mai yawa".
**** **** ****
Su Aisha sun sauka Lagos da tsakar rana, nan suka tadda tarbar Nenne ta alfarma. Ga abinci (Yoruba traditional food) da fresh juice din kankana da apple Nenne ta shirya musu. Ga yoghurt da ta yiwa Aisha na musamman. Aisha na bude warmers din taga Ewedu ta hau dariyar farin ciki, tasan tayi kewar kalolin abincin Hamma har mafarkinsu take amma ashe Nenne ta fita sanin su take marmarin ci. Nenne kamar tasan me takewa dariyar, tace
shiyasa nayi miki su ai, na san rabonki da Yoruba food tun barinki Lagos
Prince ya gama yiwa Aisha duk wani shirin tafiyarta Qatar tuntuni, a yadda ya tsara washegari Litinin zata bar Lagos ta sameshi a Qatar. Amma sai Nenne ta ce ta daga tafiyar Aisha Qatar sai alhamis, saboda zasu tafi Umrah ita da Dade alhamis din, kuma Qatar airways zasu bi. So zasu taho da ita kawai su kawota da kansu, dama last time bataso tafiyar Aisha ita kadai ba babu 'yan rakiya don dai umarnin Emir ne.
Don haka yanzu da kansu zasu taho da ita su kawota sannan su wuce Umrah.
Prince ko kadan bai so hakan ba, amma dai yace "toh Nenne Allah ya kaimu".
Wannan daga zuwan na Aisha daga Monday zuwa alhamis da Nenne tayi ya baiwa Prince damar yin settling sosai, bayan komawarsa Qatar, don ashe aiki ne damqam yake jiransa bai sani ba, wanda zaiyi in ba shi ba. A cikin ayyukan da ya tarar akwai zuwa consultation na aiki kasar Singapore sati mai zuwa. Kuma in yaje sai yayi sati biyar acan. Tafiyar ta kama masa sati daya da dawowar Aisha gidansa, tunda sai upper week.
Har ila yau, daga zuwan nata da Nenne tayi zuwa alhamis sai ya karawa Prince wani irin dokantuwa da zuwan Aisha fiyeda na baya. Don haka ya shiga gyaran gidansa domin taren Siddiqah. Yasa aka fidda duka furniture din gidan tun daga gado har kujeru ya saka sababbi farare sol. In bai manta ba Kiki ta taba gaya masa ya kamata ya sakawa Aisha sababbin furniture, a wancan zuwan nata Argentina. Tace amarya komai sabo ake saka mata.
Ba furniture kadai ba hatta curtains din gidan da rug carpets saida Prince ya canza da samfurin zamani kirar jiya-jiya (latest arrivals).
Kayan cefane kuwa ba abinda bai sa an ajiye mata ba, tun daga kan gishiri har tsinken sakace, kai har da wadanda Aisha bazata bukata bama daga zuwanta, duk Prince yasa yaron gidansa na Qatar wato Zaid ya ajiye mata.
Wato bayeraben miji in ya tashi soyayya da dukkan zuciyarsa yake yin ta musamman mai shekaru da cikar hankali irin na Hamma Prince, don babu rawar kan kuruciya a tareda shi da zuciya daya yake son Aisha yake kuma hidimtawa soyayyar.
Kai lallai shiri ba dan karami ba na hango Kehinde na yiwa Aisha. Sai mu ce amarya Aisha Allah ya kiyaye hanya ya kawo kazantar daki.
Ya shirya mata lafiyayyen dakin barci dab da nasa, bayan master bedroom da zasuyi sharing. Babu abin da babu na bukatar mace
yar gayu a dakinnan na Petel Siddiqah.
Wannan gidan da Prince yake ciki is not a Ranch House, gida ne da Qatar Refinery suka bashi don ya zauna yayi musu aiki. Gidan 'penthouse' ne. Ranch House da Polo Horses dinsa duka suna can Argentina.
To dama Qatar wajen da yake aikinsa ne kawai, baya Polo a Qatar sai ya haura kasashen turai ko Argentina yake yin abinsa.
**** **** *****
Nenne ta gama ma Aisha duk wani shiri da ake yiwa amare 'yan kabilar Yoruba wadanda za'a kai gidan miji karo na farko, har ciccibin nagge Nenne ta dafa mata ta cinye ba tareda ta san ko menene ba. Aisha ta sha mamakin ganin Aunty Taiwo bata koma gidanta ba tun saukarsu, ta tare ma a dakin Princess Fatima.
Kuma da alama zaman gida take. Bata tambayi komai ba amma ta gane akwai matsala a auren Aunty Taiwo yanzu, shiyasa ta dawo gida.
Ranar Alhamis kamar yadda suka alqawartama Prince Nenne da Dade da surukarsu Aisha Siddiqah Yunus, suka daga cikin Qatar Airways, daga filin jirgin saman Murtala Mohammed na jihar Lagos.
Tun jiya Dade ya gaya masa lokacin tasowarsu da landing time.
Chapter 22 · 0% Book details