Sashe 9
Abulle Ta Mai Unguwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Zama waje uku suna da amfani. Zama a makaranta, zama a mahauta, da zama a fada. Zama a makaranta ko ba ka yi karatu ba, idan ak yi abun addini ka ji. A mahauta in an fiɗa, ko fince ka yi. A fada kuwa za ka ƙaru da maganar tsofaffi don nan ne matattarar magana."
"Gaskiya ne! Ina ƙaruwa kam sosai a fadar nan."
Nan suka ci gaba da tattaunawa.
_Ummyn Yusrah_
*ABULLE TA MAI UNGUWA*
*HAZAƘA WRITER'S ASSOCIATION*
  _UMMYN YUSRAH_
_18_
Leda biyu na ruwa Abulle ta sha da kuma allurai biyu bayan dogun artabu da akasha wajen sa mata ruwan da tsira mata alluran.
Ba kunya ba tsoron Allah ta zage ta yi ta zabga kururuwa tamkar wacce za a zare ma rai.
Sai wajen ƙarfe ɗaya saura na dare aka sallemesu. Shima dalilin matsawar da Lubna ta yi ma likitan, don ba zata iya kwana a asibitin ba.
Itama Abulle tunda ruwa ya ratsata, jijiyoyin jikinta ya saki, ta ji ta ƙagu su koma gida, don ta gaji da kwanciya a gado mai tafiya. Ko yaya aka ɗan muskuta sai kaga gadon ya matsa.
Kamar ba ita ce É—azu aka sha gwagwarmaya wajen sanya ruwan ba.
Gari ya yi shiru, kai ka ce ba wani É—an adam da ya wuni yana zirga-zirga a wajen.
Tituna ma É—ai-É—aikun ababen hawa ne ke giftawa.
Ba ka jin motsin komai sai kukan kwaɗi da wasu ƙwarin.
Ƙofofin gidaje ma a rufe, haka ma shaguna, sai dai a wasu ƙofofin gidajen da yake mallakin gidan almajirai, zaka iya hangosu shimfiɗe kan tabarma suna ta sheƙa barci. Wasu kuma a ƙofar shagunan mutane.
Tunda suka fara tafiya waje É—aya ne kawai suka ga mai shayi, da wasu tsirarun mutane da basu wuce uku ba.
Dare kenan! Mahutar bawa.
Kowa ya bar gida-gida ya barshi.
Hakan ce ta kasance.
Hamusu ma yana ɗaya daga cikin mutanen da ke ƙawance a ƙofar wani shago, a tsakiyar bencin da aka tokare ƙofar shagon bayan an rufeshi da kwaɗo.
***
Tun ranar da suka yi sa'insa da Abulle ya tattara kayanshi ya bar mahaifarshi, ya fita neman kuÉ—i don huce takaicin abunda Abulle ta yi mishi.
Yana da yaƙinin kuɗi ta bi, shi yasa ta amince da auren Mai Unguwa. Inda yana da su da yanzu suna tare.
Ya shigo cikin garin Jinjin ba tare da yasan kowa ba, hasalima karo na farko kenan a tarihin rayuwarshi da ya taɓa zuwa.
Sosai yaga bambanci da garinsu. Kowa a nan harƙar gabanshi yake yi, idan zaka wuni baka sami ɗigon ruwa ka jiƙa maƙoshinka ba, ba mai baka, basu damu da kai ɗin baƙo ba ne, ya saba gani a garinsu idan aka yi baƙo an rinƙa ina asaka da shi kenan.
Kwananshi biyu yana garari a cikin tasha, ganin 'yan kuÉ—aÉ—enshi na shirin gangarawa su barshi, yasa ya nemi mafita daga wajen wani da suke kwana kullum a tsakiyar motocin da ake ajesu idan dare ya yi.
Gauta yake kasawa a tire ya yi ta yawo kan tituna yana sayarwa.
Shine sana ar da Hamusu ya fara yi.
Yau kwananshi biyu kenan da fara sana ar, sai dai yanzu ya bar cikin tasha ya dawo kwana ƙofar wani shago.
Har ya fara tunanin canza sana ar, domin yau ba ƙaramin galabaita ya yi da zafin rana ba.
Sai dai kuma ba ya da wani ishashshen jarin da zai kama wani sana ar.
Juyi kawai yake yi, sam! Barci ya ƙi ya ɗaukeshi sai ma wasiƙar jakin da yake ta karanta.
"Allah sarki Inna ta! Ko yanzu a wani hali kike? Ki yi haƙuri na tafi na barki ba tare da izininki ba, na tafi na barki ba tare da tunanin lalular makanta da kike fama da shi ba. Ban yi hakan domin in sanya ki a damuwa ba, sai don sama wa zuciyata mafita, Inna ba zan iya zama cikin Mai ludaya a ɗaura wa macen da nake so aure da wani ba, zuciyata ba zata gaza ganin hakan ba Inna! Ki fahimceni, zan dawo gareki nan ba da daɗewa ba, zan dawo, zan dawo..."
Maganar da yake yi kenan a hankali cikin sautin kuka, zuciyarshi kuma na ƙuna.
***
Barci sosai Abulle ta sha akan lafiyyayen gadon da ya sha shimfiÉ—i, ba kamar gadonta da aka yi shi da yayi aka É—inkeshi da buhu ba.
"Ke wai ba za ki tashi ba ne?"
Lubna ta faɗa tana ɗaka mata duka a sangalalin ƙafafunta.
Tashi ta yi tana miƙa, tana hararar Lubnan da gefen ido, don ba ta so tashi yanzu ba.
"Lafiya kika tsareni da ido? Ko baki gama warwarewa ba ne?"
'Wannan baiwar Allah akwai buhun masifa! Inaga da ita ke da gidan ma ko wuni É—aya ba zan yi ba.'
Ta faÉ—a a zuciyarta, a fili kuma ta ce,
"Ras nake! Allah na tuba ma ai inaga na fiki lafiya."
Ta ƙarashe maganar tana sauƙa daga kan gadon.
Zaro ido Lubna ta yi,
"Me kika ce?"
Ta tambayeta.
"Cewa na yi, ai yanzu ko garin nan aka ce in zagaye da gudu zan iya."
Tsaki ta yi, ta koma ta kwanta a cikin kujerar da ke cikin É—akin.
"Ina kuma za ki je? Banɗaki za ki shiga, akwai sabon burosh da makilin na ajiye miki."
'Buroshi? Makel? Su kuma suwaye hakan?'
Ta tambayi zuciyarta yayin da ta nufi ƙofar banɗakin.
_Ummyn Yusrah_
*ABULLE TA MAI UNGUWA*
*HAZAƘA WRITER'S ASSOCIATION*
_Na_
_Ummyn Yusrah_
_Hhhhhh! Sosai Abulle ta ce in miƙo gaisuwarta ga masoyanta, musamman,_
_Abu Hisham_
_Yayana Almu_
_Kamala Minna_
_Beauty Queen_
_Mai Dambu_
_Heenart Nijar_
_Queen Beelart_
_19_
Duk dube-dubenta ta yi bata fahimci komai ba, don banÉ—akin cike yake da shirgi.
Taɓe baki ta yi, ta ce,
"Shima banɗaki sai an yi mishi jere tsabar samun waje. Wannan kwalayen idan na samu na jeresu a kan sif ɗina ba ƙaramin kyauwu za su yi ba."
Ta ƙarashe maganar tana murmushi.
"Ce miki a kayi ana magana a toilet ne kam."
Daga can ta ji Lubna na mata magani.
"Ohho miki kuma! Ni na san wani tulat ne."
Ta faÉ—a a hankali, sannan ta É—auro alwala ta fito.
"Kawai ki goge baki ki yi alwala shine ki ka zauna surutu?"
Turo baki ta yi da yatsina fuska, haÉ—e da hararar ta ta gefe don ta tsani masifa, da alama wannan mai farar fuska kamar shinkafar ba za su zauna inuwa É—aya da ita ba.
"Yo, naga dai alwalar haÉ—e take da wanke baki, kuma duk na yi. Sallah zan yi yanzu."
"Kina nufin ba ki yi burosh É—in ba?"
Yadda ta zaburo kai ka ce ashariya Abullen ta yi mata
"Magana ta gaskiya ma ni ban sansu ba."
Ta bata amsa tana sanya hijabin da ta gani kan sallayar ta tada iƙama.
Shiru ta yi ganin ta fara sallah, zuciyarta cike da tunanin wai ba tasan man goge baki ba. To su da me suke wanke bakin?
"Ina kwana?"
Shine kalmar da ya katse mata tunanin.
Kallonta ta yi, tana naÉ—e hijabin.
"Ba dai kin idar da sallar ba ne?"
Itama kallon ta ta yi,
"Na idar mana."
"Malam raka a biyu fa za ki yi, ba É—aya ba."
Kallon rashin fahimta ta yi mata.
"To, ai biyun na yi."
"A hakan? Kafin kiftawar ido da buɗewa har kin dungura kin tashi! Da aiki. Wannan shi ake ƙira 'yar mubi ba yawa sai lada."
Yatsina fuska ta yi,
'Koma 'yar waye ke kika sani.'
Ƙofa ta nufa da niyyar fita, tambayar da ta jefo mata yasa ta tsayawa.
"Na ce ina za ki je."
Ta sake maimaita mata tambayar.
"Zuwa gaida masu gidan, in kuma ci abinci."
"Ba ki goge bakin ba ne za ki ci abinci?"
Cikin jin haushi yasa ta ce,
"Wani burushi da makel da kike faÉ—a ma ni ban sansu ba."
Fuska cike da mamaki da kuma don darawa da sunan da ta ƙira abun goge bakin ta ce,
"To, da me kuke wanke bakin a can?"
"Gawayi da gihiri muke dangwala a jikin soson buhu mu yi ta gogawa a haƙoran. Nan gidan ko ban ga alamar murhu ba balle in samu."
Bata ce komai ba ta miƙe ta nufi banɗakin, sai da ta kai ƙofa sannan ta sa hannu ta yafutota.
Makilin ɗin ta matsa a jikin burunshin ta miƙa mata,
"Ki dirje duk wani lungu da saƙo na cikin bakinki har kan harshenki."
Tana gamawa ta fice ta bar Abulle a banÉ—akin.
"Wannan akwai shegen iyayi, in da ita ke da gidan inaga ko wuni guda ba zan yi ba za ta korani gi..."
"Wai waya faÉ—a miki ana magana a banÉ—aki."
Shiru ta yi, ba amsa.
Ta É—au tsawon lokaci tana tunanin yadda za ta zura wannan abun cikin bakinta, tsoro ma take kada kifiyoyin robar su caccake mata dadashi.
Lakatar man goge haƙoran ta yi, wani yaji-yaji, zaƙi-zaƙi ne ya gauraye mata baki.
Tas ta shanye makilin ɗin kan burushin ta sake ɗauko, gudar makilin ɗin ta rinƙa matsowa tana sha tana jan yaji, idan ta ja sai ta ji iska mai sanyi yana hura mata cikin baki.
"Mazauni kika samu a ciki ne kam?"
Lubna ta watso mata tambaya daga can.
Zabura ta yi,
"Gani zuwa."
Da sauri ta zura magogin cikin bakinta.
Ta dai yi yadda ya samu ta É—auraye bakin ta sake tatso man ta lashe kafin ta fito.
"Au! Duk wannan zaman naki ba wanka kike yi ba?"
"Wanka kuma da sassafen nan kamar wacce ta yi fitsarin kwance? Jiya ma ai na yi wanka kafin mu taho nan."
"Ikon Allah! Kenan acan ba kullum kuke wanka ba?"
'Wanka kullum! Wa yaga ƙwaɗi.'
A fili kuma ta ce,
"Ina muka ga ruwan da za mu yi wanka kullum."
"Uhmmm! Je ki."
Ta fice, don dama ta gaji da yawan tambayoyin nan kamar a gaban alƙali.
_Ummyn Yusrah_
*ABULLE TA MAI UNGUWA*
*HAZAƘA WRITER'S ASSOCIATION*
      _Ummyn Yusrah_
  _20_
Ta jima zaune a falon ba kowa sai Lantana mai aiki da ke share-share da goge-goge da kuma tibi da ke ta aiki shi ɗayanshi.
Gajiya da zaman ta yi, ga kuma yunwa da ya dameta.
"Baba! Don Allah an gama abun karyawa ne?"
Ta tambayi Lantana dake goge tibi.