← Book details Aisha Saddiqah Part 4 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 17 OF 26

Sashe 17

Aisha Saddiqah Part 4 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Dan haka suka ce ta kawar da maganar Taiwo daga ranta ta fuskanci aurenta da mijinta da iyayen mijinta. Ta kyautata musu ta kuma rike su da kyau.
Baba Barau yace
tunda naga ya matsa ma Indo ko zaki hakura ki bar jamb din ne? Ban ga amfaninta ba tunda kasar zaku bari fa.
Tace
Baba gara inyi, ko ba komi dole zan koma makaranta, ina so in cigaba
Baba Barau yace
toh bakomi
Addar Kumo tace
gara dai ki kara satin kema, sai ayi miki shirin amarya, kamar yadda akayi ma
yar uwarki Maryam. Yanzu ne za mu kai diya, dan wancan kaiwar daman dai yin sa kawai akayi
Ummanta tace
nima zanfi son haka
. Aka ce
toh shikenan. Allah ya masu albarka
Toh dazu bayan azhar tana tsakar gida sai ga Baban ta ya shigo yace Hamma ya kira shi yace zai zo anjima ya musu sallama sabida gobe daga Litinin ze wuce Lagos, jibi zai tafi Argentina. Aisha tace
tayi ciki.

Ta ma rasa me take ji. She is happy, kuma har ranta abin da ya faru ya wuce, amma kuma sai tana jin haushin Hamma yace zai tafi. Wato bai ma damu ba, da tace baza ta bishi ba. Hmmm! Da Haseena ce kila kuka zai yi tayi
mtsw
Satin nan da tayi a gida, quite sure tasan Hamma bashi da laifi, amman kawai dukansu taji sun bata haushi daga Taiwo din har shi. But daga baya tana dan missing dinshi.
Amman jiya yadda taji Baba Barau yana bata labarin nacin da yayi tayi akanta, ya dawo Gombe ma gabadaya duk sai ta ji tausayin shi da so me girma.
(She always want to be loved) sosai irin haka, toh gashi itama dai kamar Prince ya fara sonta.
Amman wannan cewa da yayi zai koma be matsa su tafi tare ba, ya bata haushi. Ta sake kwana a gidan Baba Barau dai, ta dawo gidansu tayi kwance har akai magrib.
Daman tun yau da safe aka fara mata gyaran jiki itama. Ummanta tasa an mata halawa dazu dasu dilka, tace baza a qara ba.
Toh yanzu ana ida magrib Umma ta miqa mata diye tace taje ta durje jikinta dashi ta hada mata lalle da khumra kuma tace ta dauraye jikin dashi. Aisha tace
. Ta shige toilet tayi ta gama ta fito. gaba daya dakin har waje kamshi ke tashi. Tace
Umma nidai mura zanyi in kullum zan wannan wankan
. Haj Zainab bata tanka ta ba dai, tace
yi ki shirya ko Hamma yau zai zo zance
tace
kai Umma, ina tsoho ina zance
Umma tace Patel kenan, ana so ana kaiwa kasuwa. Ni je ki shirya kyaji da gulmar ki
. Ta wuce ta barta a wurin.
She is so nervous, a haka ta tashi tai sallahr isha. sai ta dauki kulaccen da Ummanta ta bata ta shafa, da tasa undies dinta black ta ma rasa kayan da zata sa, akwai wata abaya da Ummanta tazo mata dashi daga Hajj bata taba sakata ba daman suka tafi Lagos da Nenne. Ita ta dauka tasa, white and silver haka kuma cif-cif jikinta. Sai ya kwanta lubb! A jikinta, kugun nan nata ya fito masha Allah.
Tace ta san dai tayi kiba saboda abayan kamar yanaso ya matse ta, karin kibar nata har haka ne? data gama ta dauko
yan hannun gold din da Nenne ta bata na Makkah ta saka su, tasa
yan kananan
yan kunne na gold suma ba sarka. Tayi parking kitson ta tayi gammo da gashi. Sai ta dau gyalen abayar ta yafa. Tana zaune taji ana gaisuwa a tsakar gida, gaban ta ya fadi
Shi kuma Prince tun da akai magrib ya dau wanka. Ya dai ma kasa cin abinci. Yayi sallah yana zaune da jallabiya har akayi isha, sannan ya shigo cikin sassan Oummana, Nenne tace yazo yaci abinci yace a koshe yake. Bari ya shirya zashi gidansu Aisha zai masu sallama tace
ya shiga ciki ya dauko kananan kaya sai kuma ya mayar, yace gidan surukai ne. Sai ya dauko w
ata baqar (voile lace) na maza. tana da shara shara haka sai daukan ido kyallin ta yake. Wando da riga irin iya cinya dinnan cip jikin sa dinkin. Sai karamin hannu haka ba dogo ba iya gwiwar hannu. Haka Hamma ya shirya tsab, ya dauko hular sa Tonak ya saka baka itama, da design din silver a jikinta, ya zuba turaren
Tomford Oudwood
ya kuma dauko
Francis Kurkdjian Baccarat Rouge
ya fesa.
Wani sanyayyan kamshi na tashi daga jikin Prince ya dauko
black hermes
ya saka ya daura
rolex
dinsa ya fito.
Ai yana fitowa sai Taiwo tasa guda har ma dai yaji kunya, su Nenne duk suka juyo, yace
meye haka Taiwo?
, tace ko dai mu dauko mayafi mu bika naga daukar amarya zaka yau
yace
kash!
Ya wuce.
Nenne da tayi murmushi dan tun bai fito ba suke jin kamshi. Lallai Aisha Siddiqa ta ciri tuta. yau Kehinde ke ta wannan rawar kafar haka zai je zance.
Alhamdulillah
Nenne ta gode ma Allah.
Yace musu se ya dawo ya fita. ya dau mallam Buhari suka wuce.
Prince ya yi sallama gidan su Aisha, Mallam Yunus yana tsakar gida suna zaune da Umma, ya amsa ya ce
shigo mana Abdulrashid
. Ya shigo ya gaishe su. Sun burge shi. Domin sun shimfida katuwar dadduma ga abinci nan a gefe, ga sallayar Umman Aisha da hijabinta akai. Nan tayi sallah kenan.
Tana gefen Mal. Yunus suna hira tana dama fura. Shikuma ya kishingida haka kan tuntu. They look so simple and very in love. Masha Allah kawai yace a ransa, ya karaso suka gaisa yace Oummana na gaishe su. Mal. Yunus yace suna amsawa ina Dade? Yace ai ya koma Lagos tun dazu. su Nenne suma jirgin safe zasu bi gobe. Suka ce
toh Allah ya kai su lafiya
. Akayi shiru, Umma tace
shiga palo Hammansu, bari in kira Petel

Petel!!!!
Umma ta kwada mata kira, ta amsa daga cikin dakinta tace
tace ga
Hammanku yazo, ki debo ruwa da abinci ki kai masa. Hammansu akul kayi min fulako
yayi dariya yace
Umma ai daga gida nake, furar kawai zan sha
. Tace
toh bari ta kawo maka
yace
Ta nuna masa kofar falo ya shiga, ya zauna yana jiran gimbiyar tasa.

Can sai gata ta fito, Ummanta tace
dau fura da yamri a fridge da kindirmo duk ki tafi dashi, wanda yafi so sai ki dama masa
. Tace
toh Umma
. Umma duk sai ta ga wani kyau diyarta yau ta tatso, tace
uhm lallai
Aisha dai an girma, masha Allah
Tayi sallama ta shigo, fuskar dai a gimtse, da dan nisa tsakanin falon Baban nata da cikin gida. Prince ya amsa mata, ta shigo, ya daga ido yana kallon ta.
Tashi yayi don ya taya ta da kayan hannunta amman sai ya kasa. Wani kamshi takeyi da ya rasa wane iri ne tun shigowarta, ta qara cika, ga wata abaya nan ta saka ta kwanta jikin ta, gabadaya surarta ta fito waje
. shi yarinyar nan take so ta jiqawa aiki a gaban iyayen ta.
Tana shigowa tayi sallama taji ya amsa tunda ta fito tsakar gida take jin wani irin kamshi yanzu da ta shigo kamar tana aljanna
Prince ya amsa mata ta dan daga kai ta kalle shi,
hasbunallah
tace a ranta, my husband, yayi kyau. abinki da fari, yasa bakaken kaya, duk ya bar qasumba se ya sake zama yaro dan shekaru 35.
Ta karaso, kamshi cool ya cika ko ina
ta ajiye furar da tray din a table din kusa dashi, sannan ta zauna, duk yana binta da ido. Ta zauna kan carpet tace
Hamma ina yini?
Yace
lafiya lau
da kyar
tace
ya su Oummana da Nenne da Maman Kiki?
Yace
they are all fine, how are you?
Tace
Am fine, Alhamdulillah yace
don gabadaya kokawa yake da kansa. Domin data duka yanzu don ajje tray dinnan a gabansa kamar ya kamo ta. Tayi kyau, ga lallen nan ashe har kafa aka yi shi. Wadannan siraran abin hannun gold din data saka sai ya kara masu kyau. Ga wani kamshi da take da ya rasa menene. Kai shi kamar ma har canza kala Siddiqah tayi.
Ya kafe ta da ido, yana yi wa kansa fada, shi fa ba yaro bane, meye haka yake abu kamar sabon balaga? Zuciyar sa ta ce to meye maraba? Tunda dai tuzurun saurayi ne yayi sa
ar samun sweet 16?
Sai duk sukayi shiru, tace a hankali
Hamma a dama furar? Ko yamri za a saka?
Yace
furar dai
tace
ta tashi ta dauko sai taga bata dauko bowl ba, sai ta mike zuwa dining din palon, ta duka haka tana neman bowl din tangaran na dama fura, gabadaya shi kuma ya kafe ta da ido, dukawar nan da Aisha tayi kuwa yaga Ali, Ali ya gan sa. Se yaji kamar yasa ihu
Yace waye ya koya ma Aisha seduction haka
Omooo this girl wan kill me
Ta dauko ta qaraso tana zama sai taji tashin motar Baban ta, tace
ah Abba fita yayi? Ina zuwa
sai ta leka waje ta gan shi tace
Abba ina zuwa?
Yace Baba Barau ne ya kira ni
tace
toh a gaishe su, sai ka dawo
(ta dawo like a child), ta zauna tasa fura a gaba tana ta dama masa, duk sun kasa magana.
Ta gama zata juye a bowl, yace shi a qwarya zai sha, da fulatanci ya fada, sai tace
Ta miko masa, sai ya nuna table din gefen sa yace a can zata sa, ta taso zata ajje ya cire hular sa yasa gefe. Ai tana ajje wa yana kama qugun ta, abinki da abaya silky nan ya jiyo jigida fal qugun, ga wata
curve besin
ya fara bi da hannu bayan ya zaunar da ita cinyar sa, Prince yace murya na shaqewa.
Chapter 17 · 0% Book details