Sashe 7
Aisha Saddiqah Part 4 Complete Hausa Novel · about 10 min read
Kuma kamar yadda kike ta tutiya kan cewa baya sona, haka zalika nima baya cikin lissafina balle na irin mazan da nake so, ki tambayeshi kiji biyayya duk mukayiwa iyayen mu, saboda sun isa da mu. Daga yau na bar miki shi. Gashinan ki jika shi ki shanye
Tana gama fadin hakan ta wuce ta bar musu dakin, ga dukkan mamakin Taiwo sai taga Prince ya bi bayanta yana
Aishah Please wait
Don Allah tsaya
ko kallonsa Aisha bata yi ba ta kara sauri, ta kara da gudu-gudu, shima ya daga kafa ya bita yana
please listen to me Aisha
. Yayi sa
ar riko gefen gyalenta, Aisha ta juyo a fusace tace
cikani, daga yau na gama wannan auren
A lokacin sun kawo kofar dakin data baro Nenne. Kalaman Aisha na karshe a kunnen Nenne suka sauka, inda tace.
na gama auren nan, na barwa Aunty Taiwo dan uwanta Kehinde ta jika ta sha, har abada baa auren!
Da sauri Nenne ta taso suka game ita dasu a bakin kofar, ganin yanayin da Aisha ke ciki da rudewar dake fuskar Hamma saida gaban Nenne ya fadi.
Ta kama hannun Aisha suka shiga cikin dakin Prince da hanzari ya rufa musu baya.
Nenne na jin irin numfarfashi da ajiyar zuciyar da Siddiqah ke sassaukewa a jejjere, ta durkushe a gabanta, ta hada hannayenta wuri guda cikin roko tace.
Nenne ke uwace mai adalci a wurina, babu abinda zaki sani in ki yi, amma don Allah ki barni naje gun Ummata. Nayi rantsuwa a gidanmu zan kwana yau. Kar kisa nayi kaffara.
Ni Nenne wallahi Allah tun ranar da kika kawoni Lagos da niyyar zaki kaini asibiti, har aka kai ga maganar aure, aka yi aka dawo, duk da banaso har raina, ban taba jin zan iya yi muku gardama ba. kuma na karbi kaddarar auren a haka, nima ai da wanda yake so na din nake kuma son shi aka raba mu amma ban yi bore ba.
Amma Nenne yau Maman Kiki ta tabo martabar wadanda ba
a iya taba su in hakura, inna hakura ma ji zan yi kamar nayi gagarumin laifi ga iyayena, don haka Nenne don Allah zan tafi, na rantse bazan kwana garin nan ba
Jikin Nenne yayi sanyi kalau, at the same time she is so proud of Aisha, domin ta haifu, ta cika diya.
Prince na kallon Nenne da dukkan hope na cewa zata lallashi Aisha ta shawo masa kanta ta saurareshi. Shi meye laifinsa a ciki? Amma sai gani yayi Nenne ta dauki wayarta tayi kira.
Bai dai san wa ta kira ba yaji tana
lallai-lallai a nemo jirgin zuwa Gombe yanzu, idan ma babu direct a nemi na Abuja daga nan sai ta kara shiga wani
Sai Prince ya dubi Nenne a firgice, yace
Nenne me kike nufi? Gidan zata tafi da gaske? Ta gama auren fa tace, ni kuma fa Nenne?
Gabadayansa a daburce yake, kansa da duk wani lissafinsa ya kwance, duk wani azanci da tsinkaye da kunyar idanun mahaifiyar tasa sun kwace daga hannunsa.
Nenne bata ko bashi amsa ba tace
Aisha dauki kayanki kinji, muje driver da Dade suna waje suna jira zasu saka ki a jirgin Gombe
Dadi sosai ya kama Aisha sai lokacin ta samu hawaye suka zubo, tafe da wata sassanyar ajiyar zuciya, tace
nagode da uzuriki, amma ni Nenne yadda nazo haka zan koma Gombe, ko tsinke bazan dauka ba
Ta dauko wayarsa da ya bata daga jakarta ta russuna ta ajiye a gabansa ba tare data kalli yanayinsa ba. Saura kadan Prince yayi hauka a cikin kansa, musamman ganin Nenne tasa hijab ta kama hannunta suka fice suka barshi tsaye a wurin.
Sai kawai ya fito daga dakin shima a matukar fusace, ya san yayi kadan ya dakatar da Nenne yanzu, a yadda yaga fushinta da bacin ranta irin wanda bai taba gani ba, to balle kuma Dade mijin tace din Nenne, wanda sai abinda Nenne tace yake amfani dashi. Don haka maimakon yabi bayansu, dakin su Taiwo ya nufa. Yana tafe da sassarfa yana tambayar ransa me zai yiwa Taiwo ya huce?
Ance ba
a raba hanta da jini, ance blood is thicker than water
wai ba
a batawa da
yan uwa saboda mace, komin son da ake yi mata. Amma shi yadda yake jin matukar bacin rai da soyayyar Aisha data bijiro masa yanzunnan, mai raba shi da Taiwo dinsa yau sai Allah.
**** **** ****
Tun kafin su Nenne su karaso jikin motar daya daga cikin direbobin Emirate da Dade ya kira ya bude musu kofar gidan bayan wata jibgegiyar mota baka wuluk suka shiga har Aisha wadda hannunta ke cikin na Nenne. Direban ya ja motar cikin nutsuwa suka bar fada. Har sai da suka dauki hanyar airport din Ilorin sosai, suka yi nisa fintinkau da masarautar ta Ilorin, sannan ne Aisha ta ji ta (at ease) kuma bugun kirjinta ya soma lafawa, Aisha ta yi ajiyar zuciya na samun kwanciyar hankali, saboda abinda take so Nenne ta yi mata nan take, Nenne ta dubi halarci, kauna da amana ta yi mata kan ta rufe baki. Me za ta ce da Nenne Sappa? Ban da Allah ya ja kwananta?
Tana jin Nenne da Dade suna magana amma da harshen Yoruba suke yi, (which means) ba su so ta fahimta sosai, don kuwa yarbancin mai zafi da sauri da sauri sosai suke yi. Amma a cikin dan abinda take tsinta yanzu a harshen ta fahimci kamar Dade na rokon Nenne ne akan ta bari a yi komai a hankali kada ta biyewa fushin Siddiqah, ta bata hakuri su wuce Lagos don yana so ya fahimci meye matsalarta data sa aka taso tafiya Gombe haka bagatatan, suna tsaka da sabgar biki, kuma daga ina matsalar take?
Sai taji Nenne na cewa,
ah Dade, yi hakuri ka barta ta tafi, ni a wurina tafiyar Siddiqah Gombe yau ba makawa sai wani babban ikon Allah mai karfi da ya gagari iyawata, matsalar daga Taiwo take, zaka fahimci komai daga baya don ba yau matsalar Maman Kiki ta fara akan Siddiqah ba, na yau din na fahimci yayi tsamari ne tunda har kaga Siddiqah tayi fushi, amma a halin yanzu bazan iya yarda da komai ba banda cikawa Siddiqah burinta
Ta Lawanti International Airport. Dade ya yi ma Siddiqa tikiti, babu ko waya a hannunta haka ta shiga jirgin, Nenne ta gaya mata tana sauka Malam Buhari direban Nani Oummana zai zo ya dauke ta daga gidan Sarki. Ya kaita har zuwa nasu gidan.
In kaga idanun Siddiqah a lokacin a soye suke kamar gyada marau-marau, babu ko kyallin hawaye a cikinsu. Na Nenne ne fal kwalla, suka yi sallama ta shiga jirgin Mangal. Dade dai yana gefe yana kallonsu ya rasa abin da ke masa dadi, don Nenne har zuwa lokacin ba ta yi masa wani cikakken bayani da zai gamsu da tafiyar Siddiqah Gombe kuma ita kadai ba, don ta ce ita ma ba ta gama fahimtar matsalar ba kawai ta yi wa Siddiqah abin da ta ke so ne kada hawan jini ya kama yarinyar, a yanayin da ta ganta kamar mai tashin iskokai sanda ta ke rokonta ta maida ta gida. Hakika Nenne ta tsorata, kuma ta dauki laifin duka ta dora a kan Abdulrasheed, duk da a hargitsatstsen bayanin Aisha ta fahimci ita dasu Taiwo ne.
Siddiqah na sauka a Gombe ta tarar da direban Nani Oummana watau Buhari ya dade yana jiranta, wanda dama ta sanshi, duk zuwan da suke yi Gombe da ma shi yake daukarsu zuwa gida haka in zasu koma Lagos shi yake kaisu airport.
Suna tafe a hanya Siddiqa banda ajiyar zuciya ba abin da ta ke yi. Wata irin ajiyar zuciya mai tafe da numfashin fushi da bacin rai. Ji ta ke a ranta, daga yau aurenta ya gama karewa da Prince Abdulrasheed ko za
a mutu ko za
ayi rai.
Nenne kuma a sanyaye ta kira Hajiya Zainab, bayan tasowar Siddiqah sukuma suna hanyar komawa Emirate, ta gaya mata komai a sakaye. Inda ta ce (murya ba karsashi)
Zaynaba ga Siddiqah nan zuwa, ki yi wa Mallam Yunus bayani, Siddiqah ce ta daga hankalinta sai ta taho gida, muna tsaka da bikin twins a Ilorin.
Ta ce ba ta bi ba
asin maganar ba tukunna sai sun koma gida daga raka Siddiqah, ta dai biye wa Siddiqa ne don kada ta yiwa kanta illah, in ta koma gida daga airport din zata bincika ko me yake faruwa kuma za ta dauki matakin da ya dace, insha Allahu.
Nenne tace ma Umman Siddiqah.
For now Zaynaba, ba don ni ba ina so ku taimakeni, ku tausasawa bakuncin na Siddiqah zuwa gareku, ku karbeta babu tambaya babu tuhuma, naga kamar tana da iskokai idan ranta ya baci, ku karbeta da hannu bibbiyu kada ku ce mata don me, yanzu zan koma gidan Kakannin nasu Hammansu, in binciki Taiwo da Firdausi inji me ya faru, saboda na tara al
umma ciki da waje suna jirana da ni da kaina zan rakota, in yaso idan an gama biki an kai amare dakunansu zamu san kwakkwaran matakin dauka.
Tun daga nan Hajiya Zainab ta san cewa ba lafiya ba. Bata san Siddiqah da wasu iskokai ba amma tana da fushi in an kaita bango mai wuyar sauka. Don a saninta Siddiqah ta gama kwantar da hankalinta da auren Prince. Kullum ta kira ta sai ta ce
Hamma na gaisheta, Hamma kaza da kaza.
Ko kwanaki biyun bayannan sun yi waya ita da Siddiqah tana farin ciki tana dariya ta ce mata sun sauka a Lagos ita da Hamma Prince. Bikin kannensa Princesses. Amma bata jin zasu biyo ta Gombe in an gama, don yace daga gama bikin immediately Qatar zasu wuce bakin aikinsa don hutunsa ya dade da karewa. Har tace ma Umman da zata yarda da ta sa Hamma ya kawo mata Umma har Qatar taga muhallinta. Umman tace mata a lokacin
ashe ni Zaynaba kenan na zama ba bafullatana bace tunda zan biki gidan miji
. Siddiqah tayi ta dariya tana fadin
Umma fulani fa sun waye, sun daina irin wannan yanzu, balle ni Petel dinki wadda ni ce ta fari nice auta, bakiga yadda Nenne take kula da Hamma ba shi da yake babban dan ta ma, bata iya wuni guda bata san me yake ciki ba
Haka kawai kuma ba za ta zo lokaci guda suna tsaka da biki mai muhimmanci irin wannan ta dagawa Nenne hankali ta ce lallai a maido ta gida ba. Ruwa dai baya tsami banza. Koma dai mene ne za ta jira isowar Siddiqah lafiya, ta gaya mata me akayi mata ta ji.
Mallam Buhari direban Oummana yana kashe motar a kofar gidan su Siddiqah, tayi wuf ta bude kofa ta fice. Siddiqah ko sallama ba ta tsaya yi wa Malam Buhari ba ta shige gidansu ba godi bare an gode. Shi kansa Malam Buhari yayi mamaki don ya san ba haka yasan yarinyar ba. A tsakar gida suka yi kacibus da Ummanta, wadda jin dirin tsayuwar mota ya sa ta tasowa da sauri har tana tuntube. Da wata irin azama Siddiqah ta shiga gida tayi karo da Umma, ai kuwa ta rungume Ummanta sosai, Umman ma ta rungumeta tana hamdallah na saukarta lafiya.
Sai a lokacin Aisha ta samu kuka dan gaske ya balle mata. Umma na cewa cikin fillanci,
Petel dina, mi ya hwaru? In ji dai lafiya lau kike, ba wasu iskokai, kuma kin zo lafiya baki samu matsalar komai a hanya ba?
Aisha babu baki sai na kuka, wanda tun a Ilorin ya tokare mata a makogaro, sai yanzu da ta ji ta a kirjin Ummanta, ta samu
yanci da sukunin fitar da shi, ko ta ji sakayau da sanyi a kirjinta.
A haka suka karasa cikin falon Umma, Hajiya Zainab na rike da ita ta zaunar da ita a doguwar kujera, itama ta zauna a gefenta. Siddiqah an samu abinda ake so, wato anzo inda za
a yi shagwaba son rai, a kuma biye mata, nan ta yi ta rusawa Haj. Zainab kuka, tana cewa auren ta da Hamma ya kare, Umma ko za
a yankani ba zan koma ba.
Ita gara a ce ita aka taba aka ciwa mutunci basu ba, da ko daga ido bazata yi ba kuma abin ba zai dame ta haka ba.
Hajiya zainab ta ce,
Yi shiru Petel ki gaya min Abdulrasheed din ne ya yi miki laifi ko waye? Me yayi miki haka? Mutumin da na lura yana da kirki sosai