Sashe 14
Abulle Ta Mai Unguwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
_Matso kusa ku ji! Ko kuna da labarin shahararren kamfanin nan mai suna *RANDAWA MEDIA CONCEPT* kuwa? Kamfani ne ɗaya tamkar da dubu. Aiki cikin aminci, inganci, rangwame da kuma rahusa. Ku dai kawai ku tuntuɓemu ta wannan number domin samin biyan buƙata cikin sauƙi 08062176520. Ga kaɗan daga cikin aiyukanmu_
_1. Waƙar biki, suna, siyasa, ring tone da sunanki/ka, waƙe masoynka/ki, miji ko mata._
_2. Calendar da sticker biki, suna sauƙar karatu, ko dai na wani abun._
_3. Tallata haja ko wakar ma aikata ko company._ da dai sauransu
_Kai tsaye ku tuntuɓemu ta numbermu dake sama don samun aiki cikin rangwame da rahusa, sai kun zo._
_28_
Ada baya tana son zuwa cikin garin Jinjin, sai dai a yanzu da take cikinsa duk ta ji ya fita mata a rai. Ta tsani garin gaba É—ayanta, ko kaÉ—an ba zata iya rayuwa cikinta ba. Gara ta koma inda ta fi wayo, gurin da aka san kimarta da darajarta.
Sai daf magriba Hajiya suka dawo. Kai tsaye É—akin Lubna suka nufa dukansu, bata ciki, har banÉ—aki tasa Lubna ta duba bata ciki.
"Ina ta shiga to? Kika ce ta kwanta É—azu, shigowarmu kum bata falo."
Hajiya ta tambayi Lubna da ta yi tsuru-tsuru da ita. Cike da tsoro ta ce,
"A nan fa na barta tana kwance."
Ta faÉ—a tana nuna gefen gado
"Barin dubata ko tana kicin ne."
Ta fice da sauri ta nufi kicin É—in, duk tsoronta kada Hajiya ta ji abinda ta yi mata.
Tana fita Hajiya da Afreen suka bi bayanta.
"Ba ta kicin É—in."
Lubna ta faÉ—a lokacin da ta sami su Hajiya tsaye a tsakiyar falo.
"Ba ta kicin? To, kodai sake fita ta yi ne irin na ɗazu? Kai Afreen tambayo Ɗayyabu, ke kuma duba ɗakin baƙin can."
Hajiya ta basu umurni
Da sauri dukansu suka fita.
Tana buɗe ƙofar ɗakin kuwa ta ganta kwance,
"Har kin tsoratamu, mun duba É—aki bakyanan ashe nan kika dawo."
Ba tare da ta É—ago ba, ta ce
"Eh!"
"Ki zo Mommy tana nemanki to."
Bata amsa ba, kuma bata tashi ba.
"Na ce, Mommy tana ƙiranki."
Kaɗa kai ta yi, ganin har yanzu tana kwance yasa ta keɓe baki ta juya zuwa falon.
Zaune ta samesu yanzu a kan kujera, Afreen ya sanar mata saƙon Ɗayyabu cewar Abulle bata fita ba.
"Tana kwance a can, ta ce tana zuwa."
Sai da ta É—au lokaci kafin ta fito, ta tsugunna can gefe.
"Shigo mana ki zauna, kin koma can gefe kin raɓe kamar wata baƙuwa."
Ƙara matsowa kaɗan ta yi,
"Ke dai akwai baƙunta Zainab! Ace mutum da gidansu ba zai saki jiki ba, sai ki ta ɗari-ɗari. Ko ba ki jin daɗin zama da mu ne?"
Girgizar kai ta yi,
"To mene ne?"
"Ba komai."
Ta faÉ—a a hankali
"To, ki saki jikinki kin ji?"
"To."
Murmushi ta yi,
"Yaya kan naki? Lubna ta ce kanki na ciwo, ta baki magani. Fatan kin ji sauƙi."
Kai ta ɗaga ta kalli Lubna, a zuciyarta kuwa cewa ta yi, 'Makira.' A fili kuma ta ce "Na ji sauƙi."
"To, Allah ya ƙara sauƙi."
Ƙiran sallar da aka fara ne yasa suka watse.
Ko da aka fito cin abincin dare ma, kaÉ—an Abulle ta ci, don gaba É—aya tunaninta da hankalinta ya koma gida. Duk zaman gidan ya isheta.
***
Ba laifi, yau kasuwa ta buÉ—e ma su Hamusu sosai, har takai ga sun haÉ—a kuÉ—in É—aki, sun kuma biya an basu. Yanzu zasu yi barci cikin salama.
***
Ƙwanƙwasa ƙofar ɗakin a kayi daga waje, daga bisani ya ce,
"In shigo?"
Kanta na kan waya tana kishingiÉ—e a kan gado ta ce,
"A a, ka yi ta tsayuwa."
Buɗe ƙofar ya yi ya shigo, ya janyo kujerar da ke gaban madubi ya aje kisa da gadon sannan ya ce,
"Ina abokiyar zaman taki?"
Keɓe baki ta yi, ta ce
"Ohho mata ba! Can É—akin naga ta koma."
Girgiza kai ya yi, kafin ya fara magana.
"Anti Lubna dama magana nake so mu yi."
Sai sannan ta É—ago kai ta kalleshi
"Ina jinka."
"Daddy da Mommy suna son Zainab ta zauna a gidan nan, sai dai kuma abinda kike yi mata naga bata jin daÉ—inshi. A tunanina zaki jata a jiki ki yi farin ciki da murnar samun 'yar uwa, sai kuma naga akasin hakan. Don Allah Anti Lubna ki sassauta mata ko zata ji daÉ—in zama da m..."
"Dakata! Mara kunya. Tazarar shekaru nawa ne tsakani na da kai?"
Ta katseshi ba tare da ya kai ga ƙarshen maganarshi ba.
Mamaki ne ya kamashi jin ta ambato shekaru, bai ga zancen da ya yi da har zai kai ga hakan ba.
"Biyar!"
Ya bata amsa
"Ok! Ashe kana sane, kana da shekara ishirin ina da ishirin da biyar. Kenan kaga ba kai zaka gwadamin yadda zan yi rayuwa ta ba, idan ba zaka iya ganina a haka ba ka kau da ido."
Baki kawai ya saki cike da mamaki, daga bisani ya miƙe ya bar mata ɗakin don baida ta cewa.
A yi haƙuri da kura-kuran da ke ciki, ban bibiyaba gaskiya.
*Ummyn Yusrah*
*ABULLE TA MAI UNGUWA*
*HAZAƘA WRITER'S ASSOCIATION*
_Ummyn Yusrah_
_29_
Yana fita ta miƙe ta ja tsaki, ta sa ma ƙofar makulli ta rufe.
Dawowa ta yi ta fara rage kayan da ke jikinta don shirin kwanciya. Abun hannunta ne ɗaya ya gangara zuwa ƙasan gado garin cirewa.
Tsaki ta ja, da nuna alamar gajiya sannan ta sunkuya da niyyar cirowa. Ba ta ganshi ba, ya yi nisa, sai wani farin takarda ta ci karo da shi.
Hannu ta miƙa ta ciro.
***
Yana fita kai tsaye ya nufi É—akin da Abulle take, da sallama ya shiga yana faÉ—in
"Ba dai har amaryar mai unguwa ta yi barci ba?"
Tashi ta yi daga kwanciyar da ta yi tana faÉ—in,
"Tuni na kwanta, barci ya ƙi zuwa."
Dariya ya yi
"To, yaya za a yi ya zo, bayan lokacin yinshi bai yi ba."
"Ai so nake in tashi da wuri."
"Ai ko ba ki kwanta da wuri ba, gidan nan ba a makara. Dolen mutum ya tashi ya yi sallar asuba da zarar lokaci ya yi, idan ya idar sai ya koma."
'Ya koma barcin asara ba.'
Ta faÉ—a a zuciyarta
"Mu je falo akwai film É—in da za a sa."
Kallonshi ta yi, ta ce
"Fin? Meye kuma wannan?"
Dariya ya yi,
"Ba fa fin na ce ba. Film!"
Dariyar da yake ne ya fara ƙular da ita,
"Uhmmm! Koma dai mene ne, ni barci zan yi, so nake gobe in tashi da wuri in shirya."
Ta jingina da gadon fuskarta na bayyanar da murmushi ta ce,
"Gobe kamar wannan lokacin ina gida."
Kallonta ya yi,
"Nan ma ai gida ne, mu da muke so ki zauna ko 'yar diplomar nan ki yi ki karanto mana engineering."
Zaro ido ta yi,
"In zauna a ina? Yasin a a! Kuma waye shi gudulomar da injimiyarum É—in?"
Dariya ne ya kamashi har da riƙe ciki
"Ba fa guduloma ba! Diploma na ce da engineering, ina nufin ki zauna ki yi karatu anan har a kai ki jami a."
A tsarace ta ce,
"A ina ɗin? Yasin ba ni zama. Har wani jami a ma zani? Taɓ! Ashema so ake mutanen Mai ludaya su ƙirani da 'yar iska. Hu'umm! Ba da ni ba aradu."
Yau wannan yarinyar zata kasheshi da dariya, da zantukanta masu cike da shirme.
"Yau kam nan kuka tare da hirar ne?"
Hajiya ta katseshi lokacin da ta shigo É—akin
"Yau mun ba falo hutu Mommy! Hirar nan É—in ma ya fi na falon daÉ—i."
Ya ba Hajiya amsa
"Ai kam naga alama! Tun É—azu nake jiyo dauriyarka. Zainab yaya kayin naki?"
"Na ji sauƙi Memi."
"Ankuma!"
Afreen ya faÉ—a
"Don Allah Mommy ki ji, Diploma fa na ce mata da engineering, ita kuma wai guduloma da injimiyarum. Ance Mommy ta ce Memi."
KaÉ—an ya rage itama ta yi dariya, sai dai ta gimtse.
"To, ai bata iya ba ne. A hankali zata koya."
Har ta juya zata fita sai kuma ta juyo tana tambayar,
"Ina Lubnar kuma?"
Take fuskar Abulle ya canza
"Ta kwanta."
Afreen ya bata amsa lokacin da ya lura da sauyin da ya gani a fuskar Abulle.
Matse baki ta yi, ta juya ta yi gaba. Tasan halin 'yar tata na rashin son hayaniya, hala sun dameta ta korosu nan.
Shi kanshi ya sani mai zama inuwa É—aya da Lubna sai ya shirya, ko kaÉ—an bata iya zama da mutane ba.
"Zainab! Nasan bakya jin daɗin zama da Aunty Lubna. Haka halayyata yake, duk mai zama da ita sai ya yi haƙuri..."
"Idan zaman ya zama dole ma mutum ba."
Ta katseshi
"Haka ne kam! ÆŠazu nima na shiga mu yi magana kan yanda take yi miki, ko saurarata bata yi ba. Sai ma wani maganar shekaru da ta fara jeromin."
Ya faɗa yana jan ƙaramin tsaki. Da alama maganar ta konashi
"A rayuwa ai ba a duba yawan shekaru, abinda aka aikata a tsahon shekarun ake dubawa."
"Haka ne kam, na yi iya ƙoƙarina don ganin na saitata amma abun ya gagara."
Ya faÉ—a cikin damuwa
"Abune mawuyaci ka iya canza mutum lokaci É—aya akan wata É—abi a tashi."
"Haka ne kam! Na tabbata inda hakan na da tasiri da Aunty Lubna ta daÉ—e da canzawa. Sai dai hakan ya riga ya zama É—abi arta. Ki tayata da addu'a sannan ki yi mata uzuri Allah ya bata ikon canzawa."
"Uhmmm! Amin."
***
Saida ta juyo taga hoto ne ashe. Ƙurama hoton idanu ta yi, kabanta na dukan uku-uku ganin kyakkyawan matashin saurayin da ke jikin hoton tare da Abulle.
_Goron Jumma a_
_Ummyn Yusrah_
*ABULLE TA MAI UNGUWA*
*HAZAƘA WRITER'S ASSOCIATION*
   _Ummyn Yusrah_
_30_
Ga saurayi har saurayi, sai dai da gani ƙauyanci ya gama yi mishi ƙawanya. Da zai samu ya goge, ba ƙaramin nagartaccen namiji za a yi a wajen ba.
Wurgi ta yi da hoton kan durowar da ke gefen gadonta, da niyyar idan gari ya waye zata ba mai shi. Sai dai maimakon ya zauna kan durowar sai ya faÉ—a bayanshi.