← Book details Aisha Saddiqah Part 4 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 8 OF 26

Sashe 8

Aisha Saddiqah Part 4 Complete Hausa Novel · about 5 min read

Babu abin da ya yi min Nenne sai kyautatawa ta alkhairi da mutuntawa cikin alfarmarsa
Umma ta kara shiga duhu tace
to Petel din Umma, gayamin menene ko wanene?
Daidai lokacin Malam Yunus ya shigo gidan, yana ta sauri kamar ya tashi sama, don har ya fita wajen aiki Prince Abdulrasheed ya kira shi a waya, yana tambaya cikin jin nauyi da murya mara amo da karsashi, bayan ya gaisheshi yadda ya saba kira lokaci-lokaci ya gaisheshi tun bayan rasuwar Emir da suka hadu a wajen makoki a Ilorin, sai ya tambayi Malam Yunus din,

ko Aisha ta iso gida lafiya?
Abban Aisha ya ce masa,
Siddiqah kuma? Ba dazu aka ce min kuna Ilorin ba? Ita da wa tazo? Kai ban san komai ba, amma bari inyi hanzari in karasa gidan in duba
Sallamar Malam Yunus ta sa Aisha tashi zaune daga jikin Umma. Ta sauko kasa tana gaida Babanta shikuma ya zauna a kusa da ita. In ta tuna irin kalaman Aunty Taiwo a kansa bata sanin sanda ta ke jin sababbin hawaye sun bulbulo mata. Ta durkushe gaban Malam Yunus tana ta sabon kuka.

Petel in ki ka yi haka ba ki kyauta mana ba, ba ki kyauta wa Hajiya Sappa ba, in wani laifi mijinki ya yi miki ai tsakaninki da shi sulhu ne, bai kamata ki daga musu hankali ki ce komai dare sai kin taho gida ba, zo mu zauna zo mu saba shi ne aure.
Ina ta yabonki sallah kinyi zamanki kin kwantar da hankalin ki a gidan aurenki kada ki kasa alwala mana Siddiqahrmu Petel
yar Ummanta. Yanzu dai gaya mana me ya faru? Don Abdulrasheed bai gaya min komai na dalilin tahowarki ba, ya dai kira ni don jin saukarki lafiya? Kuma daga ji yana cikin damuwa a kan tahowarki. Ya ce ayi hakuri yana tafe gobe insha Allah bayan daurin auren kannensa
Aisha ta kara sautin kukanta, har da zambarwa tana cewa,
ko Hamma ya zo yayi a banza, don ba zan bi shi ba, na dawo gaban talakawan iyayena kenan, na gama wannan auren tunda a kansa aka ci mutuncin Babana da Ummata da bana hada su da kowa.
Aka yi muku zagin da ba zan iya hakura ba a bainar jama
a. Aka yimin gorin suttura harda na lefe, wallahi ko Hamma shi ya saura da namiji a duniya na bar wa Aunty Taiwo dan uwanta
Ta kwashe komai ta gaya musu, jikinta har tsuma yake da tana fadi, ko kalma daya ba ta cire ba cikin muggan maganganun Aunty Taiwo.
Shi kansa Malam Yunus sai da jikinsa da zuciyarsa suka raurawa. Abinki da bafullatanin usuli, sanin kowa ne Bafullacen mutum baya daukar kaskanci da raini ko kankani amma ya kanyi kara da alkunya.
Malam Yunus Hamza da maidakinsa Haj. Zainab Yunus duka jikkkunansu sunyi mugun sanyi, kuma rayukansu sun yi karshen baci don basu taba jin abinda ya taba mutuncinsu irin wannan ba. Kuma wai daga wadda tafi kowa kusanci da Abdulrasheed din. Amma kokari suke su shanye hakan akan fuskokinsu daga idon Petel, don kar su kara dugunzuma ta.
Sanin kansu ne Petel bata iya bacin rai ba, bahagon hukunci take yi in aka kaita makura, sannan bata da rufi akan komai, bata boye abinda bai mata ba wai don ta faranta maka wannan halinta ne na tun asali keke-da-keke, kuma bata da kara bata kuma damu itama ayi mata ba.
Murya a sanyaye Malam Yunus ya ce.

Haka abin ya zama? Ashe ana maida manufar alkhairi zuwa ta sharri da wulakanci da tozarci?
Sha zamanki Petel, duk da cewa aure rai ne da shi to ina rokon Allah ya kawo karshen wannan daga yau.
Allah shi ne shaidata na bada aurenki gare su ne darajar mutuncin Hajiya Sappa, ban yi la
akari da dukiya, sarauta ko wani abu nasu ba, karewar ma da na ji hakikanin ko su waye Akanni, a tambayi Yaya Barau cewa nayi ban yarda ba, ba kuma zan yarda ba. Na yi tattaki na tafi wajen Malam Hassan a kan maganar ki da Ishaqa shi kuma ya kwance min zani a kasuwa.
A dalilin haka Yaya Barau ya fusata ya ce a basu, ba Yarbawa ba ko Ijaw ne, saboda dalilai masu karfi akan Haj. Sappa. Amma ban da haka wallahi-wallahi na fi karfin kwadayi a wurin kowa, nafi karfin kwadayin sarauta ko mulki ko neman suna, ita ma Hajiya Sappa ta sani, banida wata manufa a kan auren nan sai ta tunanin zasu rike min ke da mutunci da martaba tunda su suka zo suka ce suna so cikin mutunci.
Amma tunda haka suka ce, to Petel share dakinki ki zauna, su kawo min takardar sakinki, dama Ishaqa ya dawo Gombe, ki gama iddah ki auri daidai ke.
Petel ke kadai muke da, ke kadai Allah ya bar mana, bayan
wabi
na
ya goma! Ta yaya za mu yarda ki wulakanta a gidan aure ko a duniya? Bayan ba wai bamu da abinda zaki ci ki sha ki suturta bane? Aure ne kawai wanda ya zama dole akan diya mace? Ko da muke talakawa a kansu, su masu mulki da dukiya wallahi bazasu kira matsiyata ba, ba kwadayayyu bane mu da zuri
ar mu duk fadin garin Gombe kowa ya san masu wadatar zuci ne, masu sana
ar da zasu dogaro da Allah da kuma kansu
Ran bafillacen ya baci, yana fulatanci yana gamutsawa da Hausa. Umma dai kasa magana ta yi, don ta tsorata sosai da yadda Malam Yunus ya fusata, ya sa Petel a gaban motarsa nan take suka dauki hanyar gidan Baba Barau suka bar Hajiya Zainab ta rasa abinda ke mata dadi.
Ba ta so a ce Petel dinta ta zama bazawara, at a very tender age ko a kirata sauta ga wawa, kuma bata so ya zama su Mallam Yunus sun yanke hukunci kawai daga bakin Petel gabanin jiran Dade da Nenne, da shi kansa Abdulrasheed din yace zai zo gobe.
Sun samu Baba Barau a gidansa a turakarsa yana cin abinci, ya yi mamakin ganin Aisha. Amma fuskarsu kadai ya kalla ya san ba zuwan ziyara ta yi ba, ba kuma na dadin rai ba. sai ya ture kwanukan abincinsa gefe yana cewa
Indon Legas saukar yaushe?
Wajen zama ya bai wa kaninsa, sannan Aisha ta tsugunna gabansa ta gaida shi, ya ce,
In ce ko lafiya na ga Indo kamar daga sama? Ba ance min kun bar kasar ba zuwa turai?
Chapter 8 · 0% Book details