← Book details Aisha Saddiqah Part 4 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 1 OF 26

Sashe 1

Aisha Saddiqah Part 4 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Root Entry
WordDocument
0Table
Data
AISHAH-SIDDIQAH

4

SUMAYYAH ABDULKADIR
[email protected]
[email protected]
TUNASARWA/JAN HANKALI
a rubuta littafin AISHAH-SIDDIQAH don cin zarafin kowacce kabila ba, ko don nuna wata kabila ta fi wata daraja a tsakanin kabilun Najeriya ba.
Kyakkyawar manufar dake kasan labarin itace dabbaqa kalmar WA-ZO-BIA da fadakarwa cikin nishadi akan kabilancin da ake nunawa ita wannan kebantacciyar kabila dana dauka, da kuma wanda suma suke nunawa ga kabilar hausawa.
Labarin AISHA-SIDDIQAH labari ne da aka gina shi kacokam akan manyan kabilun Najeriya guda uku, don son samar da fahimtar juna da rage tasirin kabilancin da yayi katutu a zukatanmu ga junanmu.
Asali mun san cewa Najeriya kasa ce bata kabila guda ba, bata yare ko harshe guda ba. Bincike ya nuna kusan kabilu 371 da yarurruka sama da 500 suka hadu suka mallaketa, wadanda suka fi yawa sune Hausa, sannan Yoruba, Igbo da kuma Fufulde.
In haka ne kenan babu wadda ya kamata ace tana faharin tafi wata, ko tata itace kan gaba ko mafi daraja, in dai Allah daya muke bautawa sai mu rike ayar
Inna akramakum Indallahi Atqaakum
Idan kuma ba addini daya ya hadamu ba, sai mu dauki ayar
Lakum Deenukum Wa liya Deen
nan ma sai kaga an zauna lafiya da juna.
Fatan marubuciyar shine Hausawa mu daina kabilanci, in bazamu iya dainawa ba mu rage shi, sauran kabilun suma su rage nasu kabilancin ga hausawa, ta hakane kadai za
a samu hadin kai da fahimtar juna a tsakanin WA-ZO-BIA wadda zata iya zama jagora wajen cigaba da haifar da auratayya da kyakkyawar mu
amala tsakanin kabilun musulmai a duk inda suke a kasar nan. Don haka kada kayi tsalle ga tafiya karshen labarin ko ka dauki wani abu ya zama cin zarafi ga yarenka ko kabilarka ba tareda ka ga karshen littafin ba. Taku har abada.

Takori Sumayyah AbdulQadir.
SADAUKARWA
Aisha-Siddiqah ta sadaukar da labarinta ga daukacin mambobin whatsapp group na TAKORI
S LOUNGE bakidayanku. Allah ya bar zumunci da kauna har
ya da jikoki.
KIYAYEWA
Hakkin mallaka abin kiyayewa ne ga marubiciyar littafin, ban yarda a karanta shi a kowacce kafa ta sadarwa ba tare da rubutaccen iznina ba. Yin hakan ya sabawa doka ta shari
ah kuma abin tuhuma ne daga lauyana Barr. Sadiq Rufa
I Wali.
GODIYA DA JINJINA
Godiya da jinjina ga aminan kwarai wadanda suka taimaka matuka gaya wajen shawarwari, tacewa da gyarawa. Dr. Amina Jafaru Musa, Barr. Azima Musa Abdullahi, Aisha Muhammad, Maryam Yusuf Abubakar, Haj. Zainab M. Ahmed da Bilkisu Askira.
In tsaya ina ce muku na gode kuma kunsan yayi kadan, saidai kawai in jinjina muku bisa namijin kokarinku akan ingantuwar littafin AISHATU SIDDIQAH.
KAFIN MU FARA INA TALLATA MUKU AISHA LAME (ORIGINAL ORIFLAME AMBASSADOR)
Kina neman jakadiyar oriflame ta kwarai? Kinason mayuka da zasu dace da launin fatarki a wannan lokacin na zafi kona sanyi? Kinason kamshi na alfarma? Kinason supplements ingantattu na wellness and meal replacement ga masu bukatar weight loss and weight control? Kayan kwalliya na kerewa sa
a? Kina bukatar zama Dawisu sarkin ado? Kawai tuntubi AISHA LAME a lambar waya 07036662633 zaki samu duka wadannan cikin farashi mai inganci da kyakkyawar mu
amala. Aisha lame karshe ce wajen baiwa faat hakkinta ku tuntubi Aisha ku zo ku bani labari.
-Takorinku

AISHA SIDDIQAH 4
Haseenah na ganin fitowarsa ta mike tsaye with great excitement a kan fuskarta. A take sai Aisha taga Hamma ya wani irin daure fuska. Gabadaya ya koma babu annuri. Ya fito a basarakensa sosai. Yau sai taga ma Hamma yafi mata kama da yarbawa akan Fulani. Fuskar nan ba rahma ko kadan ko kankani. Yace cikin wata irin murya.

What are you doing here?
Haseenah tace
kayi hakuri Prince, just give me few minutes of your time. Ta
aziyya ce nazo nayi maka na Emir. Aunty Taiwo ta gaya min kana Argentina, nikuma na zo yin wani project daga office dinmu, nace zan zo har gida in yi maka ta
aziyya kuma in yi amfani da wannan damar in baka hakuri Prince. Am sure she told you sakon dana bata gareka
Sai Hamma ya zauna gefen Aisha yana kokarin cooling anger dinsa, ita kuma Aisha taji kamar an kada mata kararrawa a cikin kanta, domin nan take ta ayyana itace tsohuwar budurwarsa Haseenah Ambursa, wadda Kiki ta bata labari. Don haka nan take sai ta mike, amma sai Hamma ya rike hannunta, ya saka idanunsa cikin nata yace
ina zaki mu da zamu fita kuma?
tace
naga kayi bakuwa ne Hamma, zan kawo mata ruwa da lemo ne in baku wuri
Sai Prince yace mata
zauna, ba shan ruwa ya kawota ba, yanzu zata tafi
Ya mayar da ita zaune inda ta tashin, zuciyar Aisha tayi mata nauyi, ba don komai ba sai don tuno soyayyar da ake bata labarin Hamma ya yiwa Haseenah, har shine silar da yaki aure shekaru goma sha uku, a zuciyarta tace ita daman matar cushe ce a gareshi, kila yanzu Haseenah ta dawo rayuwarsa kenan, dan bond din da suka fara developing ita dashi zai bi iska. Zai tashi a banza. Mai wuri ya zo mai tabarma sai ya nade kayarsa.
Sabon takaici ya lullubeshi na yadda akayi Haseenah ta samu address dinsa na Argentina gun Taiwo, ta shigo gidansa na Sunnah bada izninsa ba. A ran sa yana ayyana yadda zai ci uwar Pareto ciki da waje, da yake budewa kowane kare da kowanne doki gidansa ba tareda ya masa izni ba.
Haseenah ta roki samun privacy na tanaso suyi magana ita da shi, wani asararren kallo yayi mata yace.

I have got nothing to hide from my wife
Nan duk Haseenah tabi ta sha jinin jikinta, cewa wannan sabon Prince Kehinde Abdulrasheed ne, ba wanda ta dade da sani ba.
Jikinta yayi mugun sanyi. Ala dole ta fara fadin abinda ya kawota akan idon Aisha.
Na farko ta bashi hakuri, kan abinda ya faru shekaru sha uku a baya, tace babu ranar da bazata wayi gari ta kuma wuni tana nadama ba, amma bata da excuse, bata ma son kawo shi. Ta yarda kaddararsu ce tazo a haka amma ba don rashin so tayi masa abinda tayi ba
Sai Haseenah tayi shiru, sannan ta kalli idanunsa tace
Kehinde, you will always be the one that has got my heart, and I am so sorry for being the reason you stayed this long without a wife.
Na tabbata nima hakkinka keta bina na kasa aure sai yanzu, ina ji a raina kullum in har ba na nemi gafararka ba zan fara rayuwa ne akan karya. Ka yafemin. Yarinta ce da shaidan suka taka rawarsu gareni a lokacin.
Amma na maka alkawarin cewa na dau darasi na domin Tokumbo bai aure nib a bai kuma kara waiwayata ba bayan ya gama kwasar rabonsa a tare dani
Prince ya kalleta sai yaga tana share hawaye, a zuciyarsa yaga zallar nadama a tare da ita da talalar Ubangiji bayyananniya. Haseenah duk ta tsofe, wannan kyan duk ya dushe. Ba dai cikin wahala take ba, amma kuma duk kyannan na kuruciya babu shi a tareda ita.
Sai kawai ya daga kai ya kalli Aisha, a take sai yaji duk wani bakin cikinnan na Haseenah yana
melting
, har ya zamo babu shi babu sauransa ko kadan a tare dashi.
Yayi duba ga irin kyawun da Aisha tayi a gabansa, tana sanye cikin shirin atamfa
super exclusive, looking beautiful and innocent, yaga cewa in bai yafewa Haseenah bama kamar ya yiwa Allah butulci ne. Saboda ya bashi abinda ya fita sau dari. Wannan shi ake kira
blessing in disguise
Da wannan tunanin sai kawai Prince ya dubi Haseenah yace.

Haseenah Allah ya yafe mana bakidaya, yes I was hurt, amman in gaya miki gaskiya I have no ill feelings towards you now, Allah ya wanke min zuciya yayimin sakayya da AISHAH-SIDDIQAH...
Ya dan kalli Aisha da itama shi take kallo, yace
na yafe miki Haseenah ko don albarkacin Aishah.
Saboda ba don kinyi abinda kika yi din ba, da ban hadu da ita Aisha ba, so in this way, I must say a big THANK YOU! Allah kuma yasa ku zauna lafiya keda mijinki din
Prince sai yaga Haseenah tana kallonsa kawai, ta sake share hawaye tace
thank you
. A ranta tana mai kissima babban rashin datayi na Prince Kehinde, wanda ta tabbata ko shugaban kasar Ingila taaura bazata maida kamarsa ba.
Prince ya mike ya dubi Aisha yace
muje ko?
Sai Haseenanma ta tashi tace
to na barku lafiya, Madam Aisha bye, till next time
. Prince yace
ah Haseenah babu next time, please, kamar yadda nace
I have no ill feelings towards you, haka babu alaqa, na yafe miki, but please don
t show up in our house again
Tace
in sha Allah. You really deserve to be happy, Aisha congrats to you, you don
t know what God did to you!
Daga haka sai tayi wani murmushi mai daci ta tafi.
Aisha a ranta taji dadin yadda Hamma ya hanata tafiya, ya girmamata a idon Haseenah, amma duk da haka wani irin kishin Haseenah take, ta hau ayyana irin mugun son da Prince yayi mata, data tuna hakan sai taji wani bala
in haushi a makogaronta.
Ta koma tana cewa a ranta meyasa ma take jin haushin? Itada ba son Hamma take ba. wata zuciyar tace
ai dai mijinkine da so ko babu SO. Haka dai, duk ta zama confused, taga cewa ko Ishaq da take ikirarin ta so, bata jin wannan zafin zuciyar a kansa da wata.
Haseenah na fita, Aisha ta zame hannunta daga na Hamma, ya kalleta yace
muje
tace
nidai na fasa zuwa ko
ina, sai ka dawo kawai, I don
t feel like going out any more
Hamma yace,
Why?
tace
hakanan, ban jin dadi sai wani lokacin
Ta soma warware daurin kallabin data yi.
Nan Hamma yaso ya gane meke faruwa. Ya tuna ranar da yaji tana maganar Ishaq, abinda yaji a ransa, balle ita yau dungurungum Haseenar ce tazo. Sai yace.

Aisha listen to me, Haseenah wata long chapter ce a rayuwata da bani ko son tunawa, don Allah ki fahimta, don
t read too much into it
Chapter 1 · 0% Book details