← Book details Abulle Ta Mai Unguwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 2 OF 15

Sashe 2

Abulle Ta Mai Unguwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Kai! Wannan yarinyar ƴar gidan Ilu mai Amalanke nan fa kalar mu ce."  Zaro ido ya yi, cike mamaki ya ce "Ranka shi daɗe! Wannan ai ta yi ƙarama, duka-duka nawa take."  "Ka ji shashanci! Ita Abullen ba za ta zauna ba ne idan an kai ta ɗaki ko me ka ke nufi Kallamu?"  "Ahh! Zama kai, daram ma kuwa. Kawai dai gani na yi ta ƙawar Indo ce ta wajenka kuma ƴar autar gidan ka."  Ɗagowa ya yi, ya na ƙare ma Sarkin fada kallo  "Ahir ka iyar ma bakinka. Ka je ka sami Ilun ka gaya mishi idan bai bada ita Abuwar ba ina ciki." "An gama ranka shi daɗe!" Har ya fara tafiya sai kuma ya dawo ya durƙusa yana jinjina "Amma yallaɓai kana ga ita yarinyar za ta yarda?" Murmusawa ya yi har sai da jajayen haƙoranshi da suka gama rinewa da goro suka bayyana. "Yarda kam ai ta riga ta yi an gama. Kai dai je ka sanar ma Ilun. Ita da ke zuwa cin hinkahwa duk sati, ta samu a sati sau biyu ko uku ai kaga ta more, domin da zarar an yi auren nan za a dawo da girka ta sau biyu ko uku a sati don in samu ta zauna." Shima dariyar ya yi ya ce "Kuma fa haka ne yallaɓai! Na wuce ma, da zarar na yi sallar magariba zan wuce can ɗin." "To, madalla. A dawo lafiya."

"A ah! Yau kuma mutanen fadar Mai Unguwa ne a gidan namu?" Malam Ilu mai Amalanke ya faɗa lokacin da ya fito ƙofar gida bayan ɗan aike ya sanar ana nemanshi a ƙofar gida.

"Ranka shi daɗe nine da magaribar fari." Juyawa ya yi ya kalli gabas da yamma kudu da arewa "In ce dai Sarkin fada makuwa ya yi ko?" "Makuwa kuma? Mai ka gani?" "Ji na yi ka ƙirani da sunan manya." "Au! Wai da na ce Ranka ya daɗe? Ai ka dace da hakan ne. Ko za mu samu waje na musamman, domin muhimmin saƙo ne ke tafe da ni." "To! Allah dai yasa lafiya ba?" "Lafiya lau ma, sai alkairi." "To Madalla. Ina zuwa." Gida ya shiga ya ɗauko tabarma ya shimfiɗa a ƙarƙashin bishiyar darbejiyan da ke can gaba da gidan.

Bayan sun zauna, suka sake gaisawa gami da tambayar lafiyar iyalan da kuma harƙoƙinsu. Shiru ne ya gifta tsakani, kafin Sarkin fada ya katse shirun da faɗin.

"Mai Unguwa ne ya tasani ya ce in zo takanas ta kano, ƙafa da ƙafa in sameka in sanar kuma in yi maka albishir cewar idan ba a yi ma Abulle miji ba yana riƙo. Ya gani yana so." Ilu ya faɗaɗa fara arsa ya ce "Ikon Allah! Banda Mai Unguwa da abunshi ai Abulle ƴar shi ce, ko an bada ita ya ce ya mata miji ai da gudu za a ƙarɓo ta. Wa ma zai ƙi haɗa zuri a da jinin Mai Unguwa? Wanne ɗa ne ko jika za a ba Abullen daga ciki?" "A ah! Ɗa ko jika kuma? Ba ko ɗaya daga ciki." "To, wane ne daga cikin dangin nashi?" Yana maganar fuskarshi fal annuri. "Da alama dai ba ka fahimci maganar tawa ba. Shi Mai Unguwar ne ya gani ya ke so, ya kuma buƙaci a bashi auren ita Abullen." Cak! Numfashin shi da tunaninshi ya tsaya na wucin gadi.

Jin shirun da ya yi ba amsa yasa Sarkin fada gyaran murya ya ce "Malam Ilu na tare da ni kuwa?" "Ina tare da kai Sarkin fada." "To, me ka ce ne?" "Anya ko Abulle ta wajena ka ke magana kuwa?" "Ita ɗin ce dai, ai duk faɗin unguwar nan tamu ta Mai ludaya ita ake ƙira da Abulle ko Abuwa. Sai Zebu ƴar gidan Iro mai tumaki sai kuma Zinaru ƴar gidan Audu gurgu. Dukda sunayen nasu guda ne Zenabu amma ai da Inkiyar da ake ƙiran kowa." "To, amma ai ita Abuwar ba wata babba har can ba ne. Ina laifin Ma ƙaramin ɗan shi Mado da Indo ƙawar ita Abuwar ke bi ko dai wani daga cikin jikokinshi. Amma shi da kanshi ai ya girme mata nesa ba kusa ba." "To, shi aure ina ruwan hi da wani girma da tsufa ko shekaru? Zaman lafiya da kwanciyar hankali ake nema ai. Kada ka manta abunda ka ce, ba wanda zai ƙi haɗa zuri a da mai gari."

'Da ne da na fahimci maganar a baibai.'

"Haka ne. Yanzu a yi haƙuri aɗan bani lokaci in tuntuɓi ƴan uwana da uwar ƴar da ita ƴar, duk abunda muka yanke zan zo har fadar Mai Unguwar in sanar muku." "To, ba damuwa. Muna jira, fatan ba za a ɗau lokaci mai tsawo ba?" "Da ikon Allah." "To, Allah yasa mu ji alheri. Na barka lafiya. A gaida Iyalan da ita Abullen a ce mai unguwa yana miƙo gaisuwa."

_Ummyn Yusrah_
[9/5, 10:15 AM] Ummyn Yusrah🧕🏻: *ABULLE TA MAI UNGUWA*

_Ummyn yusrah_

_A ƙara yawan feji, a ƙara yawan feji. Duka-duka labarin fa bai wuce feji ɗaya ba idan na ƙara, ban son ya ƙare ne yasa na ke ta yi muku shi kaɗan-kaɗan domin nishaɗinku. Kawai a ci-gaba da gahi kawai._

5

Naɗe tabarmar ya yi ya nufi cikin gida ranshi ɓace, tunda ya shiga gidan ma bai iya zama ba. Jingina ya yi da zanar da aka zagayeshi da ɗakin. Inno da ta fito daga daki hannunta ɗauke da tire na kwano, an jere kwano tuwo da miya na ci ka duba da kofin ruwa shima na ci ka duban akai tana ƙoƙarin ƙiran ƙanin Abulle ya zo ya kai ma Babansu waje ta ganshi tsaye ƙiƙam kamar wani soja.

Da sauri ta sunkuya ta a jiye kayan abinci ta matso ta ɗan rage tsawo tana tambayeshi "Lafiya kuwa Malam ka shigo ko ƴar gyaran muryar nan babu?" Tsaki ya ja kafin ya bata amsa, murya cike da takaici "Ina fa lafiya Inno?" Karɓar tabarmar ta yi ta shimfida musu. "Malam ka zauna." Zaman ya yi domin yana da buƙatar yin hakan, wannan baƙon al amarin da ya kawo mishi ziyarar bazata yasa ya ji jikinshi duk a mace ba wani kuzari. Ji ya ke yi ma kamar ba ƙasusuwa a jikinshi.

"Hankali dai Malam! Wannan irin zama haka kamar tumar ƴan bori ai sai ka ji rauni." "Yo, Inno ai na gode ma da na iya yin hakan. Gaba ɗaya fa ƙafafuwana yadda ki ka san an miƙe sanda haka na ke jinsu." Kare ma zaman da ya yi kallo ta yi, ya jingina bayan shi da bukkar ɗakin nasu, yayin da ya miƙe ƙafafuwan shi ƴan sirara masu kama da maburgin miya.

"Niko in ce Malam tsere ya yi da agaribar farin nan dai ko, ko in ce lisha i tunda lokaci ya yi, don ma wajen namu sai ai sallar ma mutum bai ji ba." "In da tseren na yi ai da na ji daÉ—i da wannan mummunan labari da ya riskeni a farkon dare." Gyara zama ta yi "Tofa! Wannan wani irin labari ne haka? Allah yasa dai ba Baffa Jafaru na burni cikin garin Jinjin ba ne ya riga mu gidan gaskiya?" "Ji wani mugun alkaba i a nan? Wan nawa ki ke yi ma fatan mutuwa a wannan tsakani? To li ilafi tsakanin shi da ke." Tsuke baki ta yi ta koma gefe. Tsawon shuÉ—aÉ—un mintunan da ba su gaza goma ba ya ce "Habba! Ai hakan ma ba zai yiwu ba." Bayan ya gama jero tsaki ya furta hakan.

"Malam wai me ke faruwa ne kam?" "Me ke faruwa ku? Bayan turo ssrkin fada da mai Unguwa ya yi kan cewar idan ba a yi ma Abulle miji ba yana kamu." Zaro ido waje ta yi ta haɗa hannayenta biyu ta sauƙe su kan ƙirjinta da ƙarfi tana faɗin "Na shiga uku! Wai wani Mai Unguwar?" "Mai Unguwa namu dai na mai ludaya." "Da kanshi ko dai ma jikinshi ko ɗan shi?" "To, wai Abuwa tamu ko dai Abu na gida Baba Ɗan Azumi da mijinta ya mutu kwanaki?" "Kin ji ki da wani batu! Ita Abullen nawa ke garemu?" "Ɗaya ke gare mu a gidan nan. Amma a dangi sun yi huɗu." "To, ta gidan nan yake magana." "Ji wani budurwar zuciya ana. Kuma shi tsofai-tsofai da shi, uban wane kakan wance ya rasa wa zai aura sai Abuwa? Ince dai ba ka amsa mishi ba." "Ina fa, na dai ce su bani nan da mako guda zan sanar da ƴan uwana. Duk hukuncin da aka yanke zan sanar da shi." "Gara hakan ai. Kafin nan cikin manemanta ta cire gwani sai a ce musu an ba da ita kawai." "Yauwa, hakan za a yi. Ku zauna da ita ki ji waye gwanin nata." "To, Malam." "Barin je in yi sallar lisha i, har an ida a masallaci ina nan." "To, a dawo lafiya."

Ummyn yusrah
[9/5, 10:15 AM] Ummyn Yusrah🧕🏻: *ABULLE TA MAI UNGUWA*

*HWA*

_Ummyn Yusrah_

_7_

Duk suka nufi gida rai bai so haka ba, don basu samu sun raba raini da Abulle ba. A cewarsu tsoro ta ji tunda har ta k'i zuwa dandalin.

Itama ta nufi gida rai b'ace na rashin samun biyar buk'atar ta, don ta gama tsara yadda za ta luguÉ—en tsuntsayen kan Karime, tunda ta gaggaya mata magana. Don tasan halin Karime da son gulma da neman shiga, duk yanda aka yi ta je ta sanar ma Indo abun da ya faru. Kuma tabbas tasan tare za su zo, gashi iya zaman da suka yi a hanyar zuwa dandali ba wak'iyarsu.

Haka ta nufi gidan rai b'ace, tana shiga ba tare da sallama ba ta yanki hanyar bukkar d'akinta.

"Ke Abulle zo nan." Juyowa ta yi tana tura baki, ta dawo ta durƙusa kusa da Inno ba tare da ta ce komai ba. 
Chapter 2 · 0% Book details