← Book details Aisha Saddiqah Part 4 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 5 OF 26

Sashe 5

Aisha Saddiqah Part 4 Complete Hausa Novel · about 5 min read

ah Nenne na yafe, ta zauna kawai, na gode
Wannan gwasalen da Hamma yayiwa rakiyar Aisha, duk ya faru akan idon amare Princess Fatima da Princess Firdausi, don tare aka zauna cin abincin har dasu gabadaya.
Abin yayi matukar yiwa Fatima dadi, na yadda Prince ya nuna bai damu da Aisha a gaban kowa ba. ita bata fahimci haushi yaji don Aisha tace da bakinta bazata bishi ba. Har ta samu abin adarwa a gaba.
Fatima na komawa dakinta ta kira Aunty Taiwo, tana mayar mata da yadda aka yi, da irin gwasale tayin binsa gidansa da Prince yayi ga Nenne da Aisha, sai Taiwo tace da Fatima,
ewo, to dama nifa na san Kehinde sarai, nafi kowa saninsa, saninda ko Nenne bata yi masa ba, ba son zama da yarinyar nan yake ba, biyayya yake yi musu don a rabu lafiya da kafaffun iyayenmu da basa shawara, su Nenne ke faman cusa masa ita kamar dusa, kamar ance lafiyayyun mata
yan asali na manyan gida sun gama karewa a duniya.
Na rantse idona idonta a Lagos ko Ilorin in ta sake tazo, sai nayi mata wulakanci da kaskancin da bazata kara kuskuren zuro jiki cikin zuri
ar Akanni ba, balle ta wani kwashi siraran kafafunta tazo mana biki irin wannan na girma
A dakinta na baya wato dakin Kiki aka sauketa, kafin ta kwanta saida ta kira Ummanta ta gaya mata saukarsu lafiya a Lagos, sannan ta kira Hamma don tayi masa saida safe ta kuma bashi hakuri da kalamai, amma sai ta samu ya kashe dukka wayoyinsa.
Haka ta kwana da tunani da damuwar Hamma a ranta.
Washegari da safe ita da Nenne ne suka shirya abin karin Dade da Hamma, sai wajen karfe goma na safe Prince yazo gidan kuma a gurguje suka karya shida Dade zasu fita, bayan yabi Nenne dakinta sun gaisa, yanaso ya tambayi Aisha amma ya dake. Sai gata tana shigowa dakin Nennen dauke da lemun tuffah da sassanyar madarada tanbulan na tangaran akan karamin tray, ta gefensa ta wuce zuwa ciki, taci ado har ta gaji gabadaya ta saje da
yammatan amarya da suka cika gidan tun jiya.
Ta ajiye a gabansa, don tun safe take dakon shigowarsa duk ta damu, tace a ladabce
Hamma ina kwana?
Yayi mata wani kallo yace
lafiya kalau, yaya gajiyarki?
Nenne aka kirata a waya sai ta fita daga dakin tana amsa wayar.
Aisha bata yi aune ba taji Prince ya kamata ya mikar daga durkuson data yi a gabansa ya jata zuwa kusurwar dakin ya matseta sosai a jikinsa, sannan ya manne ta a kirjinsa da wata zazzafar hug, ya rage tsaho ya sumbaci lips dinta lightly, yace,

Aisha jiya banyi barci ba isashshe saboda rashin ki a gadona Aisha, I missed you and your sweet lips, me
yasa kika yimin hakane wai?
Ya yi mata wani kallo na so da sha'awar da baisan yaushe ya fito daga idanunsa zuwa nata ba, saida Aisha taji tasirin kallonnan har spine dinta, tsigar jikinta saida ya tashi yarrr, Hamma ganin haka ya sake manne bakunansu wuri guda yana kissing lips dinta hungrily, wannan karon zazzafar kiss yake extending Wanda ya rikita Aisha bakidayanta. Duk da haka tunanin a inda suke ya hanata nutsuwa ta amshi sakonnin nasa. Aisha ta soma kokarin kwatar kanta tana fadin.

Please don Allah Hamma ka bari, ka sakeni kada Nenne ta dawo. Dakin Nenne ne fa!
Hamma yace
I don
t care, ai gara ta gani ta san yadda kuka taru kuka kwareni jiya, I missed your warmth, shine jiya kika ce nan zaki zauna ko? Don kawai kinga ina shirin angwancewa? Wannan ai mugunta ne Aisha.
Hummm! Ni na manta ma I am pissed at you na tsaya Ina romancing dinki
. Aisha tayi wani murmushi kawai ta kalleshi
ni dai don Allah Hamma ka sakeni kunya nake ji
ya sake mata kiss a kasan wuyanta sannan ya saketa jin kamar motsi a bayansu. Ashe Firdausi ce ta shigo neman Aisha, ganin abinda ke faruwa tayi maza tayi excusing kanta da gaggawa ta juya tana murmushi.
Firdausi na fita Nenne ta dawo, sai Aisha ta gusa ta basu wuri. Har Hamma ya gama gaisawa da Nenne ya fita daga gidan, wanda ya soma dinkewa da baki musamman kawayen amarya dana Nenne, bai kara ganinta ba. Kuma a washegarin ranar first flight ya tashi dasu zuwa Ilorin, shida Dade, Nenne, Aisha da amaren domin su samu addu
ar arba
in kuma a dauro auren a fadar Ilorin.
Da hantsin ranar suka shiga Ilorin Emirate, Aisha tana like da Nenne duk inda tasa kafa nan take mayaswa. A yanayin kalar fatar jikinsu da kamanninsu na Fulani sai suka fita dabam a gidan, kamar
ya da uwarta. Wadanda basu san matar da aka aurawa Prince bama a gidan a ranar suka ganta, masu yabawa nayi haka masu gatsinen yarbawa na kankantar Aisha. Amma maganar rashin wayewa ya fara barin jikin Aisha ta yi fes da ita ta kara cikowa ta fara cika idanun mai kallonta. Prince yana can fada tareda Uncles dinsa do a ranar ne ake shawarar wanda za
a bawa sarauta a cikin
yan Emir. Idris Akanni y ace a
ah, ko dama Emir ya dade yana gaya musu su cire Idris da dan sa daga sha
anin sarauta. Basu kara yarda da hakan ba sai yau da Dade ya fitittike yace bazai karba ba, baida ra
ayin sarauta ko kankani, don haka ya barwa kaninsa mai bi masa wato Abdulyaqeen Akanni wanda shine Turaki of Ilorin.
Da wannan aka bar zancen cewa washegari bayan addu
a arba
in din za
a zarce da bikin nadin sarautar da daurin aure.
Da farko a dakin da Nenne ta sauka Siddiqah take amma da Aunty Taiwo tashigo yiwa Nenne barka da zuwa, suka gaisa, ta tambayeta Hakeem tace yana fada, tana kallon Siddiqah a kaikaice, taga alamar a dakin Nenne take nufin zata sauka sai tace da Nenne cikin yarbanci da tayi tsammanin Siddiqah bata ji sam.
Chapter 5 · 0% Book details