Sashe 23
Aisha Saddiqah Part 4 Complete Hausa Novel · about 7 min read
A cikin jirgin, Dade da Nenne suna a first class Q suites na Qatar Airlines (aisle seats), so sun rufe kofar ya zama kamar daki suna hirarsu, Aisha kuwa na jikin window ta kwantar da kanta akan wuyan seat dinta, tayi shiru cikin tunani, tana tuna waccan tafiyar tata ita kadai zuwa Argentina, da abubuwan tarihi da suka faru cikin tafiyar. Har gobe bata san hikimarsu Dade ta tura ta ita kadai da farko ba a wancan lokacin, saidai da yake Nenne ta gaya mata daga baya cewa Allah ya jikan rai Emir ne yayi umarnin hakan.
Ita da kanta daga baya take tunanin watakila hikimar Maimartaba Emir of Ilorin na yin hakan shine basa son tursasashi yayi welcoming dinta, wato ya zamanto ya karbeta karba irin ta ganin idonsu, su tafi ya canza mata zuwa true colour dinsa, sun barshi yayi deciding yadda zai karbeta don radin kansa.
Bata san meyasa ba tafi jin dadi da kwarin gwiwa har ma da karin
self-confidence
na isa ga Hamma yau, da fara sabuwar rayuwar meaningful aure tare da shi, da ya zama cewa su Nenne ne suka kawota da kansu yanzu.
Har sukayi landing a Qatar, Aisha bata jin me suke cewa cikin hirarsu, wadda suke yi da yarbanci, wani lokacin su cakuda da harshen fulatanci, duk dai suna tattaunawa ne akan sha
anin rayuwar
yansu da matsalar auren Taiwo. Da alama a irin wannan trip din kadai suke samun lokaci su tattauna extensively akan
yansu irin haka.
Ita daga karshe ma barci tayi, bata farka ba saida aka ce cikin bututun magana kowa ya daura belt, jirgi zai sauka a Qatriyyah.
Prince daga office dinsa kusan duk bayan minti biyar sai ya duba agogon swatch din dake hannunsa, tun kafin lokacin saukarsu ya cika ya yanke duk abinda yake yi ya taho filin jirgin daukarsu Nenne. Jirgin su Aishah na sauka shima yana shiga reception na tarbar baki, don haka Prince baiyi zaman dogon jiransu ba.
Aisha ce ta fara fitowa rike da jakar hannunta data Nenne, kafin su Nenne su biyo bayanta. Prince ya runtse ido ya bude yana kallon beautiful Aishah
tana takowa majestically zuwa gareshi, da wani madaukakin murmushin SO a fuskarta, hamdala yake a zuciyarsa, sai kuma ya hango Nenne daga bayanta itama ta taho, tana taku ita kuma cike da sarauta. Prince ya karasa da hanzari ya fara rungumar Nenne, sannan Dade, kafin ya dawo ga Aisha ya rungumeta itama, yace
Aysha welcome oooo, sai yau Nenne ta gama boyon naki ta kawo min?
Dade yayi dariya, Nenne ta harareshi, Dade yace
yaushe muka boye ta din? Daga cewa zamu yi mata rakiya?
Duk suka yi dariya, nan Hamma ya karba mata jakunkunan hannunta, ya sake rungumota jikinsa yana cewa
welcome Aysha! Welcome oooo!
. Daga haka suka wuce mota.
Kasancewar Dade da Nenne duk sunada
Entry Visa
na Qatar kuma zasu yi transit na awanni hudu a Qatar sai suka yi amfani da wannan damar suka rako Aisha har gidanta.
Prince na tuki akan hanyarsu ta isa gidansa, amma hankalinsa rabi na kan Aisha wadda jikinta duk ya nuna gajiya da lalaci, ta dauko wayarta daga jakarta ta kunna, ta soma kokarin roaming layinta domin ta samu ta kira Umma da Baba Yunus, ta gaya musu saukarsu lafiya amma ta kasa connecting.
Duk wani motsi da Aisha tayi a cikin motar sai taji idon Prince Abdulrasheed a jikinta, kai har a ruhinta, ita kuma ta ki yarda su hada ido da gangan kada taje ya bata kunya, don tun daga rungumar da yake mata a gaban su Nenne ta san komai ma zai iya (that
s his real identity of Yoruba demon), gashi duk dagowar da tayi sai ta hango Nenne ta cikin mudubin gefenta, wadda ke zaune a kujerar bayanta, Nenne waya take yi da Fatima a lokacin bata maida hankali a kansu ba sam. Aisha ce dai duk ta ji ta takura da idanun Prince dake yawo a jikinta. Kuma idanun nasa sun rikitata.
Finally, Abdulrasheed ya kashe motar a muhallinta wato
parking lot
na kofar gidansa, yaron dake kula masa da gidan wani baqar fata ne dan Senegal mai suna Zaid, kuma har ila yau, Zaid is a good Chef for him, tun kafin su iso ya gama girki na musamman na larabawa, ya shirya a dining sai jiran isowarsu bisa umarnin Ogansa, tunda safe Zaid ya shiga kitchen yake aiki saboda zuwansu. Zaid ya shirya Lamb mandi, kebabs, fatoush salad, humus, Baba ganoush, ga kuma desserts da bakhlava ga arabic coffee. Duk ya tanadar musu kamar mai hada wata
yar kwarya-kwaryar get together. Saidai ba wai yayi da yawa bane daidai cin abincin mutum 4-5. So already table was set before their arrival.
Suna shigowa Prince ya budewa Aisha dakinta ya shigar mata da akwatinta ya ce
your room
. Su Nenne ma, ya bude musu wani dakin yace su shiga su yi alwala da sallah, nan ne Nenne ta gane Hammah yayi gyaran gida sosai, ta yaba mashi bisa wannan kokarin ta kuma dan tsokane shi da fulatanci
da angon Aisha ka sha kamshi, na Siddiqah bada kanka a sare
, nan dai duk suka yo alwallah har Aisha, Hamma ya jasu sukayi sallahr jam
i gabadaya, sannan suka fara cin abinci cikin nutsuwa suna yi suna duba agogo.
Da suka kammala Nenne tace a bata
black tea
(lipton) ta kara, saboda Nenne bata shan coffee ita. Prince da kansa ya dafo shayin a kettle din dafa ruwan zafi, ya hado ma Nenne a kan tray da mug cup da liptons kala-kala na alfarma da yake ajiyewa don baki don shi in ka cire chamomile da lavender ba shayin da ya ke sha, ya ajiye mata bakidaya liptons din kala kala don ta zabi wanda tafiso cikin su, (and honey instead of sugar) don Prince baya shan sugar sai zuma.
Nenne na sipping zazzafan lipton Dade ya hada Prince da Aisha yana musu nasiha a tare. Ya ja hankalinsu kan su hada kansu su zauna lafiya, su zama sirrin juna, su kuma taimaki junansu akan komai. Yace ma Aisha, ko me Prince zai mata na rashin kyautawa ta doshesu kai tsaye. (They are always there for her) muddin suna raye. Ya roketa kada ta kara dosar iyayenta da matsala inba a inda taga sun gaza daukar mataki ba.
Shikuma Prince Dade yace dashi
har kullum ka tuna Aisha mace ce, kuma mai kankantar shekaru a kanka.
Yadda duk ka mikar da ita a haka zata girma.
Don haka sai ka nuna mata abinda kakeso da wanda baka so a hankali.
In tayi kuskure ka nuna mata ta lalama da jurewa kuruciyarta.
A karshe suka saka musu albarka shida Nenne, a bisa biyayyar da suka yi musu, suka roki Allah ya basu masu yi musu mafiyinta da gaggawa. Ya kuma sa
yansu su kasance nagari masu bin iyaye kamarsu
Dade yace
saura ke Nenne ko?
Tace
ai you have said it all Dade, banida abin cewa, addu
a kawai zanyi musu, wadda kullum bana fasawa. Allah yayi musu albarka da zuri
a dayyiba albarka Annabijo
Daga haka duk suka mike, Prince ya dauki mukullin mota don ya maida su, yace ma Aisha,
Ayshah ki rufe kofar falon ta ciki, in na dawo zan bude da key dina, idan Zaid ya tattare wajennan ya tafi
. Ya gaya mata akwai yaron gidan, mai suna Zaid, amma baya kwana a gidan, da safe yake zuwa ya tafi karfe 6 na yamma in ya gama masa dinner.
Har sun fita tare dasu Dade sai yai excusing dinsu ya dawo kamar yayi mantuwa. Da sassarfa ya isa ga Aisha ya rungumota ta baya tana kokarin rage nauyin laffayar jikinta. Aisha tace cikin
yar rawar murya
Hammah, mantuwa kayi? Kada suma kasa jirgi ya tashi ya barsu fa?
Prince kamar bai ji korafinta ba, ya sunkuya ya sumbaci bakinta dake maganar cikin shagwaba so lightly yayi sumbar, sannan a daidai kunnenta yace cikin shauki.
Welcome Ayshah.. welcome to your abode! The lady of my heart, love of my life, mother of my children, the one that has completely changed and shaked my whole universe. I am coming back soon to welcome you Baby, kin ji?
Ya sake kai mata sassanyar sumba a wuyanta da lips dinta, amma Aisha bata barshi yayi nisa ba ta kwace bakinta cikin jin kunya, tace cikin shagwabar da bata zuwar mata sai in tana gaban Hammah Abdulrasheed kadai.
Hamma Abdul mana?! Dade da Nenne, suna bakin mota suna jiranka fah?!
Prince da kyar ya juya ya fita kuma da baya da baya, yana sumbatar hannunsa yana huro mata iskar, ita abinma sai ya bata kunya da dariya, tasa tafukanta ta rufe fuska tana kallonsa ta tsakanin yatsunta cikin idonsa da wani irin kallon SO, wanda yasa Prince yin tuntube a bakin kofar fita.