← Book details Abulle Ta Mai Unguwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 15 OF 15

Sashe 15

Abulle Ta Mai Unguwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read

Bata bi ta kanshi ba, gado ta haye ta ja bargo ta rufu. Ba jimawa barci ya yi awon gaba da ita.

***

Duk wani rarrashi da magiyar da Afreen ya ma Abulle kan ta koma ɗakin Lubna ƙi sauraronshi, sai ma tsalle da ta daka ta ce ita da ɗakin Lubna sai a ƙiyama, ta barmata shi bari na har abada kuwa. Tana iya jure komai amma banda walaƙanci

Ƙarshe dai haƙura ya yi ya barta, nan itama ta bi lafiyar gado cike da ɗokin gobe tana garinsu.

Daren yau ya mata nisa, ta yi barci har ta gaji gari ya ƙi wayewa. Tun tana juyi har dai ta tashi ta zauna.

Agogon bangon da ke manne a jikin bangon ɗakin ta ƙura ma ido, gashi dai sai aiki yake yi, amma ita sam bata fahimtar me yake aikatawar, don ba iyawa ta yi ba.

Ita dai kawai bin ɗan dogon tsinken da ke ta zagaye a ciki take da kallo. Daga bisani ta keɓe baki ta ce,
"Agogo kenan! Sarkin aiki."
Da ta gaji da zaman sai ta sake jawo jakar kayanta ta sake zazzagesu tana kuma yi musu sabon naÉ—i tare da shiryasu cikin jaka.

Sai da ta gama tas! Ta sake ciro hotunan nan tana sake ƙare musu kallo. Wasu ta yi dariya, wasu kuma haka kawai sai su bata tausayi. Mussaman ma wanda suka yi a wani sallah ita da Inno, Ilu da ƙaninta Muntari. Duk sunci kwalliyar sallah. Ilu da Inno zaune a kan kujera, Abulle da Muntari kuma zaune a ƙasa a gabansu.

Kuka ne ya ƙwace mata wanda bata san dalilin yinshi ba.

Sosai take kewar iyaye 'yan uwa da illahirin mutanen Mai Ludaya. Haka nan kawai take jin wani irin janji a jikinta dama yanayinta. Ita kanta tana mamakin yanda aka yi Lubna ke cin bulus da yawa a kanta.

Duk da kasancewarta mai tsoro, bata lamunci rashin mutunci da raini ba. Da zarar ka ce mata kule zata ce cas!

Share hawayenta ta yi, ta ci gaba da kallon hatunan.

Sosai ta kura ma hoton idanu. Tsaye suke a bakin gona ita da Hamusu, yana sanye da rigarshi 'yar shara mai ruwan bula da na yadi da farin wando, ita kuma tana sanye da atamfarta riga da zani da ɗankwali mai kalar ruwan ƙasa da baƙi yayin da ta tamke kunkuminta da gyalenta.

Dukkanninsu rake suke sha. An É—auki hoton ne daidai lokacin da suka kai raken bakunansu da niyyar gutsura.

Ta daɗe tana ƙare ma hoton kallo, ƙirjinta na dukan sha uku-uku.

Yau ce rana ta farko da ta fara nadama da da-na-sanin biye ma banzar zuciyarta wajen rabuwa da rabun ranta Hamusu! wanda a baya ko a mafarki basu taɓa tunanin hakan ba.

Yau ce rana ta farko da tayi Allah wadai da ƙin tsayawa ta saurari uzurinshi, sabida baƙin kishi irin nata.

Yau ne kuma ta tuna irin gangancin da ta yi na amincewa da auren Mai Unguwa sabida tsantsar ƙwaɗayi irin nata.

Inama tana da halin hana faruwar auren nan nata da Mai Unguwa? Bakin alƙalami ya riga ya bushe. Ta yi ganganci tun a karon farko, a yanzu bata isa ta je da zance fasuwar auren ba, don tasan hakan babban abun kunya ne, abune kuma da zai iya taɓa kima da darajar gidansu. Abune da zai kafa tarihi tun daga iyaye har jikokin-jikoki a gari. Domin abun kunya ne a saka auren mutum a ce an fasa. Gaba ɗaya gari da maƙota sai zance ya zaga kuma gidan sai ya shiga cikin tarihin garin.

Tunowa ta yi da ranar da zata tafi Mairangwangan ya biyota yana yi mata magiyar ta tsaya ta saurareshi, amma ta ƙi, sai ma maganganu da ta gaggayamishi wacce ya gaza haƙuri shima ya mayar mata. Duk da kasancewarshi mai haƙuri sai da ta kai shi maƙura.

Ta sake É—auko wani hoto da suka yi a yammacin biyun sallah.

Tarin samari ne da 'yammatan garin, sun taru sun yi layi, mata sun tsaya a ɓangaren gabas, maza kuma yamma, dukkanninsu suna kallon juna.

Tafi aka fara tare da waƙa.

'Yammata a dandali da samari a dandali.

Kowa nata shaggali, yau ranar tamu ce

Abulle zo ki rausaya, Hamusu ne gwaninki ke.

Kowa ya san dashi, kema kin tsayar dashi.

An ɗaukeshi ne daidai lokacin da ta fito tsakiyar fili tana rawa, kai a ƙasa Hamusu ya fito yana tayata takawa.

Kuka ne mai ƙarfi ya ƙwace mata, da sauri ta toshe bakinta da hannayenta duka biyun, ta miƙe samɓal a ƙasa tana kuka mara sauti.

_Ummyn Yusrah_
Chapter 15 · 0% Book details