← Book details Aisha Saddiqah Part 4 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 20 OF 26

Sashe 20

Aisha Saddiqah Part 4 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Suna tafe a hanyar zuwa fadar Gombe, Malam Buhari na gulmar Prince a ransa. Yana cewa wato jinkirin aure ga namiji ba sauki gareshi ba, ranar duk da ya samu mata ko yaya take komai yarintarta sai Allah, domin kamun kazar kuku mace take musu, dubi dai yadda 'yar yarinya ficiciya ta tashi kan Yallabai Abdulrasheed, yana can ya like mata ya lalace har jirgi ya tashi ya barshi.
Yawan shekarun nan nasa, matsayi da girman sarautarsa (mulkinsa na gado gaba da baya), da 'fame' din nasa na Polo (as African Polo Legend) duk an tashi kansu cikin dan lokaci ya dawo yaro daidai ita.
Domin tareda shi Malam Buhari din Nenne tayi ta zaryar nemawa Prince auren Aisha. Bata Lagos bata Gombe, har saida ta tabbatar sun daura auren sun daukota Ilorin.
Nani Oummana ma sai daga ido tayi taga Prince ya dawo. Bayan sun riga sunyi sallama ta karshe cewa daga can zai wuce airport ya tashi gida Lagos. Ba suyi dashi zai dawo ta nan ba.
Oummana tace "Yaya haka Hammansu? Mantuwa kayi?"
Ya zauna yana cewa "to ya za'ayi? Jirgin ya tashi ya barni Oummana". Wani miskilin murmushi Oummana tayi masa, tace "garin yaya toh? Kana can kana soyayya ko?" Hamma ya dukar da kai yana
yar dariya yace, "kusan haka, ai bakya karya Oummana" Oummana ta sake yin murmushi irin nata, ita tasan watarana za'ayi haka. Domin da alama AISHA INDO SIDDIQAH! Ta shigo rayuwar Yarima da zafinta. Zata murza kambu son ranta, ranar duk da Prince ya shiga komarta. Yarinyar nada tarin baiwa da kullum take tuna mata da auren Nenne da Dade.
Kusan tace tarihi ke maimaita kansa akan Abdulrasheed Dan Idris dan Abdulrasheed Akanni. Tana fatan wannan soyayya da Prince yake yiwa Siddiqah ta dore musu har tsufansu, su zama (typical replica) na Sappa da Idrisu.
Ganin Oummana bata ce masa komai ba sai murmushi take zabgawa yace cikin basarwa da hadiye kunyar da yaji.
"Amma gobe in Sha Allah bazan yi wasa ba Oummana, morning flight dani zai tashi karfe 6am, ko sallama bazan je mata ba".
Oummana me zata yi ba dariya ba, tace "to ni me kaji nace ne? Ko nace kayi laifi ne? Haka akeso abubuwa suyi daidai. Saika koma ka daukota ka kawomin ita yau da kanka. Daman nafi so in ganku a gabana tare". Yace "In sha Allahu Oummana, Baba Yunus ma da kansa yace yace inje in daukota in kawo miki, dama na gaya musu kinason ganinta.
Da nayi sallahr Isha zan koma na taho miki da ita".
Ya wuce zuwa dakinsa na sassan Oummana kai tsaye toilet ya fada don yin wanka, don yasan a yanayin da suka kasance da Aisha yau, bai yiwuwa yayi sallah yanzu bai yi wanka ba.
Saida Umma ta tashi daga barci taga Siddiqa a zaune a gefenta, tace "har ya tafi?" Tace "eh Umma, gashi har jirgin Lagos da zai hau ya tashi ya barshi. Dole sai gobe zai tafi gida".
Sannan cikin jin kunya ta gayawa Ummanta Hamma yace zai dawo su tafi wurin Oummana anjima, ta aikoshi tana son ganinta.
Nan Haj Zainab ta hau tunanin me zata baiwa Aisha ta tafiwa da Oummana, karshe tunaninta ya tsaya a kan turarukan
da
Sandaliyyah
na jiki dana turaka data sayo a Saudiyyah. Su ta saka a kyakkyawar leda tace Aisha ta kaiwa Oummana tsaraba.
Kafin sallahr Isha Siddiqah ta yi wanka ta kara shiryawa cikin wani tattausan cotton lace mai tsananin taushi da adon kananan duwarwatsu, kalarsa Orange ne da adon (milk color) furanni, tun lokacin hajjin bara Ummanta tazo mata dashi daga Jeddah, sannan tayi sallah Maghreb da Isha.
Aisha ta dauko turarenta Fahrenheit ta feshe jikinta dashi. Kana iya jiyo sanyin kamshinsa tun daga dakinta har tsakar gidansu zuwa dakin Ummanta.
Daidai lokacin Baba Yunus ya dawo, Siddiqah tayi masa sannu da zuwa ta karbi ledar hannunsa yace mata balangun Ayuba ne ta juye su ci ita da Umma shi sun ci shi da Baba Barau. Ya kuma ce ta shirya Hamma ya kira shi zai zo yanzu su wuce gun Oummana, Mallam Yunus ya gyara zamansa akan kujera yace "toh Indo nasan ba sai na maimaita miki ki kula da kanki ba, kuma ba sai na gaya miki ki zama ambassador din kanki da kanki ba a wurare irin wadannan.
Waje ne da yake bukatar nutsuwa da kamewa wadanda bana jinki a kansu Siddiqah. Tunda gidansu mahaifiyar sa ne".
Aisha tace "toh in sha Allah Baba". Daidai lokacin Sunusi ya shigo yace "wai mijin Aisha yazo daukarta, suna cikin mota".
Siddiqah ta dauki gyalen data tanada wanda yayi matukar shiga da kayan jikinta ta yafa wato off white, nan ta dauki karamar 'hand bag' dinta tun tana gida take amfani da ita, ta dauki ledar sakon Oummana ta yiwa Umma sallama. Haj. Zainab tace,
"to sai kun dawo. A gaida Nanin".
Prince ya mika hannun damansa ya budewa Aisha kofa barin hagunsa ta shiga. Malam Buhari na kokarin fitowa don ya rufe ya hutasheshi. Shi da kansa ya rufe mata kofar. Saukin kan Prince yana kara masa kima mai yawa a idon dattijon direban. Ya koma ya zauna ya rufe kofa ya jasu a hankali suka bar Jeka da fari, zuwa babban titin da zai kaisu gidan Sarkin Gombe.
Saida Prince ya san yadda yayi cikin dabara ya sanya tafin hannunshi cikin na Aisha. Ya sarkesu, sannan ya matsesu cikin nasa hannun. Taushin hannun kowannen su ya ratsa su. Suna tafe yana mata hira kasa-kasa amma ta kasa sakin jikinta dashi kamar dazu, don Ummanta ta jaddada mata ta kama kanta, ta rike kunyarta, don gidan su mahaifiyar shi zata je kuma zuwa na farko.
Da yake duhun dare ya shigo ba kowa ya ankara da shigar su sassan Oummana ba. Suka sameta har lokacin akan dardumar sallahrta tun bayan data idar da sallahr Isha tana zaune tana lazimi bata tashi ba.
Shigowarsu tasa ta shafa addu
ar da take yi, ta mike tana cewa "Jabbama da Indo Siddiqah, barka da zuwa, Indo Aisha". Aisha tayi kasa ta zube a gaban Oummana zata fara gaisheta cikin girmamawa, tsohuwar ta kamo hannunta ta mikar da ita tsaye, ta jata zuwa kan shimfidar fata irin
traditional rug
dinnan da akeyi da fata wanda akanshi take zama a falon, da Tum-tum a kowanne gefe da gefe manya har guda hudu, Nani Oummana ta zaunar da ita a kusa da ita.
Kasancewar Oummana bata zama akan kujera sai wannan shimfidar tata. Prince ne ya zauna a kan two seater, a gabansa akwai karamin centre table dauke da
tray
shake da kayan marmari. Prince ya dauki apple guda daya jawur da ita yana yankawa da karamar wuka kaiwa bakinsa yana ci.
Yana kallon Oummana ta rasa ina taka-saka -ina taka-aje da Siddiqah, kaunar da suke mata itada Nenne, ya tabbata daga Allah ne ta dalilin son da suke yi masa. Domin bayan Oummana ta zaunar da Siddiqah a kusa da ita, sawa tayi hadimanta suka cika gabanta da kayan motsa baki na alfarma, wanda ko tabawa da hannunta Siddiqah ta kasa yi, ji take kamar yau ta fara haduwa da Oummana.
Chapter 20 · 0% Book details